Aminu Bashir Wali

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Aminu Bashir Wali
Ministan harkan kasan waje

2014 - 2015
Viola Onwuliri - Geoffrey Onyeama
Permanent Representative to the United Nations (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Kano, 3 ga Augusta, 1941 (82 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƙabila Hausawa
Harshen uwa Hausa
Karatu
Makaranta University of North London (en) Fassara
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Mai wanzar da zaman lafiya da ɗan siyasa

Aminu Bashir WaliAbout this soundAminu Bashir Wali  (an haife shi ne a ranar 3 ga watan Agustan, shekara ta alif ɗari tara da arba'in da daya 1941A.c) ya taba riķe mukamin ministan harkokin waje na Najeriya daga shekarar 2014 zuwa shekara ta 2015.[1]

Tarihin rayuwa[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Wali a cikin garin Kano a shekara ta 1941. Ilimin nasa ya hada da samun horo a Makarantar Koyon Larabci da ke Kano kuma ya kammala a shekara ta 1967 tare da digiri a kan Gudanar da Harkokin Kasuwanci daga North-Western Polytechnic da ke Landan. [2]

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Daga shekara ta 2004, ya kasance wakilin Najeriya na dindindin a Majalisar Dinkin Duniya . Sannan ya zama Jakadan Nijeriya a Jamhuriyar Jama'ar Sin wato China.

An nada Wali a matsayin Ministan Harkokin Kasashen Waje a karkashin gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan . Tafiye-tafiye zuwa kasashen waje sun hada da guda daya zuwa Turkiyya, bayan gayyatar da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlüt Çavuşoğlu ya yi . [3] A watan Oktoban shekara ta 2014, Wali ya karbi Ministocin Harkokin Wajen na Jamus da Faransa, Frank-Walter Steinmeier da Laurent Fabius, don tattaunawa kan sace-sacen Boko Haram da matakan yaki da barkewar cutar Ebola .

'Yan uwan juna

1, Abubakar Bashir Wali

2, Mahe Bashir Wali

3, Umar Bashir Wali

4, Mustapha Bashir Wali

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

  • Ministan Harkokin Waje (Najeriya)

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. "The Honourable Minister of Foreign Affairs Mr. Geoffrey Onyeama". Ministry of Foreign Affairs of Nigeria. Archived from the original on 2016-08-12. Retrieved 10 February 2016.
  2. Biographical Notes, UNVienna, Retrieved 10 February 2016
  3. No: 6, 07 January 2015, Press Release Regarding the Visit of H.E. Aminu Bashir Wali, Minister of Foreign Affairs of the Federal Republic of Nigeria Archived 2016-02-16 at the Wayback Machine, Retrieved 10 February 2016