Jump to content

Maher Al-Mu'aiqily

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Maher Al-Mu'aiqily
Rayuwa
Haihuwa Madinah, 7 ga Janairu, 1969 (55 shekaru)
ƙasa Saudi Arebiya
Harshen uwa Larabci
Karatu
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a Liman
Imani
Addini Musulunci

Maheer Bin Hamad Bin Almu'aiqily Al-Balawi an haife shi a Madina (a ranar 7 ga watan Janairu shekarar 1969) Limami kuma mai Khuɗuba a Masallacin Harami da ke ƙasar Saudiyya.[1][2]

Rayuwar shi da karatu

[gyara sashe | gyara masomin]

Ya yi karatu a Kwalejin Malamai da ke Madina, inda ya kamala karatunsa a matsayin malamin lissafi, sannan ya koma Makkah Al-Mukarrama a matsayin malami, sannan ya zama jagoran ɗalibai a makarantar Yarima Abdulmajeed da ke Makkah. Ya yi digiri na biyu a shekara ta, 1425 bayan hijira a fannin ilimin fiƙihun Imam Ahmad bin Hanbal a Kwalejin Shari’a ta Jami’ar Umm Al-Qura kuma ya sami digiri na uku a fannin tafsiri. Yayi aiki a matsayin mataimakin farfesa a sashin nazarin shari'a a kwalejin nazarin shari'a da ƙa'idojin shari'a na jami'ar Umm Al-Qura. kuma yana riƙe da matsayin Mataimakin Shugaba don Nazarin Digiri da Binciken Kimiyya. Ya samu digiri ta biyu a jami'ar Umm Al-Qura, a kwalejin Shari'a, tsangayyar Fiqhu (Fiqhu) a shekara ta, 1425 bayan hijira inda yayi nazarin Littafi mai suna: Imam Ahmad Ibn Hanbal Mas'alolin Fikihu. Ya sami digirinsa ta uku a jami'ar Umm Al-Qura a shekara ta, 1432 bayan hijira, wanda yayi bincike akan littafin (Tuhfat Al-Nabih, Sharh Al-Tanbih) (na Imam Shirazi a fikihu Shafi'i). Har ila yau, ya sami takardar shaidar digirin digirgir, ya sake samun digirin digirgir a fannin shari'a a ranar 28 ga watan Muharram a shekarar, 1434 na Hijiriyya wanda yayi daidai da 11/12/2012 Miladiyya.

Limamin Masallacin Harami

[gyara sashe | gyara masomin]

Ya jagoranci huɗuba a Masallacin Al-Saadi da ke gundumar Al-Awali a cikin Makkah Al-Mukarramah. Ya karɓi jagorancin Sallah a Masallacin Manzon Allah S A W a watan Ramadan mai alfarma a shekara ta,1426 bayan hijira da kuma, 1427 bayan hijira. Kuma ya jagoranci Sallar Tarawihi da Tahajjud a Masallacin Harami na watan Ramadan a shekara ta, 1428 bayan hijira, daga an naɗa shi Limamin Masallacin Harami a cikin wannan shekarar, yana cikin limaman Harami har zuwa yanzu.

  1. "Biography Of Sheikh Maher Al-Muaiqly, Imam Of The Grand Mosque In Mecca". المرسال. 27 February 2019. Archived from the original on 27 February 2019. Retrieved 8 May 2022.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)
  2. "جامعة أم القرى/Ummul Qura University". uqu.edu.sa. 24 August 2015. Archived from the original on 24 August 2015. Retrieved 8 May 2022.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link)