Jump to content

Mamman Jiya Vatsa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mamman Jiya Vatsa
ma'aikatar Babban birnin tarayya

1984 - Disamba 1985
Sarki kuma ɗan Siyasar Najeriya - Hamza Abdullahi
Rayuwa
Haihuwa Bida, 3 Disamba 1940
ƙasa Najeriya
Mutuwa Lagos,, 5 ga Maris, 1986
Yanayin mutuwa  (gunshot wound (en) Fassara)
Karatu
Makaranta Indian Military Academy (en) Fassara
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da maiwaƙe
Digiri Janar

Mamman Jiya Vatsa OFR (3 Disamba 1940 zuwa; 5 Maris 1986) ya kasance tsohon janar ɗin sojin Najeriya ne kuma mai-waƙe wanda yayi aiki amatsayin Minista na Babban Birnin Tarayya Abuja, kuma mamba ne na Majalisar Ƙoli ta Sojojin Najeriya

A 5 Maris 1986, gwamnatin soji ta Janar Ibrahim Babangida ta sanya an kashe shi (wanda abokinsa ne a yarinta) biyo bayan wani hukunci da Kotun soji ta yanke masa akan kama shi da laifin yin zagon ƙasa ga ƙasar Najeriya da ƙoƙarin aiwatar da juyin mulki.

Farkon rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

Vatsa ya kasance aboki ne tun a yarinta da Ibrahim Babangida kuma sun kasance tsarakin juna tun a lokacin da suke makaranta ɗaya. Kamar Babangida, Vatsa shi ma ya halarci Kwalejin Gwamnati Bida daga 1957 zuwa 1962 sannan ya fara aikinsa da shiga Kwalejin Horar da Sojojin Najeriya (Nigerian Military Training College (NMTC)) a 10 Disamba 1962.[1]

  1. Abejide, Olusegun (21 January 2011). IBB – Smart But Foolish: THE FALL OF A GOLIATH. Trafford Publishing, 2011. p. 55. ISBN 9781426955938. Retrieved 11 August 2015.