Jump to content

Kisan gilla a kwalejin Gujba

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentKisan gilla a kwalejin Gujba
Map
 11°30′08″N 11°56′04″E / 11.5022°N 11.9344°E / 11.5022; 11.9344
Iri Kisan Kiyashi
Bangare na Rikicin Boko Haram
Kwanan watan 29 Satumba 2013
Wuri Gujba
Ƙasa Najeriya

A ranar 29 ga watan Satumba, 2013, wasu ƴan bindiga na ƙungiyar Boko Haram sun shiga ɗakin kwanan dalibai na maza a cikin makarantar Kwalejin Aikin Noma da ke Gujba a Jihar Yobe a Najeriya, inda suka hallaka dalibai da malamai su arba’in da huɗu.[1]

Wai-wa-ye[gyara sashe | gyara masomin]

An kafa kungiyar ta Boko Haram ne a shekara ta 2002 domin yaki da kakkabe kasashen Larabawa a Najeriya, wanda ƙungiyar ke ganin shi ne tushen aikata laifuka a ƙasar.[2] Daga shekara ta 2009 zuwa 2013, tashe-tashen hankula, rikice-rikice masu nasaba Boko Haram ya yi sanadin mutuwar mutane dubu 3,600, ciki har da fararen hula 1,600.[3][4] A tsakkiyar watan Mayun shekara ta 2013, gwamnatin tarayya ta saka dokar ta ɓaci a jihohin Adamawa, Borno, da Yobe, da nufin kawo ƙarshen ta'addancin ƴan ta'adan Boko Haram.[3] Sakamakon murkushe ƴan Boko Haram ɗin ya kai ga kame ko kuma kashe ɗaruruwan mayaƙan na Boko Haram, yayin da sauran suka fantsama cikin yankunan tsaunuka, inda suka riƙa kai wa fararen hula hari.[4]

Tun a shekara ta 2010, Boko Haram ke kai hare-hare a makarantu, inda suka kashe ɗaruruwan dalibai. Wani mai magana da yawun ƙungiyar, ya ce; za a ci gaba da kai hare-hare muddin gwamnati ta ci gaba da yin katsalandan ga ilimin kur'ani. Sama da yara dubu 10,000 ne ba sa iya zuwa makaranta a yanzu sakamakon hare-haren da ƴan Boko Haram ke kaiwa.[2] Kuma kimanin mutane dubu 20,000 ne suka tsere daga Yobe zuwa Kamaru a cikin watan Yunin shekarar 2013, domin gujewa afkuwar tashin hankalin rutsawa da su.[4]

Kai hari[gyara sashe | gyara masomin]

Da misalin karfe ɗaya na safe ne ƴan bindigar Boko Haram suka shiga kwalejin inda suka buɗe wuta kan daliban a dai-dai lokacin da ɗaliban suke tsaka da barci.[5] Wurin kwana ɗalibai maza ne kawai suka nufa.[6] Gawarwaki arba'in da biyu ne sojojin Najeriya suka zaƙulo yayin da aka kai goma sha takwas da suka jikkata zuwa asibitin kwararru na Damaturu. Biyu daga cikin waɗanda suka jikkata daga baya sun mutu.[1]

A cewar wani da ya tsira, maharan sun shiga cikin kwalejin ne a cikin motoci guda biyu . Wasu na sanye da kayan sojan Najeriya, kuma kusan dukkan waɗanda aka kashen Musulmai ne, haka zalika dalibai ne. Wannan harin ya zuwa biyo bayan harin da aka kai a ranar 6 ga watan Yuli, 2013 a Mamudo da ke wajen Damaturu wanda yai sanadiyyar mutuwar dalibai 29 da wani malami, wasu an ƙona su da ransu, hakan ya sa aka rufe makarantu da dama a yankin, da kuma wasu hare-haren da aka kai a cikin makon da ya biyo bayan kashe wasu fararen hular kuma su 30. Sunan ƙungiyar Boko Haram, na nufin "ilimin yamma zunubi ne".[1]

Bayan hare-haren, wasu dalibai 1000 sun tsere daga kwalejin. Ga dukkan alamu mayakan sun samu mafaka ne a tsaunin Gwoza, inda suka samu mafaka a cikin kogo daga hare-haren bama-bamai da sojoji suka yi. Rikicin da aka yi da sojojin Najeriya ya yi sanadin mutuwar 'yan ta'adda 100 da sojoji 16. A garin Gwoza da ake jinyar wasu daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su, mayaƙan sun kori jami’an lafiya daga asibitin gwamnati tare da ƙona wasu makarantun gwamnati guda uku, kuma an ce garin ya zama ba kowa. Fiye da mutane dubu 30,000 daga yankin sun yi gudun hijira zuwa Kamaru da Chadi.[1]

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 Adamu, Adamu; Faul, Michelle (29 September 2013). "Boko Haram blamed after attack on Nigerian college leaves as many as 50 dead". The Globe and Mail. Associated Press. Archived from the original on 2 October 2013. Retrieved 1 October 2013.
  2. 2.0 2.1 McElroy, Damien (6 July 2013). "Extremist attack in Nigeria kills 42 at boarding school". The Daily Telegraph. Retrieved 3 October 2013.
  3. 3.0 3.1 "Nigeria school attack claims 42 lives". The Australian. AFP. 6 July 2013. Retrieved 3 October 2013.
  4. 4.0 4.1 4.2 Adamu, Adamu; Faul, Michelle (6 June 2013). "School attack kills 30 in northeast Nigeria". Newsday. AP. Archived from the original on 9 March 2021. Retrieved 3 October 2013.
  5. "Tens killed in Nigeria college attack". Al Jazeera. 29 September 2013. Retrieved 29 September 2013.
  6. "Islamic terrorists kill at least 40 students in attack on Nigerian college". Fox News. 29 September 2013. Retrieved 29 September 2013.

Coordinates: 11°30′08″N 11°56′04″E / 11.5022°N 11.9344°E / 11.5022; 11.9344