Jump to content

Mustapha Lawan Nasidi

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Sayyid Mustapha Lawal Nasidi shahararren malamin addinin Musulunci ne kuma ɗan Islamic Movement Of Nigeria, (Harkar Musulunci A Najeriya) sannan kuma shine ke wakiltar mabiya mazhabar Shi'a a garin Potiskum, yana daga cikin manyan almajiri Sheikh Ibrahim Zakzaky jagoran mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya, wanda ke zaune a garin Potiskum, dake jihar Yobe a tarayyar Najeriya a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.[1]

An haifeshi a ranar 25 ga watan Zulkadah na shekarar alif dari uku da tamanin da biyar(1385), Hijiriyya. Wanda ya yi daidai da ranar 29 ga watan Yuni na shekarar alif dari tara da sittin da biyar (1965), Miladiyya.[1]

Karatun Addini

[gyara sashe | gyara masomin]

Malam Mustapha Lawan Nasidi a gidan addini ya taso, ya fara karatun addini ne a gaban mahaifinsa, sannan ya yi karatun littattafa a wurin Malamai kamar haka, Shaikh Yusuf Dambam da Malam Babangida Shaikh Sa'id Potiskum. Ya fita karatu kasar Iran da Lebanon, sannan ya jagoranci 'yan'uwa almajiran Shaikh Zakzaky mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya daga Nijeriya zuwa kasar Iraq, ziyarar Arba'een na Imam Hussain (as), jikan Manzon Allah (SWA) shekaru biyu a jere. Sannan ya je kasar Saudi Arabia aikin Hajji. Sayyid Mustapha Lawan Nasidi shi mahaddacin Alqur'ani ne.[1]

Karatun Zamani

[gyara sashe | gyara masomin]

Malam Mustapha Lawal Nasidi ya yi karatun Firamarensa a Central Primary School Potiskum, sannan ya yi sakandire a Government Science and Technical College, Damagum.[1] Bayan kammala Sakandire sai ya tafi ABU Zariya, inda ya yi IJMB, sannan ya je University of Maiduguri, inda ya karanta Physics, sannan ya tafi ATBU Bauchi inda ya karanta Computer Science.[1]

Mahaifinsa shi ne Alhaji Lawal Nasidi, da ne ga Alhaji Shu’aibu Nasidi, wadda dukkansu Malamai ne, Mabiya Darikar Tijjaniyya. Kakansa asali mutumin Unguwar Koki ne ta cikin birnin Kanon Dabo, daga baya ya dawo garin Potiskum domin harkokin addini da Kasuwanci.[1] Manyan Shehunnai a garin Potiskum sun bada labarin cewa a kofar gidan Alhaji Shu’aibu Nasidi aka assasa Wazifa da Zikirin Jumu’a na Darikar Tijjaniyya a garin Potiskum, kuma an samu tabbaci sosai akan kasancewarsa Sharifi.

Mahaifiyarsa ita ce Hajiya Asma’u Muhammad Wabi, ‘yar asalin garin Jama’are ce ta jihar Bauchi, a can aka haifeta amma a garin Potiskum ta girma a hannun kanin Mahaifinta Alhaji Yusuf Mai Kwano Potiskum. Ita ma iyayenta dukkansu ‘yan Darikar Kadriyya ne, sai da ta haddace Alqur’ani mai tsarki sannan aka yi aurenta. Mahaifiyarsa tana nan a raye, amma Mahaifinsa Alhaji Lawan Nasidi ya rasu tun a shekarar alif dari tara da tamanin da biyar 1985.

Sayyid Mustapha shi ne na 4 a wurin Mahaifinsa, sannan yana da yayu da kanne. Yana da mata 1 da 'ya'ya guda 6, sune Fatima (Zakiyya), Zainab, Muhammad, Ali, Ummu Kulthum da Subaika Durra.

