Dogo Giɗe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Dogo Giɗe
Rayuwa
Sana'a

Dogo Giɗe dai fitaccen ɗan fashi ne a Najeriya wanda ya aikata munanan laifuka na cin zarafin bil'adama da suka haɗa da garkuwa da mutane, fyaɗe, satar shanu, da fashi da makami. Ta'addancinsa ya shafi jihohin Zamfara, Katsina, Neja, Kaduna, da wasu sassan Jihar Nassarawa dama Abuja, inda ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dama da kuma lalata ƙauyuka da dama a sassan Arewa maso Yamma da wasu yankunan Arewa ta Tsakiya, kamar jihohin Neja da Nasarawa da sauran su[1]

Rayuwar sa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Dogo Giɗe a ƙaramar hukumar Maru da ke jihar Zamfara a Najeriya. Yana da aure da ƴaƴa.

Jita-jitar mutuwarsa[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 2021, an yi ta raɗe-raɗin cewa Dogo Giɗe ya rasu. Kamar yadda aka bayyana cewa wasu ne daga cikin mutanen Dogo Giɗe sun kashe shi. A lokacin ana zargin an kashe shi ne a wata maɓoya a lokacin da yake karɓar magani sakamakon harbin bindiga da ya samu a wani faɗa da suka fafata a dajin Kuyan Bana da ke jihar Zamfara.[2][3][4]

Hare-haren cikin Makarantu[gyara sashe | gyara masomin]

Dogo Giɗe ya shirya kuma ya jagoranci sace ɗalibai kimanin 126 na makarantar sakandaren Baptist Baptist dake Maraban Damishi a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna a ranar 5 ga Yuli na 2021. Bugu da ƙari, yana da sa hannu wajen yin garkuwa da ɗalibai sama da 90 da ma’aikatan Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin Yauri dake Jihar Kebbi.[5] A ƙarshe dai sun sako ɗaliban da lamarin ya rutsa da su ne biyo bayan biyan wasu maƙudan kuɗaɗe da suka kai miliyoyin nairori, da iyayen waɗanda aka sace suka biya a matsayin kuɗin fansar ƴaƴansu. Ana tunanin cewa Dogo Giɗe yanada sa hannu a wajen sace ɗaliban wata Makarantar sakandare dake Kagara a ƙaramar hukumar Rafi ta jihar Neja. Duk da dai wasu na ganin shine ya taimaka akayi sasanci da wadanda suka sace ɗaliban, har aka samu suka sako su.[6]

Auren Ɗaliban Yauri[gyara sashe | gyara masomin]

Bayan shekara ɗaya da wasu watanni da sace ƴan matan makarantar Yauri, an samu labarin cewa Dogo Giɗe ya auri Farida, ɗaya daga cikin ɗaliban, kuma ya aurar da sauran 11 daga cikin ƴan matan ga abokan sana'arsa ta banza.[7][8][9]

Kakkaɓo Jirgin sojin Najeriya[gyara sashe | gyara masomin]

A watan Agustan shekarar 2023, Dogo Giɗe sun yi alfaharin kakkaɓo jirgin sama mai saukar ungulu na Najeriya a gundumar Chukuba da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja. Wannan al'amari ya kaɗa zukatan al'umma Najeriya da kewaye, duba da yadda ƴan ta'adda zasu harbo jirgin yaƙi. Kuma har suyi alfahari da hakan. Abin takaici, harin ya yi sanadin rasa rayukan jaruman sojojin saman Najeriya da adadin su ya haura sama da 30 da ke cikin jirgin.[10][11][12][13]

Duba kuma dai[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Umar Gusau, Shehu (18 March 2018). "Dogo Gide: The man who killed Buharin Daji". Daily Trust. Archived from the original on 18 August 2021. Retrieved 21 September 2023.
  2. Babangida, Mohammed (3 November 2021). "Nigeria: Is Notorious Bandit Dogo Gide Dead? What We Know So Far". allafrica.com. Retrieved 20 September 2023.
  3. Ibrahim, Aminu (1 November 2023). "Labari da ɗuminsa: An kashe Dogo Giɗe, ƙasurgumin shugaban ƴan bindiga da ya daɗe yana addabar jihohin arewa". legit.ng.hausa. Retrieved 22 September 2023.
  4. "Bandit Leader, Dogo Gide, Killed in Dispute With Deputy Commander". prnigeria.com. 31 October 2023. Retrieved 22 September 2023.
  5. Ayitogo, Nasir (17 June 2021). "Bandits storm federal college in Kebbi, abduct students, staff". premiumstimesng.com.
  6. "Zamfara bandits' leader, Dogo Gide Assures Of Release Of Abducted Kagara Students And Teachers". the Nigeria voice.com. 20 February 2023. Retrieved 21 September 2023.
  7. Adebowale, Yemi. "Tears for Birnin Yauri Schoolgirls". thisdaylive.com. Retrieved 21 September 2023.
  8. Sabiu, Muhammad (23 April 2023). "Terrorists free 4 Yawuri female students with babies". tribuneonlineng.com. Retrieved 21 September 2023.
  9. Babangida, Mohammed (21 December 2022). "Nigeria: Why I Abducted FGC Yauri Pupils - Dogo Gide". allafrica.com. Retrieved 21 September 2023.
  10. "FACT-CHECK: Did Bandits Shoot Down NAF Helicopter With AK-47 in Niger State?". PRNigeria.com. 16 August 2023. Retrieved 20 September 2023.
  11. Odewale, Taiye (14 August 2023). "Breaking: Aircraft belonging to Nigerian government shot down, 13 Soldiers killed in Niger". Blueprint.ng. Retrieved 20 September 2023.
  12. Umar Bologi, Musa (15 August 2023). "Air Force probes helicopter shot down claim by bandits". thenationonlineng.net. Retrieved 20 September 2023.
  13. "Mu Muka Harbo Jirgin Sojin Najeriya —Dogo Giɗe". Aminiya.ng. 16 August 2023. Retrieved 11 October 2023.