Barnabas Andyar Gemade

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Barnabas Andyar Gemade
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

ga Yuni, 2015 - ga Yuni, 2019
District: Benue North-East
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

ga Yuni, 2011 - ga Yuni, 2015
District: Benue North-East
Rayuwa
Haihuwa Benue, 4 Satumba 1948 (75 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
All Progressives Congress
hoton barnabas

 

Barnabas Andyar Iyorhyer Gemade (an haife shi ne a ranar 4 ga watan Satumba,na shekara ta alif 1948) miladiyya.(A.c)Ɗan siyasan Najeriya ne, tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, wanda aka zaɓe shi Sanata a mazaɓar Benue ta Arewa maso Gabas na jihar Benue, Najeriya a ranar 9 ga watan Afrilu 2011 zaben ƙasa. [1]A halin yanzu ɗan jam’iyyar All Progressive Congress (APC).[2]

Tarihin Rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a ranar 4 ga Satumba 1948 a jihar Benue, Gemade wani basarake ne daga ƙabilar Tiv.[3] Yana da laƙabin gargajiya na Tiv na Nom-I-Yange-I-Tiv.[4] Gemade shi ne babban jami’in gudanarwa na kamfanin siminti na Benue (BCC) daga 1985 zuwa 1992, kuma an ce ya yi tasiri sosai a wannan matsayi.[5] Gemade ya kasance memba a taron tsarin mulki na 1994-1995 a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha. Ya rike muƙaman sakataren (Ministan) ayyuka da kuma shugaban jam'iyyar Congress of National Consensus party na ƙasa, wanda ɗaya ne daga cikin jam'iyyun da daraktan soji, Janar Sani Abacha ya ɗauki nauyi.[4]

Shugaban PDP[gyara sashe | gyara masomin]

A babban taron ƙasa na farko na jam'iyyar PDP bayan zaben watan Afrilu na 1999, Gemade ya zama shugaban ƙasa bayan wata gasa mai zafi da ɗaya daga cikin wadanda suka kafa jam'iyyar, Cif Sunday Awoniyi.[6] Ya gaji Solomon Lar, shugaban jam’iyyar na farko, kuma an zaɓe shi a wani bangare saboda dokokin shiyyar da suka amince da baiwa dan Arewa muƙamin. Tun farko Gemade ya samu goyon bayan shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo . Duk da haka, kafin babban taron ƙasa na 2001 da aka gudanar a ranar 9-10 ga Nuwamba, yana fuskantar adawa mai ƙarfi daga manyan muradun jam'iyyar. A loƙacin da ya yi ƙoƙarin a zaɓe shi shugaba a karo na biyu tare da Dokta Okwesilieze Nwodo a matsayin sakatare, su biyun sun sha kaye a hannun Cif Audu Ogbeh wanda ya zama shugaba da Vincent Ogbulafor wanda ya zama sakatare.[7]

A zaben5 fidda gwani na shugaban ƙasa na PDP a 2003, Gemade ya sha kaye a hannun tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, wanda aka sake zaɓensa. A watan Afrilun 2003, an kore shi daga jam’iyyar PDP saboda zargin da ake yi masa na nuna adawa da jam’iyyar. Babban dalili shi ne, a zaben 2003 na Gwamnan Jihar Benuwe ya goyi bayan dan takarar jam’iyyar United Nigeria Peoples Party (UNPP) maimakon dan takarar PDP, Cif George Akume . Daga baya aka sake shigar da shi jam’iyyar kuma ya zama mamba a kwamitin amintattu. A cikin wata hira da aka yi da shi a watan Janairun 2011, ya bayyana rigingimun da aka samu a shugabancin jam’iyyar PDP a farkon shekarun da suka gabata a matsayin lafiya, wanda ke nuna gasa tsakanin ɗaiɗaikun mutane maimakon tsarin raba madafun iko tsakanin kungiyoyi daban-daban.[8]

A wata hira da aka yi da shi a watan Nuwamban 2010, Gemade ya goyi bayan matakin bai wa shugaba mai ci Goodluck Jonathan damar tsayawa takara ba, duk kuwa da cewa wasu na ganin ka’idojin shiyyar ne ke nufin ɗan takarar ya je wurin ɗan Arewa. Ya ƙara da cewa tsayawa takarar Jonathan zai iya haifar da wargajewar ƙasar, ya kuma bayyana cewa a matsayinsa na ‘yan tsiraru a arewacin ƙasar cewa ƴan tsiraru sun kasance masu goyon bayan haɗin kan ƙasa.

Sanata[gyara sashe | gyara masomin]

Gemade ya kasance mai goyon bayan Joseph Akaagerger a loƙacin da aka zaɓe shi Sanata mai wakiltar Benuwe ta Arewa maso Gabas a shekarar 2007. A zaɓen Afrilu 2011, ya yanke shawarar ƙalubalantar Akaagerger a kujerar Sanata. Al’amura da dama sun faru a Benue a dai-dai lokacin da zaɓe ke ƙaratowa, wanda ya kai ga harbin Janar Lawrence Onoja.[9] Gemade na cikin shugabannin da aka yi wa tambayoyi game da tashin hankalin da jami'an tsaron jihar suka yi a watan Maris na 2011. Sauran waɗanda aka yiwa tambaya sun hada da George Akume, Iyorchia Ayu da Daniel Saror.[10]

A zaɓen da aka gudanar a ranar 9 ga Afrilun 2011 na Sanatan Benue ta Arewa maso Gabas, Gemade ya tsaya takara a jam'iyyar PDP inda ya samu ƙuri'u 229,682, inda ya doke Akaagerger wanda ya koma jam'iyyar Action Congress of Nigeria kuma ya samu ƙuri'u 143,978.<ref>"Collated Senate results". INEC. Archived from the original on 19 April 2011. Retrieved 25 April2011.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://dbpedia.org/page/Barnabas_Andyar_Gemade
  2. "Why I returned to APC – Gemade – Daily Trust". www.dailytrust.com.ng. Archived from the originalon 10 August 2020.
  3. Sufuyan Ojeifo (4 November 2001). Gemade, Between the Payer And the Piper. Vanguard. Retrieved 25 April 2011.
  4. 4.0 4.1 Simon Imodo-Tswam (6 October 2006). "PDP Will Not Feel Atiku's Exit – Gemade". Daily Champion. Retrieved 25 April 2011.
  5. Michael Jegede (3 June 2010). "Metamorphosis of Barnabas Gemade". Daily Independent. Retrieved 25 April 2011.
  6. John-Abba Ogbodo (25 April 2003). "PDP expels Barnabas Gemade, alleges anti-party activities". The Guardian. Retrieved 25 April 2011.
  7. John-Abba Ogbodo (25 April 2003). "PDP expels Barnabas Gemade, alleges anti-party activities". The Guardian. Retrieved 25 April 2011.
  8. Jide Ajani (23 January 2011). "Why PDP chairmen are targets of conspiracy, by Barnabas Gemade". Vanguard. Retrieved 25 April 2011.
  9. Ben Agande (20 March 2010). "Why Nigerians should leave Turai alone, by Barnabas Gemade". Vanguard. Retrieved 25 April 2011.
  10. "SSS quiz Ex-Gov Akumeh, Gemade, Ayu, Others over violence in Benue". Point Blank News. 25 March 2011. Retrieved 25 April 2011.

Template:Nigerian Senators of the 7th National AssemblyTemplate:Nigerian Senators of the 8th National Assembly