Jump to content

Oserheimen Osunbor

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Oserheimen Osunbor
mutum
Bayanai
Bangare na Nigerian senators of the 4th National Assembly (en) Fassara da Nigerian senators of the 5th National Assembly (en) Fassara
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Sunan asali Oserheimen Osunbor
Sunan haihuwa Oserheimen Osunbor
Shekarun haihuwa 5 Oktoba 1951
Yaren haihuwa Harshen Esan
Harsuna Turanci, Harshen Esan da Pidgin na Najeriya
Writing language (en) Fassara Turanci
Sana'a ɗan siyasa
Muƙamin da ya riƙe Gwamnan jahar Edo, mamba a majalisar dattijai ta Najeriya da mamba a majalisar dattijai ta Najeriya
Ilimi a Makarantar Koyan Lauya ta Najeriya da Jami'ar Najeriya, Nsukka
Ɗan bangaren siyasa Peoples Democratic Party
Ƙabila Mutanen Esan
Eye color (en) Fassara brown (en) Fassara
Hair color (en) Fassara black hair (en) Fassara
Mabiyi Lucky Igbinedion
Wanda ya biyo bayanshi Adams Aliyu Oshiomhole
Kyauta ta samu Tallafin karatu na Rhodes
Personal pronoun (en) Fassara L485

Oserheimen Osunbor, (an haife shi ranar 5 ga watan Oktoban shekarar 1951), lauyan Najeriya ne kuma ɗan siyasa wanda ya kasance Sanatan Tarayyar Najeriya daga ranar 29 ga watan Mayun shekarata 1999 zuwa ranar 29 ga watan Mayun 2007 kuma gwamnan jihar Edo na Najeriya daga ranar 29 ga watan Ma Mayun 2007 zuwa ranar 11 ga watan Nuwamban 2008.[1]

Rayuwar farko da aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Oserheimen Osunbor a ranar 5 ga watan Oktoban shekarar 1951 a Iruekpen, ƙaramar hukumar Esan ta Yamma, jihar Edo, Najeriya. Ya halarci makarantar firamare ta PTTC Igueben daga shekarar 1957 zuwa 1962, sannan ya halarci makarantar Anglican Grammar School Ujoelen Ekpoma daga shekarar 1963 zuwa 1968 sannan ya samu fom na shida a Holy Trinity Grammar School Sabongidaa-Ora Edo State. [ana buƙatar hujja]

Ofishin Sanata

[gyara sashe | gyara masomin]
Oserheimen Osunbor a cikin mutane

An zaɓi Farfesa Oserheimen Osunbor a matsayin Sanata mai wakiltar Edo ta tsakiya a jihar Edo a Najeriya a farkon jamhuriya ta huɗu a jam'iyyar People's Democratic Party (PDP). Ya fara aiki a ranar 29 ga watan Mayun 1999.[2] Bayan ya hau kujerar majalisar dattawa a cikin watan Yunin shekarar 1999 aka naɗa shi a kwamitocin kan dokoki da ƙa'idoji, da'a, shari'a, albarkatun ruwa da harkokin gwamnati (Chairman).[3] An sake zaɓen Osunbor a kujerar Sanata a cikin watan Afrilun shekarata 2003.[4] Ya kuma riƙe muƙamai daban-daban na shugaban ƙasa yayin da yake Majalisar Dattawa da suka haɗa da: Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC); Shugaban Kwamitin Majalisar Dattijai kan Shari’a, Ƴancin Ɗan Adam da Al’amuran Shari’a; Shugaban kwamitin majalisar dattawa da dama da kwamitocin haɗin gwiwa na majalisar dokokin ƙasa; Shugaban, Ƙaramin Kwamitin Majalissar dokoki da Lissafin Majalisu, Kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Dokoki ta Ƙasa kan Gyaran Kundin Tsarin Mulki. Tasirinsa ya yi zurfi sosai har abokan aikinsa suka yi masa laƙabi da "Attorney-General of the Senate".[ana buƙatar hujja]

An zaɓi Osunbor a matsayin gwamnan jihar Edo a Najeriya a cikin watan Afrilun shekarar 2007 a ƙarƙashin jam'iyyar PDP.[5] A ranar 20 ga watan Maris ɗin 2008, Kotun Zaɓen Gwamnan Jihar Edo ta bayyana cewa zaɓen Osunbor bai yi nasara ba, kuma ta nemi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) da ta janye satifiket ɗinsa ta bayyana Adams Aliyu Oshiomhole na jam’iyyar Action Congress (AC) a matsayin wanda ya lashe zaɓen.[6] A ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 2008, wata kotun ɗaukaka ƙara ta tarayya da ke zama a birnin Benin, ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓe a jihar, inda ta bayyana Oshiomole a matsayin gwamnan jihar Edo. An yanke shawarar ne bisa wasu kura-kurai da aka samu a zaɓen.[7]

Rayuwa ta sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Oserheimen Osunbor ya yi aure cikin farin ciki tare da ƴaƴa shida. Shi Kirista ne na ɗarikar Anglican kuma Knight na Saint Christopher[ana buƙatar hujja]

  • Jerin Gwamnonin Jihar Edo