Jump to content

Amen Edore Oyakhire

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Amen Edore Oyakhire
Gwamnan jahar oyo

16 ga Augusta, 1998 - 28 Mayu 1999
Ahmad Usman - Lam Adesina
Gwamnan jahar Taraba

Rayuwa
Cikakken suna Amen Edore Oyakhire
Haihuwa 21 Oktoba 1945 (78 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da soja

Prince Amen Edore Oyakhire (an haife shi ranar 21 ga watan Oktoban 1945)[1]shi ne shugaban mulkin soja na jihar Taraba, Najeriya tsakanin watan Agustan 1996 zuwa Agustan 1998 a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha. A lokacin ya kasance mai kula da jihar Oyo a lokacin gwamnatin riƙon ƙwarya ta Janar Abdulsalami Abubakar, inda ya miƙa wa zaɓaɓɓen gwamnan farar hula Lam Onaolapo Adesina a cikin watan Mayun 1999 a farkon jamhuriya ta huɗu ta Najeriya.[2]

Aikin ƴan sanda

[gyara sashe | gyara masomin]

Oyakhire kwamishinan ƴan sanda ne, daga baya mataimakin sufeto Janar (AIG).[3] Ya kasance kwamishinan ƴan sanda na jihar Filato kafin a naɗa shi a matsayin mai kula da jihar Taraba.[4]

A jihar Taraba, Oyakhire ya fuskanci tashin hankali tsakanin ƙabilun Kuteb da Chamba da Jukun. A cikin watan Oktoban 1997 ya aika da takarda mai suna Comprehensive brief on the Chieftainty Stool of Takum Masarautar Jihar Taraba zuwa ga Majalisar Mulkin Soja. A wannan watan an kashe mutane bakwai tare da ƙona gidaje bakwai a rikicin ƙabilanci, kuma an kama mutane 31. Oyakhire ya ce duk wanda ake zargi da hannu a rikicin ƙabilanci, za a ɗauke shi a matsayin masu bata wa sauye-sauyen mulkin farar hula.[5] A cikin shekarar 1998 ma gwamnatin jihar Taraba ta kafa kwamitin zaman lafiya wanda ya yi nasarar yin sulhu na wucin gadi tsakanin ƙabilun.[6]

Jim kaɗan gabanin miƙawa gwamnatin farar hula a cikin watan Mayun 1999, Oyakhire ya shaidawa tawagar masu sa ido a ofishin jakadancin Amurka cewa "a miƙa mulki ga amintattun mutane waɗanda suke da tsoron Allah a cikin zukatansu, kuma hakan zai tabbatar da zaman lafiyar al'umma".[7]

Daga baya aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

Oyakhire ya yi murabus ne a cikin watan Yunin 1999 tare da sauran gwamnonin da suka shuɗe a zamanin mulkin soja. A cikin watan Agustan shekarar 1999 gwamnatin jihar Oyo ta bukaci sojojin da su taimaka wajen ƙwato Ƙadarori da ake zargin Oyakhire da muƙarrabansa sun sace da suka haɗa da motoci da na'urorin lantarki. An ƙi amincewa da buƙatar.[8]

A cikin watan Disamban 1999 wasu ƴan fashi da makami sun kai farmaki gidan Oyakhire da ke Legas inda suka sace Ƙadarori na Naira miliyan da dama.[9] Wani labari kan maita da aka buga a jaridar Daily Independent ta ruwaito cewa an kashe mutane 27 a Ozalla, jihar Edo a ranar 4 ga watan Nuwamban 2004. Labarin ya ce kisan kiyashin Ozalla ya biyo bayan wata Wasiƙa da Oyakhire ya rubuta yana zargin bokaye a cikin al’umma kan rashin samun gidan da ya dace a garin, da rashin biyansa fansho na ƴan sanda da kuma hauka a tsakanin ƴaƴansa.[10]