Badiyya Hassan Mashi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Badiyya Hassan Mashi
Rayuwa
Haihuwa Jihar Katsina
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Karatu
Makaranta Jami'ar Bayero
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Badiya Hassan Mashi babbar jami'a ce, babbar sakatariya kuma kwamishina a yanzu kan harkokin mata da ci gaban al'ummar katsina jihar Katsina.[1][2][3]

Ƙuruciya da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Badiyya Hassan kuma ta tashi a karamar hukumar Mashi da ke cikin garin Katsina. Ta halarci makarantar firamare ta Gidado da ke cikin garin Katsina, da Makarantar Sakandaren 'Yan Mata ta Gwamnati (GGSS) da ke Malumfashi da kuma Jami'ar Bayero ta Kano sannan kuma ta kammala karatun ta na BSc microbiology da sakamakon "second class upper" da kuma MSc da kuma PhD a kan ilimin muhallin kananan halittu (environmental microbiology).[1][4][5]

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Ta kasance tsohuwar babbar malama a makarantar Hassan Usman Katsina Polytechnic a sashen Basic and Applied science, daga shekara ta 1992 zuwa 2016, sannan kuma tana ziyartar Jami’ar Umaru Musa Yar’adua don koyarwa.[1] A matsayinta na kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban al’umma, ta shirya wani taron wayar da kai akan magance matsalolin shan miyagun kwayoyi. Ta ce "Mata da iyaye mata dole ne su rika yin abin da ya dace musamman wajen sanya ido a unguwanninsu domin sanin wadanda 'ya'yansu ke cudanya da su da kuma abin da suke yi a lokutansu na sirri. Za mu bi gida-gida don mu ilimantar da iyaye. ”[6]

Ta sadaukar da naira miliyan 196 domin tallafawa yara masu rauni, marayu da mata a kananan hukumomin jihar Katsina 34.[7]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 "Principal Officers | Katsina State Ministry of Women Affairs". Retrieved 2020-11-16.
  2. "Katsina Disburses N30m to 3,000 Women". nggovernorsforum.org. Retrieved 2020-11-17.
  3. "Dr. Badiyya Hassan Mashi, the Katsina State Commissioner". Independent Newspaper Nigeria. Retrieved 2022-02-23.
  4. "Mashi, Badiya (2018-12-28). "Burina in inganta rayuwar mata – Dokta Badiyya Hassan Mashi". Daily Trust Aminiya (Interview) (in Hausa). Retrieved 2020-11-17.
  5. "8 amazing facts everyone should know about Dr. Badiyya Hassan Mashi". Katsina Post. 2018-12-05. Retrieved 2020-11-17.
  6. "Women Protest Rising Drug Abuse In Katsina – Abusidiqu". Retrieved 2020-11-17.
  7. "Katsina Earmarks N196m for Orphans, Women Empowerment". THISDAYLIVE. 2019-03-17. Retrieved 2020-11-17.

Hanyoyin haɗin waje[gyara sashe | gyara masomin]