Jump to content

Leslie Cagan

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Leslie Cagan
Rayuwa
Haihuwa New York, 1947 (77 shekaru)
ƙasa Tarayyar Amurka
Karatu
Makaranta New York University (en) Fassara
Sana'a
Sana'a peace activist (en) Fassara

 

Leslie Cagan

Leslie Cagan 'yar fafutuka ce Ba’amurkiya, marubuciya, kuma mai shirya gurguzu wanda ke da hannu tare da ƙungiyoyin zaman lafiya da adalci. Itace tsohuwar mai gudanarwa ta ƙasa ta United for Peace and Justice, tsohuwar shugabar kwamitocin hulda da dimokuraɗiyya da zamantakewa, kuma tsohuwar shugabar Rediyon Pacifica.

Rayuwarta ta farko

[gyara sashe | gyara masomin]
Leslie Cagan

An haifi Cagan acikin shekara ta 1947 ga ma'aurata Yahudawa a cikin Bronx, New York City, acikin abin da ta bayyana a matsayin "iyali na ja diaper". Ta halarci taronta na farko na siyasa tun tana ƙaramar yarinya acikin shekarar 1950s, tare da rakiyar iyayenta, waɗanda tsoffin membobin Jam'iyyar Kwaminisanci ne. Kakarta, mai sana'ar dinki, ta kasance memba ta kafa kungiyar Ma'aikatan Tufafi Amalgamated. Ta kammala karatu daga Jami'ar New York a shekara ta 1968 tare da digiri a tarihin fasaha.

Acikin shekara ta 1969, Cagan tana cikin mahalarta na farko na Venceremos Brigade, ƙungiyoyin matasa da suka ziyarci Cuba a ƙarƙashin kulawar girbi sugar. A yayin tafiyarta zuwa Havana, Cagan ta shaida wa wakilin Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press cewa: "Dukkanmu muna goyon bayan juyin juya halin Cuban kuma muna jin cewa ta hanyar tafiyar da aiki tare da Cuban zamu iya nuna goyon baya."

Leslie Cagan

Bayan zabar ƙetare makarantar digiri, Cagan tafara aikinta na rayuwa na inganta dalilai daban-daban, galibi acikin gwagwarmayar yaƙi, yaƙin nukiliya, motsin yancin LGBT, motsin mata, da daidaita dangantaka da Cuba. Jaridar New York Times ta bayyana Cagan a matsayin daya daga cikin "babbar dama na yunkurin ci gaban kasar" da kuma "jimi na kasa acikin gwagwarmayar yaki."

Acikin ƙarshen shekarar 1960s – farkon shekara ta 1970s, Cagan ta kasance da hannu sosai tare da Black Panther Party. Cagan ta nuna rashin amincewarta da tsare Mumia Abu-Jamal, 'yar jam'iyyar Black Panther Party da aka samu da laifi kuma aka yanke masa hukuncin kisa kan kisan dan sanda Daniel Faulkner a shekara ta 1981.

A ranar 12 ga watan Yuni, shekara ta 1982, Cagan ta kasance jagoran shirya zanga-zangar adawa da makaman nukiliya da aka gudanar a birnin New York, wanda ta samu halartar dubban daruruwan masu fafutuka. Itace shugabar zanga-zangar neman 'yancin 'yan luwadi da madigo a shekara ta 1987.

Leslie Cagan

Acikin shekara ta 2002 tana cikin wadanda suka kafa kungiya ta zaman lpy da gaskiya a left wing coalition na sama da dubu dari uku international and U.S based organization Wanda sun bayyana abunda suke nufin gudanarwa.