Jump to content

Moji Akinfenwa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Moji Akinfenwa
mutum
Bayanai
Bangare na Nigerian senators of the 4th National Assembly (en) Fassara
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Sunan dangi Akinfenwa (mul) Fassara
Shekarun haihuwa 1930
Wurin haihuwa jahar Osun
Lokacin mutuwa 10 Oktoba 2019
Wurin mutuwa Jahar Ibadan
Harsuna Yarbanci da Turanci
Sana'a ɗan siyasa
Muƙamin da ya riƙe mamba a majalisar dattijai ta Najeriya
Ɗan bangaren siyasa Alliance for Democracy (en) Fassara

Mojisoluwa O Akinfenwa (1930 - ranar 10 ga watan Oktoban 2019) ɗan siyasar Najeriya ne wanda aka zaɓa Sanata mai wakiltar Osun ta Gabas ta jihar Osun, Najeriya a farkon jamhuriya ta huɗu ta Najeriya, wanda ya tsaya takara a dandalin Alliance for Democracy (AD). Ya fara aiki a ranar 29 ga watan Mayun 1999.[1] Bayan isowarsa Majalisar Dattawa a cikin watan Yunin 1999, an naɗa shi a kwamitocin Zaɓe, Sabis na Majalisar Dattijai, Ma’adanai masu ƙarfi, Banki & Kuɗi da Ilimi.[2]

Tarihin Rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

A cikin watan Disamban 2003 Alhaji Ahmed Abdulƙadir, shugaban jam’iyyar Alliance for Democracy na ƙasa mai barin gado ya rubuta wa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) naɗa Akinfenwa a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa.[3] Jam’iyyar dai ta rabu gida biyu ne masu adawa da juna, yayin da ɗaya kuma Cif Bisi Akande ya jagoranta. A cikin watan Fabrairun 2004 Hukumar INEC ta kira taron shugabannin AD wanda ya cire shugabannin biyu masu hamayya da juna a ƙoƙarin warware matsalar.[4] Yunƙurin da aka ci gaba da yi na warware rarrabuwar kawuna bai yi tasiri ba. Ƙungiyar siyasa da zamantakewar Yarbawa, Afenifere, ta yi watsi da Akinfenwa, matakin da aka yi suka a taron tsofaffin gwamnonin AD na jihohin Kudu-maso-Yamma a cikin watan Agustan 2004. A cikin wata hira da aka yi da shi a cikin watan Fabrairun 2006 Akinfenwa ya ci gaba da dagewa cewa shi ne shugaban AD, ba Akande ba.

  1. http://psephos.adam-carr.net/countries/n/nigeria/nigerialeg2.txt
  2. https://web.archive.org/web/20091118151316/http://www.nigeriacongress.org/assembly/committees1.htm
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-04-06. Retrieved 2023-04-06.
  4. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-04-06. Retrieved 2023-04-06.