Muhammad Salah

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Simpleicons Interface user-outline.svg Muhammad Salah
Mohamed Salah, Liverpool FC gegen 1. FSV Mainz 05 (Testspiel 23. Juli 2021) 26.jpg
Rayuwa
Cikakken suna محمد صلاح حامد محروس غالي
Haihuwa Nagrig (en) Fassara, 15 ga Yuni, 1992 (30 shekaru)
ƙasa Misra
Harshen uwa Egyptian Arabic (en) Fassara
Ƴan uwa
Abokiyar zama Magy Mohammed Sadek (en) Fassara
Karatu
Harsuna Larabci
Egyptian Arabic (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Al Mokawloon Al Arab SC (en) Fassara2010-20124412
Flag of Egypt.svg  Egypt national football team (en) Fassara2011-6741
Logo FC Basel.svg  FC Basel (en) Fassara2012-20147920
Chelsea F.C.2014-2015192
A.S. Roma (en) Fassara2015-20178334
2022 ACF Fiorentina logo.svg  ACF Fiorentina (en) Fassara2015-2015269
Liverpool FC crest, Main Stand.jpg  Liverpool F.C.2017-180118
 
Muƙami ko ƙwarewa wing half (en) Fassara
Ataka
Lamban wasa 11
Nauyi 71 kg
Tsayi 176 cm
Kyaututtuka
Imani
Addini Musulmi

Mohamed Salah Ghaly (a Larabcin Misira محمد صلا ح غل لي) , An haifeshi a (15) ga watan yuni (1992), kwararren ɗan ƙwallon ƙasar Masar ne wanda yake buga wasa a gasar zakarun Turai da ƙungiyar sa ta Liverpool F.C. kuma yana bugawa a tawagar yan ƙwallon ƙasar Masar.

Salah ya fara ne daga buga ƙwallon sa na kwararru a ƙungiyar sa ta gida El'Makawloon a gasar kwararru ta ƙasar Masar (2011),daganan kuma sai ya wuce ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Besel.A ƙasar Suwizalan, Salah ya samu nasarori da dama kamar (SAFP Golden Player award). Daga nan kuma Salah ya shiga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea F.C akan kwantaragin £11 milyan na yuro a shekarar 2014.Daga nan kuma sai Salah ya sauya sheka da ƙungiyar dake wasanta SERIE 'A' wato Fiorentina a kan kwantaragin £15 milyan na yuro.

Bayan nasarorin da ya samu a Rome Salah daga karshe ya koma ƙungiyar da yake taka leda a yanzu ta Liverpool F.C dake ƙasar Ingila akan kwantaragin yuro na miliyan £36.9,a shekarar 2017.[1]

Fara tashen sa[gyara sashe | gyara masomin]

El Mokawloon[gyara sashe | gyara masomin]

Salah a matsayin matashin ɗan ƙwallo a ƙungiyar El Makawloon. Sai ya shiga ƙungiyar kwararru ta ƙasar sa Masar.[2]

Besel[gyara sashe | gyara masomin]

Salah na wasa da ƙungiyar Besel a Zenit St Petersburg a gasar UEFA Europa League a watan Maris na 2013

Salah ya kafa tarihi sosai a ƙungiyar Besel lokacin da yake buga masu wasa. Kamar a wasan da kungiyar sa ta buga filin wasa na Stadion Rankhof, Salah ya buga zagaye na biyun wasanne kawai amma saida yasamu damar zura kwallaye biyu a raga.[3]

Chelsea[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 23 ga watan Janairu 2014 ne ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta fitar da sanarwar fara yarjejeniya da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Besel kan yiwuwar komar salah kungiyar a kan kwantaragin yuro miliyan £11. A ranar 26 ga Janairu na 2014 ne kuma dai Chelsea ta sake fitar da sanarwar kammala yarjejeniyar ta su inda Salah yazama dan kasar Masar na farko da zai taka leda a Stamford Bridge. A ranr 8 ga Janairun na 2014 ne kuma Salah ya fara nuna bajintar sa a wasan ƙungiyar sa ta Chelsea da kuma ta Newcastle. Ranar 22 ga Maris 2014 Salah yaci ƙwallon sa ta farko a wasan Chelsea da Arsenal.[4]

Salah yana wasa da kungiyar Chelsea a Totrtenham Hotspur ranar 1 janairu 2015

Zaman bashi a Fiotentina[gyara sashe | gyara masomin]

Salah yana wasa da kungiyar Fiorentin a 2015

Ranar 2 fabrairu na 2015 Salah yabar kungir kwallon kafa ta Chelsea zuwa kungiyar kwallon kafa ta Fiorentina a matsayin bashi.

Roma[gyara sashe | gyara masomin]

Ranar 6 Augusta 2015 Salah ya sake komawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Roma a matsayin bashi.[5]

Liverpool[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 22 yuni 2017 ne Salah ya sauya sheka Zuwa ƙungiyar sa ta liverpool akan kwantargin yuro miliyan £42.[6]


Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

Salah a wasan Liverpool da Manchester United a maris 2018
Salah daga hagu a wasan Masar da Tunusiya Augusta 2012
  1. Mohamed Salah" . Barry Hugman's Footballers. Retrieved 1 May 2018.
  2. Hossam Rabie (6 June 2018). "Egyptian soccer star's village has mixed feelings about native son" . Al-Monitor . Retrieved 20 March 2019.
  3. Abdelrahman, Mahmoud (3 January 2019). "Inside Salah's first club: A debut at 15, half-time tears & three-hour journeys to training" . Goal.com . Retrieved 18 January 2021.
  4. Trevor Haylett (3 May 2013). "Basel take heart after Chelsea defeat" . UEFA. Retrieved 3 May 2013.
  5. Fiorentina 1–2 Roma" . BBC Sport . 25 October 2015. Retrieved 25 August 2018.
  6. Critchley, Mark (30 June 2017). "Liverpool signing Mohamed Salah and Chelsea cleared of wrongdoing in Fiorentina loan court case" . The Independent. Retrieved 3 January 2021.