Lucie Castets
Lucie Castets | |||
---|---|---|---|
Oktoba 2023 - ga Augusta, 2024 | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Caen, 3 ga Maris, 1987 (37 shekaru) | ||
ƙasa | Faransa | ||
Mazauni | Caen | ||
Harshen uwa | Faransanci | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Q125842633 2005) Lycée Louis-le-Grand (en) (2005 - 2007) Sciences Po (en) (2005 - 2011) French masters degree (en) Fudan University (en) (2006 - 2006) London School of Economics and Political Science (en) (2009 - 2010) École nationale d'administration (en) (2012 - 2013) | ||
Harsuna |
Faransanci Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | official (en) , gwagwarmaya, spokesperson (en) , research associate professor in France (en) da ɗan siyasa | ||
Employers |
Bureau central de tarification (en) French Consulate General, Shanghai (en) (2007 - 2008) Direction générale du Trésor (en) (ga Janairu, 2014 - Satumba 2018) Sciences Po (en) (Disamba 2014 - ga Janairu, 2017) Tracfin (en) (Satumba 2018 - ga Augusta, 2020) Financial Action Task Force (en) (ga Janairu, 2019 - municipality of Paris (en) (Satumba 2020 - ga Augusta, 2024) Paris Dauphine University (en) (Satumba 2022 - Oktoba 2023) | ||
Mamba | Nos Services Publics (en) | ||
IMDb | nm13729679 |
Lucie Castets (an haife ta a shekara ta 1987 [1]) ma'aikaciyar gwamnatin kasar Faransa ce kuma masaniyar tattalin arziki. Tana da alaka da Jam'iyyar Socialist, New Popular Front ta zabi Castets don zama Firayim Ministan kasar Faransa bayan Zaben ’yan majalisu na 2024.
Kuruciya da ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Castets a Caen ga iyayen da suka yi aiki a matsayin masu nazarin kwakwalwa, kuma sun zauna a Caen har ta kai shekaru 18.[1][2] Ta koma Paris don yin karatu a Lycée Louis-le-Grand, sannan daga baya ta karanci Tattalin arzikin siyasa da dokar jama'a a makarantar Sciences Po.[3] Ta sami digiri na biyu daga Sciences Po da kuma Makarantar Tattalin Arziki ta Kasar Landan kuma ta yi karanci Chananci a Jami'ar Fudan da ke Shanghai, kafin ta kammala karatu daga École nationale d'administration a shekarar 2013.
Ayyukan gwamnati
[gyara sashe | gyara masomin]Castets ta fara aikinta ga gwamnatin kasar Faransa a shekara ta 2007, ta yi aiki a matsayin mataimakiya ga jami'in al'adu a Babban Ofishin Jakadancin Faransa a Shanghai tsakanin 2007 zuwa 2008. [4][5] Ta yi aiki da Bankin Duniya a shekara ta 2011, da farko ta yi aiki a kan ayyukan da suka shafi hikimar kudi.[6] A shekara ta 2014, tayi aiki a Direction générale du Trésor a cikin Ma'aikatar Tattalin Arziki da Kudi, sannan ta zama kwamishinan gwamnati a cibiyar Bureau central de tarification. [7][8]
Tsakanin 2018 da 2020, Castets ta jagoranci wani sashi a Tracfin a cikin Ma'aikatar Tattalin Arziki da Kudi, Hukumar leken asiri da ke da alhakin yaki da zagayawar miyagun kudade da basu bisa ka'ida, karkatar da kudi, da kuma tallafawa ta'addanci.[9] A shekara ta 2020, Castets ta shiga gwamnatin magajin gari na Paris Anne Hidalgo, ta zama mai ba da shawara kan tattalin arziki.[1] A watan Oktoba na shekara ta 2023, Hidalgo ta nada ta a matsayin Daraktan Kudi da Siyayya a ofishin Hidalgo.[10][8]
Ayyukan ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Tsakanin 2014 zuwa 2017, Castets ta kasance malamar tattalin arziki a jami’ar Sciences Po . [9] A shekara ta 2022, ta zama farfesa a fannin tattalin arziki a Jami'ar Paris Dauphine, kuma an wallafa ta a cikin mujallar Alternatives économiques .[1]
Ayyukan siyasa
[gyara sashe | gyara masomin]Castets ta kasance memba ta Jam'iyyar Socialist daga shekara ta 2008 zuwa 2011, lokacin da ta kasance mai goyon bayan Martine Aubry da Union of the Left . [1] Ta yi aiki da ƙungiyar Besoin d'un gauche a wajen Pierre Moscovici da kuma Point d'ancre think tank.[11][12] Castets ta shiga siyasa a karo na farko bayan an zabe ta don tsayawa a matsayin ’uar takarar Jam'iyyar Socialist a Zaben yanki na 2015 a Normandy, kodayake ba ta yi nasarar lashe zaben ba.[7][13][14]
Castets ta bar Jam'iyyar Socialist a shekara ta 2011, saboda rashin amincewa da salon jagorancin siyasa da François Hollande ya daukan wa jam'iyyar.[10] Koyaya, ta ci gaba da kasancewa tare da jam'iyyar kuma ta shiga cikin kamfen na Anne Hidalgo a lokacin Zaben shugaban kasa na 2022, kuma ta kusanci Clementine Autain.
