Jump to content

Masarautar Bichi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Masarautar Bichi
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin Najeriyajihar Kano
Coordinates 12°13′53″N 8°14′25″E / 12.2313°N 8.2404°E / 12.2313; 8.2404
Map
Fadar masarautar Bichi

Masarautar Bichi masarautar gargajiya ce ta Hausawa a Jihar Kano da ke Arewacin Nijeriya . Fadar ta tana cikin garin Bichi, Karamar Hukumar Bichi. Masarautar Bichi an kafa ta ne a shekarar 2019, lokacin da Gwamnatin Jihar Kano ta ƙirƙiri masarautu huɗu daga tsohuwar masarautar Kano. Masarautar Bichi ta ƙunshi Ƙanana Hukumomi 9 daga jihar Kano. Wadannan ƙananan hukumomin sune Bichi, Bagwai, Shanono, Tsanyawa, Kunchi, Makoda, Dambatta, Dawakin Tofa da Tofa.[1]

Sarkin Bichi na yanzu shine Nasiru Ado Bayero.[2][3] Aminu Ado Bayero shine sarki na farko a masarautar Bichi tun bayan kafuwarta a shekarar 2019.[4][5] A ranar 12 ga Maris, 2020, Gwamnatin Kano ta maye gurbinsa da dan uwansa Nasiru Ado Bayero a matsayin Sarkin Bichi biyo bayan sauke Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga mulkin Kano tare da maye gurbinsa da Aminu Ado Bayero.[6]

  1. "Sanusi's emirate now covers only 10 of 44 Kano LGAs -- and probe continues". TheCable (in Turanci). 2019-05-09. Retrieved 2020-09-10.
  2. "Kano Govt Appoints Nasiru Ado Bayero As New Emir Of Bichi Emirate". Channels Television. Retrieved 2020-09-10.
  3. editor (2020-03-09). "Nasiru Ado Bayero Named Emir of Bichi". THISDAYLIVE (in Turanci). Retrieved 2020-09-10.CS1 maint: extra text: authors list (link)
  4. "An bai wa Aminu Ado Bayero sarautar Bichi". BBC News Hausa. Retrieved 2020-09-10.
  5. Nwachukwu, John Owen (2019-05-16). "Kano emirate: Why I accepted Ganduje's appointment - Bichi Emir, Bayero breaks silence". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2020-09-10.
  6. PRNigeria (2020-03-09). "Bayero's Sons, Aminu and Nasiru Become Emirs of Two Emirates in Kano". PRNigeria News (in Turanci). Retrieved 2020-09-10.