Uzoamaka Aniunoh
Uzoamaka Aniunoh | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Onitsha, |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Harshen Ibo |
Karatu | |
Makaranta |
Jami'ar Najeriya, Nsukka University of Birmingham (en) |
Matakin karatu |
Digiri master's degree (en) |
Harsuna |
Turanci Harshen Ibo Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi da darakta |
Imani | |
Addini | Kiristanci |
IMDb | nm10623301 |
Uzoamaka Doris Aniunoh marubuciya ce kuma yar wasan kwaikwayo a Nijeriya.[1] Ta kasance daya daga cikin 'yan wasan kwaikwayo a shiri na MTV Shuga[2] da ke fitowa a cikin jerin da dama ciki har da na farko da na shida.[3][4]
Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Aniunoh a Onitsha.[5] Ta yi karatu a Jami'ar Nijeriya kuma ta sami mabiya a shafin yanar gizon da ta kirkira. A shekarar 2015 ta koma Burtaniya inda ta karanci rubuce-rubuce a Jami’ar Birmingham inda ta samu digirinta na biyu.[6]
'Yar wasan kwaikwayo
[gyara sashe | gyara masomin]Aniunoh ta dawo gida Nijeriya ne a shekara ta 2017 kuma ta halarci gasan gwaji na wani sabon shiri mai suna MTV Shuga.[7] Ta kasance ɗayan daga cikin 'yan wasa kadan da aka zaba yayinda aka bata matsayin Cynthia. Ta bi shawarar Niyi Akinmolayan a shirye-shiryen gwajin kuma wannan shawarar ta ba ta matsayi a cikin Rumor Has It for NdaniTV. Ta kasance jagora a fim din "Stuck" tare da Seun Ajayi da Lala Akindoju .[8]
Shirin MTV Shuga kashi na shida sun sake dawowa Najeriya kuma an sake ba Aniunoh kwangilar sake taka rawar Cynthia a cikin wadannan shekarun wanda aka yiwa lakabi da "Zabi" Sauran ‘yan fim din sun haɗa da Timini Egbuson, Rahama Sadau, Yakubu Mohammed, Bukola Oladipupo, Helena Nelson da Ruby Akabueze.
Aniunoh yana cikin jerin 6 na MTV Shuga kuma rawar da "Cynthia" take ciki lokacin da ta shiga wani karamin shiri mai taken MTV Shuga Alone Tare yana mai bayyana matsalolin Coronavirus a ranar 20 ga Afrilu 2020. Tunde Aladese ne ya rubuta jerin kuma ake watsawa a kowane dare - wadanda ke mara mata baya sun hada da Majalisar Dinkin Duniya.[9] An tsara jerin ne a Najeriya, Afirka ta Kudu, Kenya da Côte d'Ivoire kuma labarin zai ci gaba ta hanyar amfani da tattaunawa ta kan layi akan wurin tsakanin jaruman. Duk fim din ‘yan fim ne za su yi wadanda suka hada da Lerato Walaza, Mamarumo Marokane, Jemima Osunde, Folu Storms da Aniunoh.
Marubuciya
[gyara sashe | gyara masomin]Har wayau, Aniunoh marubuciya ce kuma tana da littafi wanda ta wallafa. Wata marubuciyar Najeriya wato Chimamanda Ngozi Adichie ta ta yanki wani shashi daga littafinta na Balcony ta gyara kuma ta sake wallafa shi.[10]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ Tv, Bn (2021-03-01). "Meet the Star Studded Cast of Kayode Kasum's Comedy Film "Ponzi" + Watch the Trailer". BellaNaija. Retrieved 2021-11-11.
- ↑ "17 Nigerian Actresses You Should Watch Out For in 2021". Nigerian Entertainment Today. 2021-01-08. Retrieved 2021-11-11.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-10-28. Retrieved 2020-11-21.
- ↑ https://www.bellanaija.com/2021/03/kayode-kasum-ponzi/
- ↑ https://thenet.ng/17-nigerian-actresses-you-should-watch-out-for-in-2021/
- ↑ https://bhmng.com/mtv-shuga-and-viacomcbs-africa-respond-to-covid-19-with-alone-together-online-series/
- ↑ "Every Woman Every Child partners with the MTV Staying Alive Foundation to Tackle COVID-19". Every Woman Every Child. 2020-04-16. Retrieved 2021-11-11.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-10-09. Retrieved 2021-11-05.
- ↑ "Every Woman Every Child partners with the MTV Staying Alive Foundation to Tackle COVID-19". Every Woman Every Child (in Turanci). 2020-04-16. Archived from the original on 2021-10-09. Retrieved 2020-04-30.
- ↑ "UZOAMAKA ANIUNOH CHATS WITH GLANCE NG". Glance Online. 2018-05-30. Retrieved 2020-05-13.