Sinima a Sudan ta Kudu
Sinima a Sudan ta Kudu | ||||
---|---|---|---|---|
cinema by country or region (en) | ||||
Bayanai | ||||
Facet of (en) | cinema (en) | |||
Ƙasa | Sudan ta Kudu | |||
Wuri | ||||
|
Cinema sabuwar masana'anta ce mai tasowa a Sudan ta Kudu.
Bayani
[gyara sashe | gyara masomin]Ya zuwa shekarar 2011, babu koda ɗakin kallon Finafinai ɗaya a ƙasar Sudan ta Kudu. AsAs of 2011[update], sannan dukkan ƴan ƙasar sun dogara ne da Gidan talabijin na Sudan ta Kudu wanda ake kira da SSTV. A ta bakin manajan Sudan ta Kudu Elfatih Majok Atem, "Mafi yawan ƴan ƙasar masu shirya Finafinai basu da ƙwarewar harkokin Finafinai. Masu ƙwarewa kuma basu da kayan aiki ingantattu.."[1]
Bayan Fage
[gyara sashe | gyara masomin]Sudan ta Kudu ta samu 'yancin kai a shekarar 2011; daidai shekaru shida bayan kammala Yaƙin Basasar Sudan na Biyu wanda ya haifar da rugujewar gidan sinima na Capital Juba kawai. A cikin shekarar 2011, Daniel Danis ya ba da umarnin fim ɗin farko na Sudan ta Kudu, Jamila .
Bikin fim
[gyara sashe | gyara masomin]A shekarar 2016, Sudan ta Kudu ta shirya bikin fim na farko, bikin fina-finai na Juba . Bikin ya kunshi taron masana’antar shirya fina -finai, kuma na biyu da aka shirya za a yi a Sudan ta Kudu. [2] Simon Bingo ne ya assasa wannan biki, an yi shi ne don rage mummunan hoton Sudan ta Kudu a matsayin ƙasa mai fama da yaƙe-yaƙe tare da haɓaka al'adun Sudan ta Kudu da fasaha.
Ƙungiyoyi
[gyara sashe | gyara masomin]Ƙungiyoyi da yawa a cikin ƙasar suna neman haɓaka harkar fim ta masu yin fim na cikin gida:
- Woyee Film da Theatre Industry, ƙungiyar shirya fina -finai.
- Sashin Sinima da Masana'antar Fim na Ma'aikatar Al'adu, Matasa da Wasanni . [1]
- Kwalejin Fim da TV, makaranta ce mai zaman kanta a Juba. [1]
- Cibiyar Al'adu ta Nyakuron, mai masaukin baki don bikin Fim ɗin Juba na 2016.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]
Sinima a Afrika |
Sinima a Afrika | Afrika ta Kudu | Afrika ta Tsakiya | Aljeriya | Angola | Benin | Botswana | Burkina Faso | Burundi | Cabo Verde | Cadi | Côte d'Ivoire | Eritrea | eSwatini | Ethiopia | Gabon | Gambiya | Ghana | Gine | Gine Bisau | Ginen Ekweita | Jibuti | Kameru | Kenya | Komoros | Kwango (JK)|Kwango (JK) | Kwango (JDK) | Laberiya | Lesotho | Libya | Madagaskar | Mali | Mauritius | Muritaniya | Misra | Moroko | Mozambik | Namibiya | Nijar | Nijeriya | Ruwanda | Saliyo | Sao Tome da Prinsipe | Senegal | Seychelles | Somaliya | Sudan | Sudan ta Kudu | Tanzaniya | Togo | Tunisiya | Uganda | Zambiya | Zimbabwe |