Gwanki

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Gwanki
ƙasaNijeriya Gyara
located in the administrative territorial entityjihar Kano Gyara

Gwanki, wani kauye ne dake arewa maso yammacin jihar Kano. Garin na Gwanki yana a karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano, wanda ke karkashin dagacin garin Gogori. Gwanki ta rabu a karkashin masu unguwanni uku. Unguwa ta farko itace Gwanki Babba, ta biyu Gwankin Gidan Yaro, sai kuma kashi na uku wato Gwankin Dan Kwari. Kauyen na Gwanki nada al'uma masu yawa kuma masu son dazan lafiya da juna.

Yanayi a kauyen Gwanki[gyara sashe | Gyara masomin]

Kamar ko ina a arewacin jihar kano , kauyen Gwanki nada yanayi maikyau na noma da kiwo, hakanne ma yasa gabaki dayan mutanen garin basu da sana'a da tafi noma da kiwo a wajen su.

Yanayin muhalli[gyara sashe | Gyara masomin]

Yanayin geographical co'ordination na kauyen Gwanki kamar haka, latitude, 11:35degreeN, dakuma longtitude na 8,0333degreeE.

Kauyukan da suke zagaye Gwanki[gyara sashe | Gyara masomin]

  • Gogori
  • Kodon Hayi
  • Kodon Kandas
  • Sare-sare
  • Umbawa
  • Dan Isa
  • Walawa
  • Rigar Are

Yare da addini[gyara sashe | Gyara masomin]

Dukkannin mutanen kauyen Gwanki Hausawa ne, kuma addinin su shine musulunci. Kamardai sauran garuruwan hausawa. tare da fatan zaka kai ziyara garin Gwanki.