Aliyu Akilu
Aliyu Akilu | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1918 |
ƙasa | Najeriya |
Mutuwa | 1998 |
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | maiwaƙe |
Alhaji Dr. Aliyu Akilu MFR An haife shi a shekara ta alif 1918, ya rasu 19 ga watan oktoban shekara ta alif 1999 wanda kuma aka sani da Malam Akilu Aliyu ko Aqilu Aliyu ɗan Najeriya ne mawãƙi, marubuci, masanin ilimi ɗan siyasa, kuma daya daga cikin manyan marubuta waƙoƙin Hausa a karni na ashirin.
Tarihin Rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Akliu Aliyu a garin Jega (a wani ƙauye da ake kira Kyarmi, a cikin jihar Kebbi ta yanzu). Malam Akilu ya yi mafi yawan rayuwarsa a jihar Kano Kano, wurin da ya je a matsayin dalibin Islamiyya tun yana saurayi. Ya kasance a Maiduguri na 'yan shekarun da suka gabata kafin ya dawo Kano inda ya zauna har zuwa rasuwarsa. Ya rayu a matsayin malamin Islama, tela kuma mawaƙi (waƙa ta kasance hanya da ya koyar da dubban ɗalibai marasa adadi). Ya kafa, kuma ya koyar a, makarantun Islamiyya a Maiduguri da Azare.
Harkar Ilimi
[gyara sashe | gyara masomin]Dangane da karatunsa da farko dai ya fara samun horo a makarantar Al-Qur'ani a Kano, karkashin malaman Tijjaniyya, sannan kuma daga baya ya tafi Borno yin karatu a gaban manya-manyan malaman addinin Islama daga yankin arewa maso gabashin kasar. Ya NASA nice mawaki mai kaifin basira kuma yana rubutun waƙoƙin sa ne cikin harsunan Hausa da Larabci, kuma waƙen da yasa ya samu karbuwa sosai a tsakanin al ummar hausawa yawancin masu jin wakar sa Hausawa ne. Ya fara rubuta wakokin Larabci a cikin shekarun 1930.
Ayyuka
[gyara sashe | gyara masomin]Mashahuran Wakoki Sun Hada da
[gyara sashe | gyara masomin]- Matan Aure
- Dan Gata
- 'Yar Gagara
- Hausa Mai Ban Haushi
- Maza mamugunta
- Wakar Najeriya
- Cuta ba mutuwa ba
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]
- Simon Gikandi; Encyclopedia na Adabin Afirka, Routledge, 2002.
- Bookshelf, Disamba 3-9, 1999
- https://web.archive.org/web/20120907075829/http://www.linguistics.ucla.edu/people/schuh/Metrics/sample_akilu.html