Sayyid Mustapha Lawal Nasidi mutum ne mai basira da saurin ɗaukar karatu, tun yana ƙarami haka yake har zuwa girman sa. Abokan karatun sa tun na yarinta har zuwa na Harka Islamiyya duk sun yi shaidar haka. Bayan rikicin 'yan Shi'a a Zariya ta 12-14 Disambar 2015, mahaifiyar Sayyid Mustapha Lawal Nasidi din, Hajiya Asma'u, ta bayyana cewa, "Malam Mustapha tun tasowarsa yaron kirki ne, ya kasance mai ladabi da biyayya da girmama na gaba dashi, shi mutum ne mai zumunci da son 'yan'uwansa. Lokacin yana karami, idan yana kuka, sai yayansa, Alhaji Isiyaka, sai yace Hajiya ba kuka yake ba, karatu yake. Sai nima na yi ta mamaki idan ya fadi hakan, sai da ya fara girma, dana ga irin kaifin basirar da Allah ya masa, gashi da saukin fahimtar karatu, sai na tabbatar da cewa, lallai Allah ya yi masa baiwa ta daban"

Hajiya tace "Malam Mustapha, mutum ne mai nazari da hangen nesa, duk abin da zai yi sai ya yi tunani a kansa, kuma duk abin da ya shige mana duhu, idan aka fada masa, cikin kankanin lokaci zai warware mana shi. Yana da biyayya da bin umarnin iyaye.

Har yanzu babu wanda yace mana ya ganshi ko ya ce ya mutu saboda yana daga cikin wadanda rikicin Zariya da sojoji ya rutsa dashi.[2]

Sayyid Mustapha Lawal Nasidi mutum ne mai hakuri, zai yi wahala kaga bacin ransa, sai dai in ka taba Manzon Allah (s) saboda shi mutum ne mai kishin addinin Muslunci, Sayyid Mustapha yana da yawan ibada, duk wanda ya yi mu'amala da shi, zai shaidi haka. Fasihi ne shi, Allah ya hore masa fasahar iya magana, kokai waye idan ya yi magana da kai sai ka fahimce shi. Jarumi ne shi, gwarzo, bashi da tsoro ko kadan, sai dai tsoron mahaliccinsa, hatta makiyansa sun yi masa wannan shaida. Sayyid Mustapha shi kadai ne yake fitowa ya yi magana a kan kowace irin matsala da ta damu al'umma a yankin Potiskum.

Rikicin Boko Haram

[gyara sashe | gyara masomin]

Shi ne a lokacin 'yan ta'adda na Boko Haram yake fitowa ya yi wa jama'a gamsashshen jawabi.[3] Lokacin da tashin Bama-Bamai ya yi tsanani a yankin Potiskum, ana ta guduwa ana barin gari, Sayyid Mustapha cewa ya yi "Kar kowa ya tafi ko ina, babu inda babu mutuwa, kuma mutum ba zai mutu ba, sai kwanansa ya kare, don haka ni babu inda zan tafi, ina nan a cikin garin Potiskum, ko da kuwa za ayi gunduwa gunduwa dani.[4] Wannan jawabi na Sayyid Mustapha ya saka jama'a da dama sun zauna, duk da ma wasu sun riga sun gudu. Sayyid Mustapha Lawal Nasidi an kawo masa hari don a kashe shi har sau uku.[5] Na farko shi ne wanda aka kawo masa hari gidansa a shekarar 2012. Suna zaune, bayan sun yi Azumi, ko ruwa basu sha ba, sun idar da Sallar Magrib, a ka bude musu wuta, take almajiransa uku suka mutu, aka jikkata mutum 6.[6] Shi Sayyid Mustapha ko kwarzane bai yi ba, Allah ya kare shi. Sannan sun bi shi Jama'are, a shekarar 2013, garin kakanninsa, da nufin su kama shi, su je su kashe shi, nan ma Allah ya kare shi. Sai kuma na shekarar 2014, wanda aka jefa Bom a cikin masu Muzaharar Ashura juyayin ashura na kisan Imam Hussaini da a kayi a karbala a Potiskum, sun hango dan wani da rawani, sun dauka Sayyid Mustapha ne, sai da Bom din ya tashi, sai suka ga ashe bashi bane.[7] Shi ne suka bude wuta a kan almajiransa da sauran jama'ar gari, inda suka kashe kusan mutum 30. Sun yi ta dana masa tarko Allah yana kare shi.[8]

Sayyid Mustapha mutum ne mai karamci da girmama bako, yana da sada zumunci, yana yawan ziyarar Malamai na cikin garin Potiskum, domin neman hadin kai.[1]