Umar Usman Kadafur

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Umar Usman Kadafur
Mataimakin gwamnan jahar Borno

2019 -
Usman Mamman Durkwa
Rayuwa
Haihuwa Biu, 31 Mayu 1976 (47 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Maiduguri
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Hausa
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Umar Usman Kadafur (an haife shi a ranar 31 ga Mayu, 1976 a Biu, Nigeria ) ɗan siyasan Najeriya ne. Shi ne mataimakin gwamnan jihar Borno na 8 a dimokuradiyya .

Karatu[gyara sashe | gyara masomin]

Umar Usman Kadafur ya yi karatunsa na farko a makarantar firamare ta Mbulamel, Biu. Daga nan sai ya wuce Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati Monguno don samun shaidar kammala karatunsa na sakandare. Da yawa daga baya, ya ci gaba da karatunsa a Jami'ar Maiduguri, ya karanci harkar aikin gwamnati. [1]

Mukaddashin Gwamna[gyara sashe | gyara masomin]

A kwanakin baya ne gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Zulum ya rubutawa majalisar dokokin jihar Borno takardar neman amincewar ya nada Umar Kadafur a matsayin mukaddashin gwamna daga ranar 29 ga Afrilu zuwa 19 ga Mayu, 2021. Gwamnan ya nemi amincewar majalisar dokokin jihar, domin baiwa Umar Kadafur a matsayin mukaddashin gwamna na tsawon kwanaki 21. A wata wasika mai kwanan wata 26 ga Afrilu, 2021, kuma yan majalisun jahar sun karɓi bukatar gwamnan.[2]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-09-12. Retrieved 2022-09-12.
  2. https://peoplepill.com/people/umar-usman-kadafur