Jump to content

Ishaya Audu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Ishaya Audu
Ministan harkan kasan waje

1979 - 1983
Henry Adefope - Emeka Anyaoku (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa 1 ga Maris, 1927
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Mutuwa Tarayyar Amurka, 29 ga Augusta, 2005
Karatu
Makaranta Jami'ar Ibadan
University of Liverpool (en) Fassara
University of London (en) Fassara
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Mai wanzar da zaman lafiya da Malami
Employers Jami'ar Lagos
University of Rochester (en) Fassara
Imani
Jam'iyar siyasa Jam'iyyar National Party of Nigeria

Ishaya Sha'aibu Audu an haifeshi a ranar ɗaya (1 ga watan Maris, shekara ta alif ɗari tara da ashirin da bakwai 1927 - 29 ga Agusta, 2005) ya kasance likita na Nijeriya, farfesa, kuma ɗan siyasa.[1] Ya yi ministan harkokin waje (Ministan Harkokin Waje) daga 1979 zuwa 1983 a karkashin Shehu Shagari.[2][3]

Rayuwa, ilimi, da kuma aiki a makarantu

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Audu a ranar 1 ga watan Maris, shekara ta alif ɗari tara da ashirin da bakwai 1927 a Anchau Anchau wani ƙauye kusa da Zariya dake a jihar Kaduna Kaduna ga mahaifinsa wanda ya musulunta zuwa Kiristanci.[4] Tunda farko ya yi karatu a Makarantar St. Bartholomew da ke Wusasa, ya koma Yaba Higher College a Legas. sannan ya tafi Kwalejin Jami’a, Ibadan (wanda aka sauya masa suna zuwa Jami’ar Ibadan) a shekara ta alif ɗari tara da arba'in da takwas 1948. A cikin shekara ta alif ɗari tara da hamsin da ɗaya 1951, ya tafi Jami’ar London taIngila, inda ya tsaya har zuwa shekara ta alif ɗari tara da hamsin da huɗu 1954. A cikin shekara ta alif ɗari tara da hamsin da biyar 1955, ya yi karatu a Jami’ar Liverpool (ita ma a Ingila) . A shekarar alif ɗari tara da hamsin da takwas 1958 ne ya auri matarsa, Victoria, wacce ta haifa masa yara shida 6.[5]Cite error: The opening <ref> tag is malformed or has a bad name

Harkar siyasa

[gyara sashe | gyara masomin]

Audu ya kasance memba na Jam’iyyar Jama’ar Najeriya lokacin da Shugaba Shehu Shagari ya ba Audu mukamin Ministan Harkokin Waje a shekara ta alif ɗari tara da saba'in da tara 1979. Ya kuma yi aiki a matsayin Jakadan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya. Bayan kifar da gwamnatin Shagari a shekara ta alif ɗari tara da tamanin da uku 1983 da Janar Muhammadu Buhari ya yi (da maye gurbin Jamhuriya ta biyu da mulkin kama-karya na soja), Audu ya tsare shekara guda.[6][7][8]

  1. Taiwo, Gidado (16 November 2012). "Daily Trust". Retrieved 20 May 2020.
  2. Chila Andrew Aondofa (2019-09-30). "ISHAYA AUDU: The legacy of Selfless Service". The Abusites (in Turanci). Archived from the original on 2021-01-26. Retrieved 2020-05-30.
  3. "https://blerf.org/index.php/biography/audu-reverend-professor-ishaya-shaaibu/". External link in |title= (help); Missing or empty |url= (help)
  4. Ozigi, Albert. "Tribute to prof. Ishaya Audu". Daily Trust Online. Media Trust Nigeria, Limited. Archived from the original on 2006-11-04. Retrieved 2007-04-29.
  5. Onyekwere, Joseph (2005-09-05). "A Medical Icon Goes Home". Newswatch Communications. Archived from the original on 2007-09-27. Retrieved 2007-04-29.
  6. Aluwong, Jeremiah (2019-11-10). "Nigerians in History: Ishaya Shuaibu Audu • Connect Nigeria". Connect Nigeria (in Turanci). Archived from the original on 2019-12-16. Retrieved 2020-05-27.
  7. "https://web.archive.org/web/20061104133838/http://www.dailytrust.com/archives/Monday26%20Sept2005/opinion2.htm". External link in |title= (help); Missing or empty |url= (help)
  8. {{Cite web|title=https://www.theabusites.com/ishaya-audu-legacy/ Archived 2021-01-26 at the Wayback Machine