Jump to content

Tattaunawar user:Abubakar Yusuf Gusau

Page contents not supported in other languages.
Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.

Barka da zuwa![gyara masomin]

Ni Robot ne ba mutum ba.

Hausa Wikipedia na buƙatar gudummuwarku domin ta bunƙasa!

Barka da zuwa Hausa Wikipedia, Abubakar Yusuf Gusau! Mun ji daɗin gudummuwarku. Kuma muna fatan zaku tsaya ku ci gaba da bada gudummuwa. Anan ƙasa ga wasu shafuka da zasu taimaka wajen fahimtar Hausa Wikipedia da yadda ake gyara ta:

Zaku iya yin sayinin rubutunku idan kuna akan shafukan tattaunawa ta hanyar alamar tilde guda huɗu, kamar haka (~~~~); yin hakan, zaisa sunanku da cikkaken kwanan wata. In kana buƙatar wani taimako, ku duba Wikipedia:Tutorial. Na gode. AmmarBot (talk) 13:34, 9 Satumba 2021 (UTC)[Mai da]

Goge Makala[gyara masomin]

Barka dai Abubakar Yusuf Gusau, sannu da kokari. Za kaga na goge dukkan maƙalolin da ka kirkira, hakan ya faru ne sakamakon wasu da turanci kayi su wanda hakan ya saɓa ma Dokokin Hausa Wikipedia. Wasu kuma akwai su dama. Duba Yadda ake rubuta muƙala domin samun ƙarin ƙwarewa. Idan kana da wata bukata to kana iya tuntube Ni ta Shafina na tattaunawa

-Gwanki (talk) 07:01, 14 Satumba 2021 (UTC)[Mai da]

Goge Shafin Taraba State[gyara masomin]

Barka da war haka, Abubakar Yusuf Gusau ina mai sanar da kai cewa mun goge shafin Taraba State saboda akwai shafin a Hausa Wikipedia Jahar Taraba saboda haka muka goge. Da fari idan kana so ka kirkiri sabon shafi ka fara duba ta 'search box' ko idan akwai shafin. Uncle Bash007 (talk) 13:00, 15 Satumba 2022 (UTC)[Mai da]

Saka manazarta a mukalar "Yankin Sahara na Afrika"[gyara masomin]

Assalamu Alaika @Abubakar Yusuf Gusau, naga kai ne ka kirkira mukalar Yankin Sahara na Afrika amma baka saka mata manazarta ba. yakamata mu rika inganta ayyukanmu da abin dogaro saboda yanada matikar mahimmanci. Nagode Saifullahi AS (talk) 11:27, 1 ga Yuli, 2023 (UTC)[Mai da]

Manazarta[gyara masomin]

Aslm, @Abubakar Yusuf Gusau brk da aiki. Ina so na sanar da kai akan maƙalar da kake fassarawa wannan abu ne mai kyau. Sai dai yadda kake saka Manazarta/Reference kwara guda a ko'ina madadin maƙalar gaba-daya wanda hakan kuskure ne. Bugu da kari ma manazarta da kake sakawa ba komai bane illa link kwara ɗaya, wanda zai kai mutum ainafin shafin da aka kirkiro ko fassara maƙalar, misali wannan makalar da ka fassara. Ina fatan idan kana da tambaya akan yanda ake saka manazarta ka tambaya. Fatan za'a gyara domin kaucewa gogewa. Nagode. BnHamid (talk) 08:01, 27 Oktoba 2023 (UTC)[Mai da]

Slm. Naji kuma zan gyara Insha Allah, saboda haka inaso ayi unblocking dina saboda akwai aikin dana nakeso na qara sa. Abubakar Yusuf Gusau (talk) 16:57, 29 Disamba 2023 (UTC)[Mai da]

Gajerar makala[gyara masomin]

Barka da yau, @Abubakar Yusuf Gusau, naga kana fara fassara maƙala sai ka saki ka kama fassara wata kuma, ya kamata mu riƙa amfani da abin da ake fada mana akai. Kana fara fassara maƙala section ɗaya sai ka barta kuma ka nufi wata!. Ya kamata kafin fassara wata ka tabbatar ka idasa wadda ka rigaya fara fassara akai ko da kashi 80 ne na maƙalar ka cimmawa kafin ka nufi wata kuma. Nagode da fatan zamu kiyaye.

Muma ba yin mu bane dokoki ne na gidauniyar Wikipidia baki-ɗaya kuma tunda har mun amince zamuyi to wajibi ne mu bi dokokin da tsare-tsaren tafiyar nan. BnHamid (talk) 21:19, 19 ga Janairu, 2024 (UTC)[Mai da]