Sule Lamido

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Sule Lamido
gwamnan jihar jigawa

29 Mayu 2007 - 29 Mayu 2015
Ibrahim Saminu Turaki - Badaru Abubakar
Ministan harkan kasan waje

1999 - 2003
Ignatius Olisemeka (en) Fassara - Oluyemi Adeniji
Rayuwa
Haihuwa Birnin Kudu, 30 ga Augusta, 1948 (75 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Karatu
Makaranta Government College, Birnin Kudu
Kwalejin Barewa
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da Mai wanzar da zaman lafiya
Imani
Jam'iyar siyasa Peoples Democratic Party
Sautin Muryar Alhaji Sule Lamido

Sule Lamido (An haife shi a ranar 30 ga watan Augustan shekarar 1948) ya taɓa zama ministan harkokin wajen Nijeriya daga shekarar 1999 zuwa shekara ta 2003[1]. Daga bisani ya nemi takara kuma aka zaɓe shi Gwamnan Jihar Jigawa a watan Afurilun shekarar 2007. Dan Jam'iyar People's Democratic Party (PDP) ne, kuma ya nemi zaɓe a takara ta biyu a shekarar 2011. A shekarar 2015 an gurfanar da shi da ‘ya’yansa maza bisa zargin satar kuɗaɗen gwamnati da EFCC ta yi.[2][3][4][5][6]

Iyali[gyara sashe | gyara masomin]

Matarsa Amina Sule Lamiɗo an haife ta a shekarar 1973 a Hausari Quarters Maiduguri. Ta kasance ma’abociyar addini ce wadda hakan yasa bata ɓoye daga idon duniya ba. Ta yi makarantar Irshad Primary Islamiyya (1980-1986) sannan post primary Academic a Junior Arabic Secondry School Sumaila (1988-1991).[7]

Siyasa[gyara sashe | gyara masomin]

Sule Lamido ya riƙe muƙamin ministan waje tsakanin 1999-2003. An zabeshi a matsayin gwamnan Jihar Jigawa a shekara ta 2007 an kuma sake zabarsa a shekarar 2011 zuwa 2015. sule lamido yayi shekara takwas yana mulkin gwamna a jahar jigawa, karkashin jam’iyar PDP kuma ya nemi takaran shugaban kasa a shekara ta 2019.

Bibilyo[gyara sashe | gyara masomin]

  •  Kabir, Hajara Muhammad. Northern women development. [Nigeria]. ISBN 978-978-906-469-4. OCLC 890820657.

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://m.facebook.com/sule.lamido
  2. "How EFCC arrested Lamido, 2 sons". Vanguard News (in Turanci). 2015-07-08. Retrieved 2020-04-01.
  3. "Court grants bail to Lamido, sons". TheCable (in Turanci). 2015-07-14. Retrieved 2020-04-01.
  4. "EFCC re-arraigns Sule Lamido, sons over alleged N1.35bn fraud". News Express Nigeria Website (in Turanci). Retrieved 2020-04-01.
  5. "Corruption: The Story Of Fathers, Sons On Trial". Sahara Reporters. 2017-02-26. Retrieved 2020-04-01.
  6. "EFCC re-arraigns Sule Lamido, sons over alleged N1.35bn fraud - Premium Times Nigeria" (in Turanci). 2018-10-24. Retrieved 2020-04-01.
  7. Kabir, Hajara Muhammad. Northern women development. [Nigeria]. P. 172 ISBN 978-978-906-469-4.