A shekara ta 2021, Castets ta kafa kungiyar Nos services public, wanda ta zama ɗaya daga cikin masu magana da yawun kungiyar guda uku.[9] Kungiyar ta yi burin zama "murya cikin gida” don "bayyana rashin aiki da kuma bada shawarwari" don inganta Ayyukan jama'a a Faransa.[9] Ta sami shahara a wurin jama'a a 2022, lokacin da ta tambayi Stanislas Guerini a shirin talabijin na C ce soir game da karuwar amfani da kamfanonin shawarwari da tsadar da ke tattare da su, a fuskar abin da ta bayyana a matsayin raguwar yawan ma'aikatan gwamnati, waɗanda ke iya aiwatar da irin wannan ayyuka a farashi mai rahusa.
Tsayar da ita matsayin Firayim Minista
[gyara sashe | gyara masomin]A watan Yulin 2024, New Popular Front ta tsayar da Castets a matsayin ‘yar takarar Firayim Ministan kasar Faransa, bayan zaben majalisar dokoki na 2024. [8][15] Bayan tsayar da ita, Castets ta ce abubuwan da ta fi ba fifiko na siyasa sun hada da maido da fasalin fansho na Emmanuel Macron, sake fasalin haraji don tabbatar da cewa "kowa na biyan hakkin su daidai", da kuma inganta ikon siye ta hanyar haɓaka albashi da biyan kuɗin amfanin zamantakewa.[16] Castets ta kuma ba da shawara don ƙarfafa ayyukan jama'a tare da manufar watsi da raguwa a cikin hakkoki mazu nisa, tana mai cewa "rugujewar ayyukan jama'ar wani ɓangare ne na abin da ya haifar da kuri'un National Rally". Castets kuma memba ce ta ofishi da kwamitin daraktoci na Kungiyar bincike na Hakkoki masu Nisa, tare da Thomas Portes da Caroline Fiat na La France Insoumise da kuma Marine Tondelier na The Ecologists. [7][17][18]
Bayan zaben ta, Macron ya ki nada ta a kujerarvta, yana mai ikirarin cewa ba zai yanke wata shawara ba kafin karshen Wasannin Olympics na bazarar 2024 da kuma cewa "abun tambayar ba wai sunan ba ne", amma wane gwamnati mai rinjaye za a kafa a Majalisar Dokokin Kasar.[19][20] Castets ta yi iƙirarin cewa yiwuwar kafa gwamnati Tare da hadin gwiwar Macron ba zai yiwu ba, saboda rashin jituwa mai zurfi tsakanin hadin gwiwan biyu, kuma ta bukaci Macron da ta yarda da zaben ta.[21][22]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 "Lucie Castets (NFP) : la page Wikipédia de la candidate pour le poste de Premier ministre supprimée, "C'est cocasse"". Marie France, magazine féminin (in Faransanci). 2024-07-23. Retrieved 2024-07-24. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":3" defined multiple times with different content - ↑ "Qui est Lucie Castets, proposée par le Nouveau Front populaire pour Matignon ?". Le Nouvel Obs. 23 July 2024.
