Umar Gombe

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Umar Gombe
Rayuwa
Cikakken suna Umar Sani Labaran
Haihuwa 13 ga Afirilu, 1983 (40 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a Jarumi
IMDb nm13173654

Umar Sani Labaran, Wanda aka fi sani da Umar Gombe (An haife shi a ranar 5 ga watan Afrilu, shekarata 1983) a Gombe, Jihar Gombe, a Najeriya. ɗan wasan kwaikwayo ne na Najeriya, mai shirya fina-finai, kuma darakta.[1] Wanda ya fito a fina-finai sama da ɗari. Umar Gombe ya kasance manajan shirye-shirye na farko da ake watsawa a tashar Northflix.[2] Baya ga fitowa a fina-finai, yana kuma fitowa a shirye-shiryen talabijin, rediyo, da kuma wasannin barkwanci. Sau da yawa an zaɓe shi a matsayin gwarzon ɗan wasan kwaikwayo, kuma ya lashe wasu kyaututtuka da dama.

Rayuwar farko da ilimi[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Umar Gombe ga iyalan Kano ranar 5 ga watan Afrilu, shekara ta 1983 a Gombe, Najeriya. Dan Malam Sani Labaran ne, manomi, dattijo kuma mamba a kungiyar tuntuɓa ta Arewa.

Daga shekara ta 1986 zuwa 1998, yayi karatu a makarantun gandun daji, firamare, da sakandare a jihar Gombe, da jihar Bauchi. Ya ci gaba da karatunsa a Jami’ar Bayero Kano, inda ya samu shaidar difloma a fannin harkokin gwamnati da sarrafa bayanai da fasahar sadarwa (diplomas in Public Administration and Data Processing & Information Technology).[3] Umar yana da digiri na farko a fannin fasahar sadarwa da tsarin bayanan kasuwanci daga Jami'ar Middlesex Dubai, kuma a halin yanzu yana karatun MBA a Jami'ar (National open University) ta Najeriya.[4]

A shekara ta 2014, Umar Gombe ya halarci wani shirin horar da fina-finai a Cibiyar Nazarin Fina-Finai da Talabijin ta Asiya, Noida a Indiya, shirin da Majalisar Dinkin Duniya ta aiwatar[5], tare da sauran jaruman Kannywood da suka halarci ci taron kamar su Falalu A Dorayi, Ali Nuhu, Ishaq Sidi Ishaq da kuma Ibrahim. Mandawari.

Muƙami da Aikin fim[gyara sashe | gyara masomin]

An naɗa Umar Sani Labaran a matsayin shugaban riko na kungiyar masu yin Hotunan Hot ta Najeriya a shekara ta 2021,[6] sannan ya zama mataimakin sakataren kungiyar na kasa bayan zaɓen da akayi a shekera ta 2022.

Umar ya fara fitowa a fina-finan Hausa a shekara ta 2001 a wani fim mai suna Shaida, wanda ya taimaka masa ya yi suna da kuma samun karbuwa a wajen jama’a da dama a masana’antar, daga karshe ya zama jigo a fina-finan Fasaha kafin ya koma ISI Films, wanda fitaccen jarumin fina-finai Ishaq Sidi Ishaq ya assasa, daga baya kuma kamfanin Kumbo Productions, ya shirya fim din Sanafahna, wanda ya yi fice a harkar fim. an ɗauki shirin fim ɗin a kasar Najeriya da Nijar. Ya fito a cikin fina-finan kamfanin Kumbo Productions da dama, da suka haɗa da Armala, Noor, da Sanafahna.[7]

A shekara ta 2014, ya fara fitowa a shirin wasan kwaikwayo na talabijin kuma mai dogon Zango Dadin Kowa[8] mallakin Arewa24, wanda ya samu lambar yabo. [14] A shekarar 2022, ya yi fice a karon farko a shirin mai dogon Zango na Gidan Badamasi [9] da ya samu lambar yabo, wani fim da ya shafi mata da maza don magance matsalolin zamantakewa wanda Faika Ibrahim Rahi ta bada umarni a fim ɗin, ta samu lambar yabo.[10]

Shahara[gyara sashe | gyara masomin]

Umar Gombe ya yi fice ne bayan fitowa a fim din Nollywood na Turanci na Netflix, Tenant of the House,[11][12] wanda Kunle Afolayan da Adieu Salut suka shirya, da sauran fina-finan Hausa kamar Kwalla, Lambar Girma, Noor, Lissafi, Iko, da kuma In Zaki So Ni. Kuma ya taka rawar gani a fina-finai kamar Lissafi, Noor, Mati A Zazzau,[13] Kishiyata, Fati, Wakili, Hauwa Kulu, da ma jerin shirye-shiryen masu dogon Zango.

Umar ya tabbatar da kansa a matsayin ɗaya daga cikin jaruman Kannywood masu hazaka. Ya kuma taka rawar gani a cikin shirin Daɗin Kowa da ya samu lambar yabo,[14] wanda shi ne shirin fim mai dogon Zango na harshen Hausa na farko da aka fara nunawa a tashar Arewa24.[15] Umar kuma ya fito a cikin shirin mujallar iyali na Najeriya, Ongacious Zango na 2.

