Sa'adiya Umar Bello

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sa'adiya Umar Bello
Rayuwa
Haihuwa jihar Kano
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Bayero
Harsuna Turanci
Hausa
Sana'a
Sana'a docent (en) Fassara da Malami

Sa'adiya Omar Bello (OON) masaniyar kimiyya ce ta ƙasar Najeriya kuma farfesa a fannin adabin Hausa a Jami'ar Usmanu Danfodiyo. Tana da digirin digirgir Ph.D daga wannan jami'a. Tsakanin shekarun 2000 da 2005, ta kasance Darakta a Cibiyar Nazarin Hausa (2000-2005) & (2013-2017) [1] Ita mamba ce ta Muslim Media Watch Group of Nigeria board of trustees tun daga shekarar 2018.[2] A shekara ta 2022, an ba ta lambar yabo ta ƙasa a cikin Order of the Niger.[3]

Jagoranci[gyara sashe | gyara masomin]

Ta taɓa zama shugabar mata ta ƙasa (FOMWAN) kungiyar mata musulmi a faɗin Najeriya. FOMWAN kungiya ce da ta shahara a Najeriya.

Girmamawa[gyara sashe | gyara masomin]

A shekarar 2018 an karrama Farfesa Sadiya Omar Bello a matsayin memba na Amintattu na kungiyar (BoT.A Muslim media group). taron wanda ya gudana a Osogbo babban birnin jihar Osun kuma ya samu halartar mai alfarma Sarkin Musulmi wanda shi ne shugaban majalisar koli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya (NSCIA), da kuma jamb rejista Pro. Ishaq Oloyede kuma ya kasance wata shahararriyar kungiya wacce ke da kwararrun masana shari'a da dama.[4]

An karrama Farfesa Sa’adiyah Omar the Formal Amirah general na FOMWAN da lambar yabo ta Nana Asmau akan ci gaban al’umma. Kyautar da Sarkin Musulmi ya bayar ita ce ziyarar Iseyin a jihar Oyo.[5]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Directory of Full Professors in the Nigerian University System, 2017 page
  2. "Sultan inaugurates Muslim Media Watch Group's BoT tomorrow". Blueprint Newspapers Limited (in Turanci). Abuja, Nigeria. 2018-03-16. Retrieved 2023-03-11.
  3. Rakiya A. Muhammad (26 Apr 2014). "I demanded to be taken to school at age 6" (in Turanci). Daily Trust. Archived from the original on Jul 16, 2023. Retrieved 23 July 2023 – via PressReader.
  4. II, Administrator (2018-03-16). "Sultan inaugurates Muslim Media Watch Group's BoT tomorrow - Blueprint Newspapers" (in Turanci). Retrieved 2023-07-16.
  5. "FOMWAN salutes Sultan". Tribune Online (in Turanci). 2021-11-19. Retrieved 2023-07-16.