Jump to content

Muhammad Yunus Jaunpuri

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Muhammad Yunus Jaunpuri
Rayuwa
Haihuwa Jaunpur (en) Fassara, 2 Oktoba 1937
ƙasa Indiya
British Raj (en) Fassara
Dominion of India (en) Fassara
Indiya
Mutuwa Saharanpur (en) Fassara da Saharanpur district (en) Fassara, 11 ga Yuli, 2017
Karatu
Makaranta Mazahir Uloom (en) Fassara
Harsuna Urdu
Harshen Hindu
Farisawa
Larabci
Ɗalibai
Sana'a
Sana'a muhaddith (en) Fassara, Ulama'u da marubuci
Wanda ya ja hankalinsa Muhammad Al-Bukhari, Ibn Taymiyyah, Ibn Hajar al-Asqalani da Zakariyya Kandhlawi (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci
Mabiya Sunnah

Muhammad Yunus Jaunpuri (an haife shi a watan Oktoban shekarata1937 kuma ya mutu a ranar 11 ga watan Julin 2017) ya kasance malamin Hadisi na Islama na Kasar Indiya, kuma tsohon Shaykh al-Hadith na Mazahir Uloom, Saharanpur. Yana daga cikin manyan dalibai da almajiran Muhammad Zakariyya Kandhlawi.

Tarihin rayuwa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Jaunpuri a ranar 2 ga Oktoban shekarar 1937 a Jaunpur. Ya kammala karatu daga Mazahir Uloom, Saharanpur a shekara ta 1961. [1]

Jaunpuri ya koyar da littattafan Hadisi daban-daban a cikin Mazahir Uloom, Saharanpur. An nada shi a matsayin Shaykh al-Hadith na Jamia a shekara ta 1388 AH. Ya karantar da Sahih Al-Bukhari a cikin Mazahir Uloom, Saharanpur kusan shekaru 50. Daliban sa sun hada da Yusuf Motala da Abdur Raheem Limbada.[ana buƙatar hujja]

Jaunpuri ya mutu a ranar 11 ga watan Yulin shekara ta 2017. Mutane sama da miliyan daya ne suka halarci jana’izar sa kuma Talha Kandhlawi, dan Muhammad Zakariyya Kandhlawi ne ya jagoranci addu’ar. Babban malamin addinin Islama na duniya Ismail ibn Musa Menk ya nuna alhinin rasuwarsa. Shima mawakin Indiya kuma masani Fuzail Ahmad Nasiri ya nuna alhininsa kuma ya ce Jaunpuri fitaccen malamin hadisi ne.[2][3][4][5]

Rayuwar mutum

[gyara sashe | gyara masomin]

Jaunpuri bai zabi yin aure ba kuma ya kasance bai da aure a tsawon rayuwarsa. Fuzail Ahmad Nasiri ya ce an ambaci dalilai da dama na hakan amma mafi alherin shi ne Jaunpuri bai ga ya iya yin aure ba don haka ya kasance ba shi da aure. Ya ji damuwa da baƙin ciki don ba shi da yara.

Ayyukan adabi

[gyara sashe | gyara masomin]

Littattafan Jaunpuri sun hada da:

  • Al-Yawaqit al-Ghaliyah
  • Kitab at-Tauhid
  • Nawadir al-Hadith
  • Nibrās al-Sārī ilā Riyāḍ al-Bukhārī
  • Nawadir al-Fiqh
  1. "Maulana Yunus Hayat-o-Khidmat by Maulana Mahmud Shabbir". Shaykh Muhammad Yunus Jaunpuri: Nuqoosh-o-Ta'assurat, Tarikhi Dastawez (PDF). Jamia al-Qasim Darul Uloom Islamia, Sapaul. pp. 134–135.
  2. "15vi Sadee Hijri Ke Azeem Muhaddis by Maulana Muhammad Islam Qasmi". Shaykh Muhammad Yunus Jaunpuri: Nuqoosh-o-Ta'assurat, Tarikhi Dastawez. Jamiatul Qasim Darul Uloom Al-Islamiah, Sapaul. p. 209.
  3. "Famous Scholar Shaykh Yunus Jaunpuri (RA) Passed Away on 10/07/2017. His Childhood Collegue [sic] and another famous Scholar from Madina Shaykh Ismail Badat passed away the same day. What a huge loss to the Ummah!". IslamHashTag.com. Retrieved 14 September 2019.
  4. "Shaykh Yunus Jaunpuri Passed Away, And His Funeral Was So Huge!". Retrieved 13 September 2019.
  5. "Final Moments and Passing of Mawlana Yunus Jawnpuri". 14 July 2017. Retrieved 13 September 2019.