Jump to content

Abdul Samad Rabiu

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Abdul Samad Rabiu
Rayuwa
Haihuwa jahar Kano, 4 ga Augusta, 1960 (64 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Karatu
Makaranta Capital University (en) Fassara
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan kasuwa

Abdul Samad Isyaku Rabiu CFR CON[1] (an haife shi a ranar 4 ga watan Agusta na shekara ta alif dari tara sittin 1960 a Kano, Nijeriya) dan kasuwa ne dan Nijeriya kuma mai taimakon al'umma.[2] Mahaifinsa shine marigayi Khalifah Sheikh Isyaka Rabi'u, yana daya daga cikin fitattun 'yan kasuwa a Najeriya a shekara ta alif dari tara da saba'in 1970 da 1980. Abdul Samad shi ne wanda ya kafa kuma yake shugabantar kamfanin BUA Group, wani kamfani na hadin gwiwa a Najeriya wanda ke mai da hankali kan masana'antu, kayayyakin more rayuwa da noma da samar da kudaden shiga da ya kai sama da dala biliyan 2.5, Kuma shi ne shugaban bankin masana’antu na Najeriya (BOI).[3][4][5] A watan Janairun 2023, Abdul Samad Rabiu ya zama attajiri na 4 a Afirka.[1].

  1. "FULL LIST: Okonjo-Iweala, Abba Kyari... FG nominates 437 persons for national honours". TheCable. 2 October 2022. Retrieved 13 October 2022.
  2. "Dangote gains $500 million, Adenuga loses $100 million today!". Encomium Magazine. Retrieved 19 March 2019.
  3. "Dangote gains $500 million, Adenuga loses $100 million today!". Encomium Magazine. Retrieved 19 March 2019.
  4. "Dangote, Adenuga, Alakija rank among richest Blacks". Punch Newspapers. Retrieved 19 March2019.
  5. "Vp Osinbajo's Unquenchable Love For Bua Boss, Abdulsamad Rabiu". THISDAYLIVE. 18 November 2018. Retrieved 19 March 2019.