- ↑ "Qui est Lucie Castets, l'inconnue proposée par la gauche pour Matignon? - Le Temps" (in Faransanci). 2024-07-24. ISSN 1423-3967. Retrieved 2024-07-24.
- ↑ "France – Qui est Lucie Castets, la nouvelle candidate pour le poste du chef du gouvernement ?". Tunisie Numérique. 23 July 2024.
- ↑ "Extrait de la fiche de Mme Lucie Castets". LesBiographies.com.
- ↑ Chatain, Pierre-Laurent. "Protecting mobile money against financial crime" (PDF). World Bank.
- ↑ 7.0 7.1 7.2 Blanchard, François (23 July 2024). "Haute fonctionnaire, ex-conseillère d'Hidalgo : qui est Lucie Castets, la candidate au poste de Première ministre du NFP ?". BFM TV. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":bfm" defined multiple times with different content - ↑ 8.0 8.1 8.2 "French left picks Parisian Lucie Castets as PM candidate after days of bickering". POLITICO (in Turanci). 2024-07-23. Retrieved 2024-07-23. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":0" defined multiple times with different content - ↑ 9.0 9.1 9.2 9.3 "EXCLUSIF : Lucie Castets proposée par le Nouveau Front populaire au poste de Première ministre - L'Humanité". Humanité. 2024-07-23. Retrieved 2024-07-23. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":2" defined multiple times with different content - ↑ 10.0 10.1 Lepelletier, Pierre (23 July 2024). "Matignon : avec Lucie Castets, le Nouveau Front populaire choisit une haute fonctionnaire comme « première-ministrable »". Le Figaro. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":5" defined multiple times with different content - ↑ "Qui est Lucie Castets, proposée par le Nouveau Front populaire pour le poste de Première ministre ?". France Info. 24 July 2024.
- ↑ "Promotion Jean Zay (2012 - 2013)" (pdf). ENA.
- ↑ Lascoux, Benoît (9 October 2015). "Seulement deux sortants sur la liste PS". Ouest-France.
- ↑ Fouda, Emile (9 October 2015). "Régionales: la liste des candidats socialistes du Calvados présentés par les présidents de Haute et Basse-Normandie". actu.fr.
- ↑ "French left bloc New Popular Front agrees to propose Lucie Castets for prime minister". France 24 (in Turanci). 2024-07-23. Retrieved 2024-07-23.
- ↑ "La gauche propose Lucie Castets pour Matignon, Emmanuel Macron dit qu'il ne nommera personne avant mi-août". rts.ch (in Faransanci). 2024-07-23. Retrieved 2024-07-23.
- ↑ "Le Bureau". Observatoire national de l'extrême droite. 21 December 2020.
- ↑ "Conseil d'administration". Observatoire national de l'extrême droite.
- ↑ Breeden, Aurelien (23 July 2024). "Macron Rejects French Left's Pick for Prime Minister". New York Times.
- ↑ "« La question n'est pas un nom », Macron esquive l'idée Lucie Castets soufflée par le NFP". Le HuffPost (in Faransanci). 2024-07-23. Retrieved 2024-07-23.
- ↑ Duguet, Margaux; Dubar, Louis (24 July 2024). "Nouvelle Assemblée nationale : Lucie Castets juge "impossible" une "coalition avec le camp présidentiel du fait de désaccords profonds"". France Info.
- ↑ Le Baron, Simon (24 July 2024). "Lucie Castets : "Je demande au Président de prendre ses responsabilités et de me nommer Première ministre"". France Inter.
- Pages with reference errors
- CS1 Faransanci-language sources (fr)
- CS1 Turanci-language sources (en)
- Wikipedia articles with faulty GND identifiers
- Pages with red-linked authority control categories
- Wikipedia articles with SUDOC identifiers
- Wikipedia articles with VIAF identifiers
- Wikipedia articles with WorldCat-VIAF identifiers
- Rayayyun mutane
- Haihuwan 1987