Alhassan Bako Zaku

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Alhassan Bako Zaku
Minister of Science and Technology (en) Fassara

17 Disamba 2008 - 17 ga Maris, 2010
Grace Ekpiwhre - Muhammed K. Abubakar
Rayuwa
Haihuwa Ibi (Nijeriya), 18 ga Janairu, 1951 (73 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a civil servant (en) Fassara

Alhassan Bako Zaku (an haife shi a ranar 18 ga watan Janairun a shekarar ta alif ɗari biyar da hamsin da ɗaya (1951) ya zama Ministan Kimiyya da Fasaha na Najeriya a cikin watan Disambar shekara ta 2007.[1] Ya bar mulki a cikin watan Maris ɗin shekarar 2010 lokacin da muƙaddashin shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya rusa majalisar ministocinsa.[2]

Fage[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Alhassan Bako Zaku a garin Dampar dake ƙaramar hukumar Ibi dake jihar Taraba. Ya halarci Makaratar Kwaleji Barewa,dake Garin Zaria a shekarar ta 1965 izuwa 1971. Sannan ya cigaba da karatu a Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria acikin shekarar ta 1972 zuwa shekarar 1979. inda ya samu digiri na B.sc (Education) a 1976, sannan digiri na biyu wato M.Ed a shekara ta 1979. A shekarar 1978, ya shiga Kwalejin Ilimi ta Jalingo a matsayin malami. Ya tafi Jami'ar Hull, Ingila a cikin shekarar 1981, inda ya sami digiri na uku a shekarar 1983. Kimiyya da Ilimin Fasaha. Ya koma kwalejin ilimi ta Jalingo kuma an yi shi a shekarar 1986.[3]

Dokta Bako Zaku ya taimaka wajen kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Adamawa a tsakanin shekarar 1991 zuwa shekarar 1993, kuma shi ne shugabanta na farko. Ya koma Jihar Taraba inda ya kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar a Jalingo a shekarar alif 1993, inda ya zama shugaban gwamnati. Ya yi aiki a National Open University of Nigeria a matsayin Manajan Cibiyar Yola tsakanin shekarar 2001 zuwa 2004, sannan ya koma Kwalejin Ilimi ta Jalingo a matsayin Babban Malami daga shekarar 2004 zuwa 2005. Daga nan ya koma Taraba State Polytechnic, Wukari a matsayin shugaba daga 2005 zuwa Mayun 2007.[3]

Sana'ar siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Gwamna Danbaba Danfulani Suntai ya naɗa Alhassan Bako Zaku Sakataren Gwamnatin Jihar Taraba a cikin watan Mayun shekarar 2007, kuma an naɗa shi Ƙaramin Ministan Kimiyya da Fasaha a cikin watan Oktoban shekarar 2007.[3] Bako Zaku ya zama Ministan Kimiyya da Fasaha na Najeriya a watan Disambar shekarar 2008. bayan da ya yi wa gwamnatin Shugaba Umaru Ƴar'aduwa garambawul.[1]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 Akin Jimoh, Abiose Adelaja And Christina Scott (2 January 2009). "Country Finally Gets New Health Ministers". SciDev.Net (London
  2. https://allafrica.com/stories/201003171041.html
  3. 3.0 3.1 3.2 https://web.archive.org/web/20110703235149/http://www.fmst.gov.ng/minister_of_state_profile.php