Bikin Pategi Regatta

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentBikin Pategi Regatta

Iri biki
Kwanan watan 1949 –

Bikin Patigi Regatta an kafa shi a cikin shekarar 1949 amman bikin ya fara gudana a 1952. Taron kwale-kwale ne na Masarautar Pategi a Najeriya wanda ke nuna tseren kwale-kwale, kamun kifi da ninkaya.[1]

Pategi Emirate River, Boating festival, ragatta
Pategi ragatta boating junction

Tarihi[gyara sashe | gyara masomin]

Kogin Patigi

An gudanar da bikin ne a bakin kogin Neja a bakin tekun Patigi wanda shugaban majalisar pategi Ahman Pategi da Etsu Umaru Bologi I, suka kafa a shekarar 1950. Bikin asali ne, na tarihi da yawon shakatawa wanda taron farko ya faru a 1952. Bikin ya ƙunshi mazauna bakin kogin Niger, Kwara da Kogi, har wayau taron ya ƙunshi tseren kwale-kwale a Gbaradogi na gabar kogin yamma.[2][3][4]

A cikin 1920, mazauna a tafkin da bakin kogin sun zauna a can saboda dalilai daban-daban, na ɗaya daga cikinsu ya ƙunshi koguna a matsayin wurin ibada kamar Gbafu na Gazun a kasuwar Pategi. Wasu daga cikin kwale-kwalen a lokacin ibada ba sa motsi kuma a tsakiyar gabar kogin Osun da kogin Nilu na kasar Masar, inda ake samun wuraren tarukan ibada. Kogunan al’ummar Nupe kakanni ne suka kafa kogin Kempe, kogin Neja da kogin Kaduna wanda ƴan kasuwa suke zaunawa su huta kamar Muregi, Sunkuso, Sunlati, Nupeko da Pang Ellah a Nijar, Kwara da Kogi suna da dangantaka ta fannin kamun kifi., nutsewa don samun babban kifi, ƙawance da fahimta tare da irin wasan tseren dawaki da aka fi sani da Dubar a hade a cikin regatta na gargajiya.

Wannan yana taimakawa wajen kawo fahimtar juna da haɗin kai a cikin mutanen Nupe da kuma abin da kabilanci ke bayyana harsuna. Yawancin mazauna wurin suna amfani da jirgin a matsayin amfani wurin jigilar kaya tare. Wurin ne cibiyar yawon shakatawa sabanin cibiyar al'adu, regatta Motel da Regatta Pavilion. Sakamakon gazawar da aka yi a cikin shekaru da dama, a shekarar 2004 Gwamnan Kwara Abuakar Bukola Saraki ya kafa wani sabon kwamiti a Regatta saboda mantuwa da mutuwar bikin da kuma irinsa a kasar.[5][6][7]

Nassoshi[gyara sashe | gyara masomin]

  1. Idrees, Aliyu Alhaji (1998). The Patigi Regatta Festival: its historical perspective since 1950 (in Turanci). Caltop Publications (Nigeria) Ltd. ISBN 978-978-31653-6-6.
  2. "Patigi Regatta Festival, Festivals And Carnivals In Kwara State :: Nigeria Information & Guide". www.nigeriagalleria.com. Retrieved 2020-03-24.
  3. "Results for 'su:Festivals Nigeria Pategi.' [WorldCat.org]". www.worldcat.org (in Turanci). Retrieved 2020-03-24.
  4. Idress, Aliyu Alhaji (1998). The Patigi Regatta Festival : its historical perspective since 1950 (in English). Ibadan : Caltop Publications (Nigeria) Ltd. ISBN 978-978-31653-6-6.CS1 maint: unrecognized language (link)
  5. "Opinion: Reviving Patigi Regatta for tourist attraction. By Alhassan Aminu | Ilorin, Kwara News". www.ilorin.info. Retrieved 2020-03-24.
  6. Idrees, Aliyu Alhaji (1998). The Patigi Regatta Festival : its historical perspective since 1950 /. Ibadan: Caltop Publications (Nigeria) Ltd. ISBN 978-978-31653-6-6.
  7. IDREES, Aliyu A. (1988). "The Patigi Regatta Festival : Its Origin, Historical Significance and Tourism Prospects". Présence Africaine. 147 (3): 63–70. doi:10.3917/presa.147.0063. ISSN 0032-7638. JSTOR 24351632.