Margaret Thatcher

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Margaret Thatcher
Margaret Thatcher portrait.jpg
ɗan Adam
jinsimace Gyara
ƙasar asaliBirtaniya, United Kingdom of Great Britain and Ireland Gyara
sunan asaliMargaret Thatcher Gyara
sunan haihuwaMargaret Hilda Roberts Gyara
sunaMargaret, Hilda Gyara
sunan dangiRoberts, Thatcher Gyara
noble titlebaron Gyara
lokacin haihuwa13 Oktoba 1925 Gyara
wurin haihuwaGrantham Gyara
lokacin mutuwa8 ga Afirilu, 2013 Gyara
wurin mutuwaThe Ritz London Gyara
sanadiyar mutuwanatural causes Gyara
dalilin mutuwatransient cerebral isolation Gyara
date of burial or cremation17 ga Afirilu, 2013 Gyara
wajen rufewaRoyal Hospital Chelsea Gyara
ubaAlfred Roberts Gyara
mata/mijiDenis Thatcher Gyara
yarinya/yaroCarol Thatcher, Mark Thatcher Gyara
yaren haihuwaTuranci Gyara
harsunaTuranci Gyara
member ofRoyal Society, Privy Council of the United Kingdom Gyara
significant eventdeath Gyara
makarantaCity Law School, Kesteven and Grantham Girls' School, Somerville College, Jami'ar Oxford Gyara
honorific prefixThe Right Honourable Gyara
wurin aikiLandan Gyara
jam'iyyaConservative Party Gyara
ƙabilaEngland Gyara
addiniMethodism, Church of England Gyara
cutadementia, bladder cancer Gyara
rikiciFalklands War Gyara
archives atNational Library of Wales, Churchill Archives Centre Gyara
official websitehttp://margaretthatcher.org/ Gyara
depicted byMeryl Streep Gyara

Margarate Thatcher (1925-2013) dai itace macen farko data zama Firaministan ƙasar Birtaniya kuma wasa wasa saida ta samu nasara a zaɓukan ƙasar har sau uku, woto dai sau uku tana zama Firaministan ƙasar a jere, tun daga shekarar 1979 da 1983 da kuma shekarar 1987.

An dai hafi Margarate Thatcher ne a ranar 13 ga watan Oktoban 1925. kuma tayi makarantan Firamare na Kesteven da kuma sakandaren 'yan mata ta Grantham da kuma Somerville na jami'ar Oxford.

Kafin kuma ta shiga harkokin Siyasa a shekara ta 1959, ta kasance maibincike na kimiyyar kemistry daga shekarar 1947-54. A shekarar ta 1954 ne kuma ta zama cikakkar lauya. Daga shekarar 1970 zuwa 1974 kuma ta zama sakatariyar harkokin ilmi na Birtaniya.

A zamanin mulki ta ne dai Rhodesiya ta samu 'yancin kai ta zama Zimbabwe a shekarar 1979. Saidai wani abu daya ƙarawa Magarate Thatcher farin jin, shine nasasar da dakarun Indila suka samu a lokacin yaƙin tsibirin Falklands ashekarar 1982, abinda yasa Birtaniyawa suka sake zaɓen ta azaɓen shekara ta 1983. Gama ka ɗan daga cikin abinda take cewa bayan sarandar da Sojojin Angentina sukayi wanda kuma ya kawo ƙarshen Yaƙin, inda take cewa: Ina son sheda maku sarandar da Sojojin Argentina sukayi, wanda ya baiwa Birtaniya nasara a wannan yaƙi na mallakan tsibirin falklands: A shekarar 1990 ne Magarate Thatcher ta sauka daga kan muƙamin Firaministan Birtaniya, kuma sunan mijinta Sir Denis Thatcher. Kuma tana da 'ya'ya biyu Sir Marka Thatcher da kuma Hon. Carol Thatcher da jikoki biyu mace da namiji. Yanzu haka dai Madam Thatcher tana da shekaru 84 a duniya.