Jump to content

Mohammed Umar Bago

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mohammed Umar Bago
Gwamnan jahar Niger

2023 -
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

11 ga Yuni, 2019 -
District: Chanchaga
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya,

6 ga Yuni, 2015 -
Rayuwa
Haihuwa Minna, 22 ga Faburairu, 1974 (51 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƴan uwa
Abokiyar zama Hajiya Fatima Umaru Bago (en) Fassara
Karatu
Makaranta Jami'ar, Jos
Jami'ar Ambrose Alli
Jami'ar Usmanu Danfodiyo
Jami'ar Calabar
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da Ma'aikacin banki
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Action Congress of Nigeria
All Progressives Congress

Mohammed Umar Bago an haife shi a ranar 22 ga watan Fabrairu shekara ta alif 1974, a garin Minna da ke jihar Niger a Najeriya, Kuma cikakken Banufe ne, dan siyasa a Najeriya. Shi ne danmajalisan mai wakiltan yankin Chanchaga a majalisan taraiyyan Najeriya. Ya nimi kujeran kakakin majalisan taraiyan Najeriya, Kuma ya samu sakamako na biyu yayin da Femi Gbajabiamila ya lashe zaben a shekara ta dubu biyu da shatara (2019). Sannan kuma cikakken dan jam'iyar All Progressive Congress wato (APC).

Rayuwar farko da Ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a shekara ta alif 1974, Hon. Umar Bago ya halarci Makarantar Firamare ta Marafa, Minna da Kwalejin Gwamnatin Tarayya dake Jos. Ya sami takardar shaidar karatu ta yammacin Afirka WAEC. Ya sami digiri na farko a kimiyyar siyasa a Jami'ar Usman Danfodio, Sokoto.

Hon. Umaru Bago ya sami mabanbanta diflomar bayan da digiri dakuma digiri na biyu, gami da difloma na digiri na biyu a kan fannin gudanarwa daga Jami'ar Fasaha ta Tarayya Minna a shekara ta 2001, Master of Business Administration (MBA) a gudanar da sha'anin kasuwanci a Jami'ar Ambrose Ali, Ekpoma, a shekara ta 2003, da kuma digiri na biyu a fannin kudi a Jami'ar Calabar a shekara ta 2005. Ya kuma kasance fitaccen tsohon ɗalibi ne daga Jami'ar Cambridge a Ingila a shekarar 2014. [1]

  1. Obi, Ifoh (11 June 2019). "Gbajabiamila Beats Bago To Emerge Speaker 9th Assembly". Newsreel Daily (in Turanci). Archived from the original on 8 July 2020. Retrieved 8 July 2020.