Jump to content

Mullah Omar

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Mullah Omar
Prime Minister of Afghanistan (en) Fassara

27 Satumba 1996 - 13 Nuwamba, 2001
Amir al-Mu'minin

3 ga Afirilu, 1996 - 13 Nuwamba, 2001
Amir al-Mu'minin of the Taliban (en) Fassara

1996 - 2001 - Akhtar Mansour (en) Fassara
Supreme Leader of Afghanistan (en) Fassara

1996 - 2001
Rayuwa
Haihuwa Khakrez District (en) Fassara, 1960
ƙasa Kingdom of Afghanistan (en) Fassara
Republic of Afghanistan (en) Fassara
Democratic Republic of Afghanistan (en) Fassara
Islamic State of Afghanistan (en) Fassara
Afghanistan
Mutuwa Zabul (en) Fassara, 23 ga Afirilu, 2013
Makwanci Zabul (en) Fassara
Yanayin mutuwa Sababi na ainihi (Tarin fuka)
Ƴan uwa
Yara
Ahali Abdul Manan Omari (en) Fassara
Karatu
Makaranta Darul Uloom Haqqania (en) Fassara
Jamia Uloom-ul-Islamia (en) Fassara
Harsuna Pashto (en) Fassara
Malamai Qazi Hamidullah Khan (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Aikin soja
Digiri Amir al-Mu'minin
Ya faɗaci War on Terror (en) Fassara
Soviet–Afghan War (en) Fassara
Afghan conflict (en) Fassara
Battle of Arghandab (en) Fassara
Imani
Addini Mabiya Sunnah
Jam'iyar siyasa Islamic and National Revolution Movement of Afghanistan (en) Fassara
IMDb nm12586610
Mullah Omar

Mullah Mohammed Omar (Pashto : ﻣﻼ ﻣﺤﻤﺪ ﻋﻤﺮ , Mullā Muḥammad 'Umar ; ya rayu tsakanim 1960 zuwa 23 April shekarar 2013),[1] An kuma san shi da Mullah Omar, wani ɗan Ƙungiyar jahadi ne a ƙasar Afghanistan kuma babban kwamanda wanda ya kirkiri kasar Masarautar Musulunci ta Afghanistan a shekarar 1996. Kungiyar Taliban ta Nada shi matsayin kwamandan imani ko kuma babban shugaba na kolin musulmai har zuwa lokacin magajin shi Mullah Akhtar Mansour a shekarar 2015. Majiyoyi da dama sun aiyana shi a matsayin shugaban gwamnati na koli a kasar ta Afghanistan tun daga kirkirar masarautar Musulunci ta kasar mai hedikwata a birnin Kandahar.[2]

Tarihin rayuwar sa

[gyara sashe | gyara masomin]

An haife shi a wata iyali masu ɗan ƙaramin ƙarfi kuma waɗanda basu da wata dangantaka Siyasa, Omar ya shija cikin Mujahidai Afghanistan a lokacin yaƙin ƙasar da Taraiyar Sobiyat a shekarun 1980. Ya samar da ƙungiyar Taliban a shekarar 1994 kuma zuwa shekarar 1995 ƙungiyar ta kama mafiyawan kudancin ƙasar ta Afghanistan a Satumban shekarar 1996, Taliban ta karbe iko da birnin Kabul babban birnin kasar. A lokacin jagorancin sa matsayin sarkin Afghanistan, Omar yakan bar birnin na Kandahar shi kadai ba tare da wani tsaro ba domin ya hadu da mutanen wajen gari. An san shi da rashin yawan maganganu ko surutai kuma yafi son rayuwa a muhallin daba kayatacce ba. Kasar Amurika ta shiga Neman sa ruwa a jallo sakamakon nuna goyon bayan sa da yayi ga Osama bin Laden da kungoyar sa ta al-Qaeda a harin 11 ga satumba. Ya kalubalanci Amurika matuka a kokarin ta na dakatar da shi tare kuma da umartar mayakan sa na Taliban da kai hare hare kan sojojin srundunar tsaro ta NATO. Omar ya rasu a Afrilun shekarar 2013 sakamakon jinya da yayi, amma kungiyar ta Taliban ta ki bayyana rasuwar tasa har zuwa shekarar 2015 sannan ta baiyana.[3] [4]

Farkon rayuwar sa

[gyara sashe | gyara masomin]

Kamar yarda wasu majiyoyi suka ce, an haifi Omar ne a wani lokaci tsakanin shekarar 1950 da shekarar 1962 a ƙauye a yankin Kandahar, masarautar Afghanistan. Wasu sun kaddara shekarar haihuwar sa a shekarar 1950 ko shekarar 1953 ko a ƙarshen 1966. Babu tabbacin a inane aka haife shi; amma wani waje da aka fi sanin shine ƙauyen da ake kira da Nodeh kusa da birnin Kandahar. Marubutan Manituddin sun CE anhaife shi a shekarar 1961 a kauyen Nodeh, gundumar Panjwai, yankin Kandahar. Wasu sunce anhaifi Mullah ne a wani waje mai wannan sunan dai amma a yankin Uruzgan. Wasu rahotannin sunce anhaifi Omar ne a kauyen Noori, gundumar Maiwand, yankin Kandahar. Kamar yadda yake a tarihin Omar wanda kungiyar Taliban ta walafa a shafin yanar gizo shekarar 2015, an haife shi a kauyen Cha-i-Himat, na gundumar Khakrez, yankin Kandahar. An kuma baiyana cewa Sansagar shine kauyen da yayi kuruciya.

Kabilar sa itace Pashtun, kuma mahaifan sa talakawa wadanda basu mallaki koda fili ba. Yan kabilar Hotak ne, babban yanki na reshen Ghilzai. Kamar yadda Hamid Karzai ya fada, "Mahaifin Omar shugaban addini ne na kauyen amma ahalin masu matalauta ne wadanda basu da wata dangamtaka da aiyas a Kandahar ko Kabul. Mahaifin Omar Mawlawi Ghulam Nabi Akhud ya rasu lokacin Omar yana karami. A kalaman bakin sa, Omar yace mahaifin sa ya rasu lokacin yana da shekaru 3 a duniya, sai kuma kawun sa ne ya auri mahaifiyar Omar din. Sai ahalin suka tashi suka koma kauye a gundumar Deh Rawod, India kawunsa yake koyar da ilimin addini. An samu rahoton cewar Dehwanawark ne kauyen da suka zauna da kawun nasa.