Jump to content

E9 (ƙasashe)

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
E9
Bayanai
Iri ma'aikata
Aiki
Mamba na Bangladash, Brazil, Sin, Misra, Indiya, Indonesiya, Mexico, Najeriya da Pakistan
Tarihi
Ƙirƙira 1993

Taron E9 dai wani taro ne na ƙasashe Tara, wanda aka kafa gamayyar ƙungiyar da ta ƙunshi ƙasashen domin cimma burin shirin UNESCO na Education For All (EFA).[1] "E" (Education) yana nufin ilimi kuma "9" na wakiltar ƙasashe Tara masu zuwa: Bangladesh, Brazil, China, Egypt, India, Indonesia, Mexico, Najeriya da Pakistan, [2] gamayyar ƙungiyar ƙasashen na wakiltar fiye da rabin al'ummar duniya da kashi 70% na daga waɗanda basu iya rubutu da Karatu ba-(illiterate) a duniya.

Asali da Manufa

[gyara sashe | gyara masomin]

An ƙaddamar da haɗa-kar E-9 a shekarar 1993 a lokacin taron EFA da ya gudana a birnin New Delhi, Indiya. E-9 ta zama taron ƙasashe don tattauna abubuwan da suka shafi ilimi, musayar kyawawan ayyuka, da kuma sa ido kan ci gaban da ya shafi EFA.

Manufar yunƙurin assasa wannan haɗa-ka ita ce don haɓaka gami da yaɗa ajandar ci gaba mai ɗorewa na buri na 4 na hanyar haifar da saurin canji a cikin tsarin ilimi a wani tsari na uku daga cikin abubuwan da suka fi dacewa da taron Ilimi na Duniya na shekarar 2020: [3]

  1. Tallafi ga malamai;
  2. Zuba jari a harkar basira;
  3. Ƙoƙarin rage gibin da ke tsakanin masu amfani da fasaha da intanet.

Matsayin zamantakewa

[gyara sashe | gyara masomin]

Ƙasashen haɗa-kar E-9 sun sami ci gaba a fannin tattalin arziki. Brazil, China, Indiya, Indonesiya da Mexico su ne mambobin G-20. Mexico memba ce ta OECD, yayin da China yanzu ita ce ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya. Brazil da Indiya suma sune ƙasashe goma na farko a fannin tattalin arziki. Indonesiya ma tana bunƙasa cikin sauri. A shekarar 1993, ƙasashen E-9 sun ɗauki kaso 16.5% kawai na GDP na duniya. Yanzu, suna wakiltar kusan kashi 30% na GDP na duniya. [4]

  1. "E-9 meet begins today, India to lay road map". Hindustan Times. 8 November 2012. Archived from the original on November 8, 2012. Retrieved 22 November 2012.
  2. "E9 Initiative". UNESCO. Retrieved 22 November 2012.
  3. "Meeting of Education Ministers of E9 Countries". Drishti IAS (in Turanci). Retrieved 2021-05-14.
  4. "E-9 Initiative Background". E-9 Initiative. Archived from the original on 6 August 2014. Retrieved 22 November 2012.

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]