Fina-finai[gyara sashe | gyara masomin]

Key
Denotes films that have not yet been released Denotes films that have not yet been released
Year Title Role Genre Note
2001 Shaida Actor Drama
2001 Haske Actor Drama
2002 Duhun Damunai Actor Drama
2002 Kwalla Actor Drama
2003 Sansani Actor Drama
2004 Ambaliya Actor Drama
2004 Tutar So Actor Drama
2005 Jarida Actor Drama
2006 Takbir Actor Drama
2006 Lada Actor Drama
2007 Attajira Actor Drama
2007 Nauyi Actor Drama
2008 Iko Actor Drama
2008 Budurwa Actor Drama
2008 Jari Hujja Actor/Writer Drama
2009 Wasila Actor Drama
2009 Wasila (English) Actor Drama
2009 Lissafi Actor Drama
2009 Kusuwar Danga Actor Drama
2010 Wa'azi Actor Drama
2010 Bakar Ashana Actor/Writer Thriller
2010 Fati Actor Drama
2010 Sanafahna 2 Actor Drama
2010 Ruwan Dare Actor Drama
2010 Sauyin Lamari Actor Drama
2011 Balele Actor Drama
2011 In Zaki Soni Actor Drama
2011 Noor Actor/Producer Drama
2014 Aci Bulus Actor Drama
2014 Armala[16] Actor/Producer Drama
2014 Makuwa Actor Drama
2015 Soyayaya Da Tsakuwa Actor Drama
2017 Samari Actor Drama
2018 Ni Da Kai Da Shi Actor Drama
2019 Tenant Of The House Actor Drama
2019 Gargadi[17] Actor/Producer Drama Short film
2020 Mati A Zazzau[18] Actor Comedy/Drama
2021 Hauwa Kulu Actor Drama
2021 Wakili Actor Comedy/Drama
2021 Ameer Denotes films that have not yet been released Actor Action/Drama Short film
2022 Tsayin Daka Actor Drama
2022 Maimunatu Actor Drama
2022 Adieu Salut Denotes films that have not yet been released Actor SciFi

Telebijin[gyara sashe | gyara masomin]

Year Title Role Genre Notes
2014 Dadin Kowa Actor Drama Series regular (13 episodes)[19]
2018 Yan Birni (Makewayi) Actor Drama A film powered by UNICEF
2019 Yan Zamani Actor Comedy/Drama
2021 Gidan Danger Actor Drama Series regular (13 episodes)[20]
2021 Bugun Zuciya Actor Drama
2021 Yan Tagwaye Denotes films that have not yet been released Producer Drama
2022 Gidan Badamasi Actor Comedy/Drama Series regular (13 episodes)[21]
2022 Kishiyata Actor Drama
2022 Sawun Giwa Actor Drama
2022 Nasaba Denotes films that have not yet been released Actor/Producer Drama

Murya[gyara sashe | gyara masomin]

Year Title Role Genre Notes
2010 Ruwan Dare Actor Drama Ɗora muryar Jarumi
2021 Madubi Actor Drama Ɗora muryar Jarumi

Hanyoyin haɗin waje[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Chidiebere Ihemebiri (2021-05-25). "I Found It Difficult Graduating From An Actor To A Producer – Umar Gombe". Daily Trust. Retrieved 2022-09-11.
  2. Ibrahim Musa Giginyu (2022-04-19). "Kannywood Actor, Umar Gombe, Turns Pioneer Program Manager Of Northflix". Daily Trust. Retrieved 2022-09-11.
  3. HausaFilms.TV (2018-07-12). "Umar Gombe HausaFilms.TV - Kannywood, Fina-finai, Hausa Movies, TV and Celebrities". HausaFilms.TV. Retrieved 2022-09-11.
  4. Daily Trust (2021-05-21). "I would have become a model if I was not an actor - Umar Gombe - YouTube". Daily Trust. Retrieved 2022-09-11.
  5. IFCPC (2018-05-12). "Indo Nigerian Film Association Moves Further Under ICMEI". IFCPC. Archived from the original on 2022-09-23. Retrieved 2022-09-23.
  6. Ahmed Lawal (2022-02-24). "Sarari appointed LOC chairman Zuma film festival". Bluprint. Retrieved 2022-09-11.
  7. HausaFilms.TV. "Umar Gombe HausaFilms.TV - Kannywood, Fina-finai, Hausa Movies, TV and Celebrities". HausaFilms.TV. Retrieved 2022-09-11.
  8. Arewa24. "Dadin Kowa - AREWA24". Arewa24. Retrieved 2022-09-16.
  9. Arewa24. "Gidan Badamasi - AREWA24". Arewa24. Retrieved 2022-09-16.
  10. Daily Trust. "Tambari by Daily Trust Tambari - Issuu". Daily Trust. Retrieved 2022-09-23.
  11. Netflix. "Watch Tenant of the House - Netflix". Netflix. Retrieved 2022-09-11.[permanent dead link]
  12. IMDb. "Tenant of the House (2019) - Full Cast & Crew - IMDb". IMDb. Retrieved 2022-09-11.
  13. IMDb. "Mati a Zazzau (2020) - IMBd". IMDb. Retrieved 2022-09-17.
  14. BBC News Hausa (2021-10-21). "Daga Bakin Mai Ita Tare Da Umar Gombe - YouTube". BBC News Hausa. Retrieved 2022-09-11.
  15. Arewa24 (2015-02-06). "DADIN KOWA EPS 3 PRT 1 - YouTube". Arewa24. Retrieved 2022-09-11.
  16. Flickr. "IMG_0709 - Producer/Actor Umar Gombe on set of Armala. - talatu-carmen - Flickr". talatu-carmen. Retrieved 2022-09-17.
  17. Mudari TV 24. "Gargadi - Warning! BY UMAR GOMBE - YouTube". Mudari TV 24. Retrieved 2022-09-17.
  18. IMDb. "Mati a Zazzau (2020) - IMBd". IMDb. Retrieved 2022-09-17.
  19. Arewa24. "Dadin Kowa - AREWA24". Arewa24. Retrieved 2022-09-16.
  20. Arewa24. "Gidan Danger Series - AREWA24". Arewa24. Retrieved 2022-09-16.
  21. Arewa24. "Gidan Badamasi - AREWA24". Arewa24. Retrieved 2022-09-16.