Bikin Al'adun Iganmode

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentBikin Al'adun Iganmode
Iri maimaita aukuwa
biki
Kwanan watan 1992 –
Ƙasa Najeriya

Yanar gizo iganmodefestival.org

Bikin al'adun kabilar Iganmode (wanda aka fi sani da Odun Omo Iganmode ) biki ne na shekara-shekara da al'ummar Yarbawa Awori na tsohon birnin Ota a jihar Ogun a Najeriya ke gudanar da shi.[1] Bikin shekara-shekaran na tsawon mako yana gudana ne a watan Disamban kowace shekara,[2] don baje kolin al'adu, ruhaniya da al'adun mutanen Ota Awori.[1][3] Har ila yau, bikin bugle ne na ruhi, kira zuwa gida don sake farfado da al'adu da kuma wayar da kan dukkan ƴaƴa maza da mata na Awori, a Legas, Ogun, Osun, Jamhuriyar Benin, ƴan ƙasashen waje da kuma duk inda suke a cikin duniya.[4][5][6]

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

An gudanar da bikin farko a shekarar 1992 lokacin da ake kiran bikin da ranar Iganmode. A tsawon shekaru, bikin ya karɓi baƙuncin fitattun wasu ƴan Najeriya da manyan baki, kamar tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo, tsohon babban lauyan Najeriya kuma ministan shari’a Marigayi Cif Bola Ige.

Sauran sun haɗa da tsoffin gwamnonin jihar Ogun Chief Olusegun Osoba, Otunba Gbenga Daniel, Ibikunle Amosun, Gwamna na yanzu kuma Mataimakin Gwamna Prince Dapo Abiodun,[7] Noimot Salako Oyedele, da Taiwo Ajayi Lycett, da sauransu.

Haka kuma wasu fitattun mutane kamar su, shugaban ƙasa Asiwaju Bola Tinubu, Sir Kesington Adebukunola Adebutu, da Sanata Musiliu Obanikoro sun jagoranci bikin.[8]

Abubuwa mafiya mahimmanci[gyara sashe | gyara masomin]

Daya daga cikin manyan abubuwan da suka fi ɗaukar hankali a bikin shine nunin da Egungun Masquerades yayi a Ota.[9] Al'adun Masquerade suna da tsarki ga al'ummar Awori yoruba na Ota.[10][11]

Yawon shakatawa[gyara sashe | gyara masomin]

Gwamnatin jihar Ogun ce ke tallafa wa bikin.[4][12][13][14] Abubuwan da suka faru na bikin an yi su ne tare da albarkatu na ruhaniya da na gargajiya na Olota na Ota. Har ila yau, bikin na neman inganta hanyoyin yawon shakatawa na Ota, Jihar Ogun da Najeriya baki-ɗaya.[15][16][17]

Bikin na baiwa mutane damar ganin baje kolin al'adu daban-daban da ziyartar wuraren yawon buɗe ido kamar ginin (storey building) a Najeriya.[18][19][20][21]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 "Iganmode cultural festival to promote exquisite Awori tradition". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 6 November 2021. Retrieved 16 March 2023.
  2. Adebayo, Sunday (4 November 2021). "Ota-Awori Kingdom Biggest Event, Iganmode Cultural Festival Set To Hold In December!". SocietyReporters.com. Retrieved 16 March 2023.
  3. "Ota Holds Iganmode Cultural Festival December To Awaken Security Consciousness – Independent Newspaper Nigeria" (in Turanci). Retrieved 16 March 2023.
  4. 4.0 4.1 "Govt to showcase Ota-Awori heritage with festival". Punch Newspapers (in Turanci). 14 November 2021. Retrieved 16 March 2023.
  5. NNN (29 November 2019). "Iganmode Cultural Festival to attract industrialists, diaspora,others". NNN (in Turanci). Retrieved 16 March 2023.
  6. "Odun Omo Iganmode: Social, Cultural Groups, Others, Enjoin to Support Celebration - The Gallant News". thegallantnews.com.ng. Retrieved 16 March 2023.
  7. "Our social investment programme will employ over 40,000 people – Governor Abiodun". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 18 December 2022. Archived from the original on 26 January 2023. Retrieved 16 March 2023.
  8. Limited, Alamy (15 December 2021). "Ota, Nigeria, Masquerades perform during the annual Iganmode Cultural Festival 2021 held in Ota, Ogun State, Nigeria. The festival is held to showcase the cultural heritage of the Awori-Yoruba people. Credit: Adekunle Ajayi/Alamy Live News Stock Photo - Alamy". alamy.com (in Turanci). Retrieved 16 March 2023.
  9. "Ota, Nigeria, Masquerades perform during the annual Iganmode Cultural Festival 2021 held in Ota, Ogun State, Nigeria. The festival is held to showcase the cultural heritage of the Awori-Yoruba people. Credit: Adekunle Ajayi/Alamy Live News Stock Photo - Alamy". alamy.com (in Turanci). 15 December 2021. Retrieved 16 March 2023.
  10. "Masquerading Politics". Indiana University Press (in Turanci). Retrieved 16 March 2023.
  11. Albert, Larry. "The Significance of the Egungun Cultural Festival. A Case of Study of Ota, Aworiland, Ogun State". Retrieved 8 August 2023. Cite journal requires |journal= (help)
  12. Staff, Daily Post (2022-09-23). "Ogun government declares support for 2022 Odun Omo Iganmode festival". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-03-16.
  13. "Governor Dapo Abiodun Congratulates Olota of Otta on Odun Omo Iganmode Cultural Festival". New Telegraph (in Turanci). 2022-12-09. Retrieved 2023-03-16.
  14. "Odun Omo Iganmode Has Attracted Investors Into The State- Dapo Abiodun Says As Festival Gets Underway". Voice of Awori (in Turanci). 2022-12-09. Retrieved 2023-03-16.[permanent dead link]
  15. David (2021-11-04). "Iganmode Festival: Olota wants annual event added to tourism calendar". The Sun Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-03-16.
  16. sunrise (2021-11-27). "Southwest ATPN drums support for Odun omo Iganmode". Sunrise News (in Turanci). Retrieved 2023-03-16.
  17. "Royal Visit: New Olowu, Prof. Matemilola visits Prof.Obalanlege on Iganmode Day Celebration. - THE BUSINESS PACKAGE". www.thebusinesspackage.com.ng. Retrieved 2023-03-16.
  18. newsheadline247. "Photos: Ogun Tourism revived as Nigeria's second storey building in Ota gets facelift | newsheadline247" (in Turanci). Archived from the original on 2023-01-25. Retrieved 2023-03-16.
  19. Great, Dennis (2021-08-08). "The Second Storey Building In Nigeria". BTATnT - Big Time Africa Travels & Tours Company (in Turanci). Archived from the original on 2023-03-21. Retrieved 2023-03-16.
  20. "The second storey building in Nigeria, Ogun, Nigeria". soamaps.com. Archived from the original on 2023-01-25. Retrieved 2023-03-16.
  21. Online, Tribune (2020-03-24). "Dent in history as Nigeria's second storey building battles anonymity". Tribune Online (in Turanci). Retrieved 2023-03-16.