Ayandiji Daniel Aina
Ayandiji Daniel Aina | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Ibadan |
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | Malami |
Ayandiji Daniel Aina ɗan ƙasar Najeriya ne mai bincike kuma tsohon Mataimakin Shugaban Jami'ar Caleb, dake Jihar LegasNajeriya.[1]
Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Ayandiji ya sami digirin sa na farko wanda shine PG Diploma a aikin jarida daga Cibiyar Jarida ta Najeriya,[2] Ogba, Legas a shekara ta 1991. Ya yi karatun digirinsa na BA (Hons) a fannin Falsafa da Kimiyyar Siyasa a Jami'ar Ibadan a shekarar 1988, daga nan kuma ya koma Jami'ar Ibadan a shekarar 1992 don yin digirinsa na biyu a fannin kimiyyar siyasa da kuma digiri na uku a fannin kimiyyar siyasa har ila yau a jami'a guda.
Sana'a
[gyara sashe | gyara masomin]Ayandiji kwararre ne kan harkokin yaɗa labarai tare da gogewar aiki (kimanin shekaru goma) tare da Kamfanin Diflomasiyya na Duniya da ke Legas da kuma Daily Times Plc ta Najeriya.[3]
A lokacin zamansa a Jami'ar Babcock, Aina ya zama Shugaban Sashen na tsawon wa'adi biyu a shekarun (1999-2003), Dean na Faculty of Management and Social Sciences a shekarun (2003-2006) bayan nan ya zama Shugaban Ma'aikata na Shugaban jami'a a shekarun (2006 – 2008), sannan ya bi kuma ya sami Dean of School of Postgraduate School a (2010 – 2011) bayan haka ya zama Dean Babcock Business School a shekarar (2013 – 2015). Ya kuma kasance Farfesa mai ziyarar kuma shugaban gidauniyar Sashen Kimiyyar Siyasa da Huldata Ƙasa da Ƙasa, Jami'ar Jihar Osun (2009). An naɗa shi a matsayin shugaban sabuwar Makarantar Kasuwanci ta Babcock bayan ya dawo daga Jami’ar Adeleke inda ya yi hidimar majagaba-Mataimakin Shugaban Jami’ar.[1]
Rayuwa ta sirri
[gyara sashe | gyara masomin]Addinin Ayandiji Kiristanci ne. Ya auri Rachael wacce Malamar Jami’a ce a fannin sarrafa albarkatun bayanai kuma yana da ‘ya’ya uku.[1]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 "Caleb University ::: Vice Chancellor". calebuniversity.edu.ng. Archived from the original on 2018-04-11. Retrieved 2018-04-10.
- ↑ "Ayandeji".
- ↑ "Ayandeji".