Jump to content

Harin Bam a Jos, 2014

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentHarin Bam a Jos, 2014
Map
 9°56′N 8°53′E / 9.93°N 8.88°E / 9.93; 8.88
Iri aukuwa
car bombing (en) Fassara
Kwanan watan 20 Mayu 2014
Wuri Jos
Ƙasa Najeriya
Adadin waɗanda suka rasu 118
Adadin waɗanda suka samu raunuka 56

A ranar 20 ga watan Mayun shekara ta 2014, wasu bama-bamai biyu sun tashi a birnin Jos na jihar Filato a Najeriya, inda suka kashe mutane aƙalla 118 tare da jikkata wasu fiye da 56.[1] Bam na farko ya tashi ne a wata kasuwa, na biyu kuma kusa da wata tashar mota. Ko da yake babu wata ƙungiya ko wani mutum da ya ɗauki alhakin kai hare-haren, ana danganta hare-haren da ƙungiyar Boko Haram,[2] wacce tayi ƙaurin suna na kai hara hare da dama a Najeriya, musamman yankin arewa maso gabashin ƙasar.

Kiristoci da Musulmai sun yi arangama da dama a birnin Jos acikin shekaru da dama kafin tashin bama-bamai, kuma ƙungiyar ta Boko Haram ma ta yi ta kai ruwa rana kafin harin.[1] A shekarar 2012, ƙungiyar Boko Haram ta kai wa wasu majami'u hari da bama-bamai da nufin assasa rikicin addini tsakanin Kirista da Musulmi.[1] A cikin watan da ya gabato harin Boko Haram, na sace 'yan matan makaranta sama da 200, [1] ko da yake birnin Jos ya fuskanci manyan hare-hare guda biyu tun daga shekara ta 2012.[1] Kwana ɗaya bayan tashin bama-baman an kashe mutane 27 a hare-haren wasu kauyuka.[2]

Fashewar bama-baman kwara biyu sun kasance mintuna 30 tsakani,[1] ɗaya ya fashe da karfe 3:00, ɗayan kuma da ƙarfe 3:30.[3] Fashewar farko ta faru ne a Kasuwar Terminus, inda aka samu asarar rayuka sama da hamsin.[4] A cikin Terminus akwai "asibitin koyarwa, shaguna, ofisoshi da kasuwa" kafin harin. [5] Na biyu ya faru ne a kusa da wani asibiti. [4] Kuma ya kashe masu aikin ceto, waɗanda suka je taimakawa bayan tashin bam na farko. [1] An kuma ga yadda hayaki mai yawa ya turnike wurin. [4] Mai yiyuwa ne an shirya tashin bama-baman ne domin yin sanadin asarar rayuka da dama.[1] Bam ɗin da aka ɗana a cikin motar ya sa motocin da ke kusa da wurin suka tarwatse.[5]

Jami’an kashe gobara da masu aikin ceto sun yi ƙoƙarin isa wuraren da bama-baman suka tashi, amma “dubban” mutane ne ke tserewa daga yankin.[1] An sanya bama-baman don kashe mutane da yawa, ba tare da nuna bambanci ba na addini [1] ta hanyar amfani da dabara, (ta kashe mutane, bayan anzo ana ceton waɗanda suka jikkata, sai kuma a tashi bam na biyu da zai yi sanadiyar mutuwar Mutanen wurin ciki hard waɗanda suka je bada agajin gaggawa).[3][1] Sojoji sun kafa shingayen binciken ababen hawa a yankin, inda wasu suka gudanar da binciken ababen hawa. Ana sa ran adadin gawarwaki zai ƙari, [5] kuma an ƙona wasu gawarwakin da ba a iya tantance su ba.[3] Adaɗin waɗanda suka mutu ya kai 46 cikin sauri zuwa adadi na 118 yayin da aka share baraguzan ginin wuraren da suka ruguje.[3] Duk da haka, wasu sun ƙiyasta adadin ya kai 150.[6]

Gida Najeriya

[gyara sashe | gyara masomin]
  •  Nigeria – Shugaba Goodluck Jonathan ya yi Allah-wadai da tashin bama-baman,[1] ya kuma kira harin da "mummunan hari kan ƴancin ɗan adam",[1] su kuma mayaƙan ya kira su da, "masu zalunci da mugunta".[3]

Ƙasashen Duniya

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Turkiyya – Ma'aikatar Harkokin Waje (Turkiyya) ta bayyana cewa, "Mun samu labari da bakin ciki game da waɗannan hare-haren bama-bamai". Turkiyya ta yi kakkausar suka ga hare-haren da ake kai wa ‘yan Najeriya, tare da mika ta’aziyyarmu ga gwamnatin Najeriya da al’ummarta da kuma fatan samun sauki ga waɗanda suka jikkata.[7]
  •  United Kingdom – Sakataren harkokin wajen Birtaniya, William Hague ya kira harin da aka kai a Jos a matsayin "laifi mai ban tsoro da rashin mutuntaka".[2]
  •  United States – Ma'aikatar Jiha ta Amurka ta baƙin mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurkan, ta ce harin bam, da sauran hare-haren baya-bayan nan da aka ɗora wa alhakinsa kan ƙungiyar Boko Haram, ayyukan ta’addanci ne marasa kan gado.[2]
  1. 1.00 1.01 1.02 1.03 1.04 1.05 1.06 1.07 1.08 1.09 1.10 1.11 1.12 "Nigerian twin bomb explosions kill dozens in Jos". BBC. 20 May 2014. Retrieved 20 May 2014.
  2. 2.0 2.1 2.2 2.3 "Nigeria violence: 'Boko Haram' kill 27 in village attacks". BBC. BBC. 21 May 2014. Retrieved 21 May 2014.
  3. 3.0 3.1 3.2 3.3 3.4 Jonah, Adamu; Igboeroteonwu, Anamesere (20 May 2014). "Bombings kill at least 118 in Nigerian city of Jos". Reuters. Retrieved 21 May 2014.
  4. 4.0 4.1 4.2 "2 explosions hit bus station in central Nigeria city". Fox News. 20 May 2014. Retrieved 20 May 2014.
  5. 5.0 5.1 5.2 Mark, Monica (21 May 2014). "Nigeria bombings leave over a hundred dead in city of Jos". The Guardian. Retrieved 21 May 2014.
  6. "none". The Punch Nigeria Vol 38, No 20, 666. 21 May 2014. pp. 1, 2 & 7. Missing or empty |url= (help)
  7. "Turkey condemns Nigerian bombings". TurkishPress.com. 21 May 2014. Archived from the original on 22 May 2014. Retrieved 22 May 2014.