Abubakar Adamu Rasheed
Abubakar Adamu Rasheed | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | jihar Kano, 22 ga Janairu, 1959 (65 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Hausa |
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Hausa Larabci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | Malami |
Imani | |
Addini | Musulunci |
Abubakar Adamu RasheedAbubakar Adamu Rasheed (Taimako·bayani), MFR malami ɗan Najeriya kuma masanin ilimi da ke koyarwa da kuma kula da sashen gudanarwa, Farfesa ne shi na harshen Turanci kuma mataimakin shugaban jami'a na 9 na Jami'ar Bayero, Kano. [1]
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]Rasheed ya samu digirinsa na farko a fannin kere kere a jami’ar Bayero ta Kano, sannan ya kuma samu digiri a fannin fasaha daga jami’ar Nottingham sannan ya samu digiri na uku daga jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. [2]
Aiki
[gyara sashe | gyara masomin]Rasheed ya zama mataimakin shugaban jami’ar Bayero a shekara ta 2010, ya rike mukamin har zuwa shekara ta 2015. A shekara ta 2016, an kuma naɗa Rasheed a matsayin babban sakataren Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa. [3]
Karramawa
[gyara sashe | gyara masomin]A wasu hanyoyin da za a ci gaba da tunawa da irin kyawawan ayyukan da Farfesan ya yi wajen ci gaban jami’ar a lokacin da yake rike da mukaminsa, an sanya wa wani katafaren ginin majalisar dattijai sunan sa wanda shi ne ginin majalisar dattijai Farfesa Abubakar Adamu Rasheed da ke cikin jami’ar.[4]
A ranar 17 ga watan Junairu ne Jami’ar Maryam Abacha American University of Nigeria (MAAUN), Kano ta karrama Farfesa Abubakar Adamu Rasheed da lakca ta Twin Theatre wadda aka sanya wa sunansa kuma shi ne ya dauki nauyin gudanar da laccar Theatre[5].
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ http://buk.edu.ng/?q=news6
- ↑ "Thank you Prof. Rasheed, VC extraordinaire!". Daily Trust. Archived from the original on 2018-04-09. Retrieved 2018-04-08.
- ↑ "Prof. Rasheed takes over as substantive Executive Secretary". NUC. Retrieved 2018-04-08.
- ↑ Yakubu, Muhammed (2020-08-13). "Minister inaugurates ultra modern Senate Building in BUK". Retrieved 2024-08-30.
- ↑ "NUC Boss Commissions Twin-Lecture Theatre Named After him at MAAUN Kano". Stallion Times. 2023-01-17. Archived from the original on 2023-08-13. Retrieved 2023-08-13.