Jump to content

Naja'atu Bala Muhammad

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
(an turo daga Naja'atu bala muhammad)
Naja'atu Bala Muhammad
Rayuwa
Haihuwa 1956 (67/68 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ahmadu Bello
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Naja'atu Bala Muhammad (An haife ta a shekara ta alif dari Tara da hamsin da shida 1956 miladiyya.(A.c) tana daya daga cikin mata a Arewacin Najeriya wacce suke takarawa a siyasan ce. Itace mace ta farko da ta fara zama Sanata, wacce ke wakiltar gundumar Kano ta Tsakiya. Ta kuma kasance daya daga cikin mace ta farko da ta riƙe shugabacin kungiyar dalibai ta kasa daga fitacciyar jami’ar Ahmadu Bello, Zariya (ABU) sannan kuma ita ce mace ta farko da ta zama Mataimakiyar - Shugaban kungiyar Daliban Najeriya ta Kasa (NANS).[1]

Tana ikirararin cewa ita ta kawo Shugaban kasar Najeriya mai ci, Muhammadu Buhari cikin siyasa, da kuma kan karagan mulkin shugabancin kasa.[2]

Kuruciya da ilimi

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Muhammad Naja'atu a shekara ta alif 1956, a cikin garin Kano.ta tsakiya cikin dangin Alhaji Ali Abdullahi, wanda ya kasance mai kishin zamantakewar al'umma kuma daya daga cikin wadanda suka yi zamani da Malam Aminu Kano a kungiyar ' Northern Elements Progressive Union (NEPU)'.[3] Muhammad a halarci makarantar firamare a St. Louis Private School, Kano, sannan ya tafi Sakandiren WTC a Kano. Ta samu digiri na farko a fannin tarihi daga Jami'ar Ahmadu Bello, Zaria.

Naja'atu Muhammed ta kasance tsohuwar matar Dr Bala Muhammed, mai bai wa gwamnan jamhuriyya ta biyu Mallam Abubakar Rimi shawara kan harkokin siyasa. Wasu mutane ne suka kashe mijinta shekaru 28 da suka gabata wanda ya haifar da mummunan rauni bayan da Malam Muhammadu Abubakar Rimi ya zargi mai martaba Sarkin Kano, Ado Bayero.[4]

  1. "Naja'atu Bala Mohammed: First Elected Female SUG President In ABU Zaria | The Abusites" (in Turanci). 2021-04-22. Archived from the original on 2021-05-01. Retrieved 2021-05-17.
  2. "Insecurity: I introduced Buhari to politics ― Hajiya Nàja'atu Mohammed". Vanguard News (in Turanci). 2020-06-21. Retrieved 2020-06-21.
  3. "HAJIYA NAJATU MUHAMMED: THE UNASSAILABLE PROGRESSIVE AMAZON". www.newsgrainmagazine.com. News Grain. Archived from the original on 21 December 2016. Retrieved 8 December 2016.
  4. Ali, Richard. "Denudation: Remembering Dr Bala Mohammed Bauchi". Pambazuka News. Retrieved 23 January 2019.