Gogori
Gogori | ||||
---|---|---|---|---|
gunduma ce a Najeriya da kauyankun najeriya | ||||
Bayanai | ||||
Ƙasa | Najeriya | |||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | jihar Kano | |||
Ƙananan hukumumin a Nijeriya | Ɓagwai |
Gogori wani gari ne da ke a karamar hukumar Bagwai a arewacin jahar Kano Najeriya. Gogori ta kafu ne ga wani mutumin Bamaguje da ake kiran sa da suna kacca yana da ɗa guda ana ce masa gori ya kasan ce bahaushe ne,haka shi kansa mutum ne mai goro har tsufar da, ya manyan ta babu haƙora a bakin sa. Sai ɗan sa gori ya rika yi masa dubawa ta go ga masa goron don yasa a bakin sa, duk lokaci da ya bukaci goron sai ya ce wa dan nasa gori gogo mana,a haka ne aka samu sunan garin Gogori.wanan garin yana da fadin kasa wanda takai da ya fidda garu ruwa guda uku daga cikin ta akwai wani garin Kadamu dake karama hukumar shanono 2. Sare sare dake karamar hukumar Bagwai da Leringo da ke wannan karamar hukuma ta bagwai kai har izuwa yau akwai gonar gandu dake a yankin ta gogori wanda Madaki Abdullahi Muahammad Sambi ya bibiya ya gano ta. Gogori tana da rafuka guda biyu (2) da ka yamma akwai kigi sannan kuma daga arewa akwai Watari wanda tana daya daga rafuka da ake dasu duk a jihar kano da kasa baki daya. Wannan gari akwai tarin albarka acikin sa,da haka muka zakulo muku wannan tarihin garin Gogori. Sanan muka bincika kafa a wannan gari na Gogori ba'a taba cin sa da yaƙi ba.duk lokacin da kazo da zummar yaki a cikin sa, sai garin sai kaga ya zama kufai, ko kuma kaga rafin watari ya cika makil da ruwa yana ta gudu. Wannan gari shine mutum da yayi yake-yake da kuma samun nasara wannan garin Gogori gori akwai wata Maciji daka arewa maso yamma a gindin wata kuka ana ce masa Nazimu kuma yana fitowa ne duk kusan kwana bakwai wanda zai zagaya garin da daddare ko da yamma ba ruwansa da kowa inzai fito sunsan shi,donuna sanji don zaka rinka jin motsin fitowar sa inori alo Saniin madakisani shine a kaba rikon garin Bagwai na tsawo shekara uku sakamakon wasu abubuwa dake nuna akwai a garin. na sarautar gargajiya Gogori na daya daga ciki mazabu goma da ke a karamar hukumar Bagwai, Kuma daya daga masarautun dagaci dake yankin masarautar hakimin Bagwai a Masarautar Bichi.
Unguwanni a Gogori
[gyara sashe | gyara masomin]- Kofar Yamma
- Zango
- Kofar Kudu
- Dafka
- Gwanki
- Kodan Hayi
- Dankwari
- Koɗo
- Rura
- Tudun budu
- Katoge
Sarakunan Garin Gogori
[gyara sashe | gyara masomin]- Madaki Muhammadu Harusu
- Madaki Muhammadu Sani
- Madaki Muhammadu Sambo
- Madaki Isah Muhammad 1986-1994
- Madaki Abdullahi Muhammad 1994-2014
- Madaki Shehu Muhammad 2014-zuwa yau
Filin jirgin sama mafi kusa da Gogorishine :-
Mal. Aminu Kano International Airport, Kano. 59km
BIRANE MAFIYA KUSA DA GOGORI
Kano 58km Katsina 149.8km Zariya 155.1km Kaduna 229.5m