Chimamanda Ngozi Adichie
Chimamanda Ngozi Adichie (an haife ta a ranar 15 ga watan Satumba,na shekara ta alif dari tara da saba'in da bakwai 1977).[1] Yar Najeriya ce, marubuciya ce wanda ayyukanta suka haɗa da novels ƙananan labarai har ma da ƙagaggun labarai.[2] Adichie, wacce aka Haifa a birnin Enugu acikin Najeriya, ta girma amatsayin ya ta biyar cikin ya'ya shida a gidan su sake garin Nsukkan Jihar Enugu.[3] A sanda take tasowa, mahaifinta James Nwoye Adichie farfesa ne na ƙididdiga lissafi (statistics) a Jami'ar Najeriya Nsukka. Mahaifiyarta Grace Ifeoma itace registrar mace ta farko a jami'ar.[4] Gidansu sun rasa kusan dukkanin abubuwan da suka mallaka a lokacin Yaƙin Basasan Najeriya, wanda ya haɗa da rashin kakannin ta biyu.[5] Asalin ƙauyen danginta shine Abba[1] a Jihar Anambra.[6]
A shekarar 2008, Adichie an girmama ta da kyautar MacArthur Genius Grant. Kuma an bayyana ta a The Times Literary Supplement amatsayin "the most prominent" of a "procession of critically acclaimed young anglophone authors [who] is succeeding in attracting a new generation of readers to African literature".[7] Ta wallafa novels kamarsu Purple Hibiscus (2003), Half of a Yellow Sun (2006), and Americanah (2013), the short story collection The Thing Around Your Neck (2009), and the book-length essay We Should All Be Feminists (2014). Kuma littafin ta na kuma baya-baya shine, Dear Ijeawele, or A Feminist Manifesto in Fifteen Suggestions, an wallafa shi a watan Maris shekarar 2017.[8]
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ 1.0 1.1 "Biography of Chimamanda Adichie".
- ↑ Nixon, Rob (1 October 2006). "A Biafran Story". The New York Times. Retrieved 25 January 2009.
- ↑ Anya, Ikechuku (15 October 2005). "In the Footsteps of Achebe: Enter Chimamanda Ngozi Adichie". African Writer.
- ↑ "Feminism Is Fashionable For Nigerian Writer Chimamanda Ngozi Adichie". NPR, 18 March 2014.
- ↑ Enright, Michael (December 30, 2018) [2006]. The Sunday Edition - December 30, 2018 (Radio interview) (in English). CBC. Event occurs at 52:00.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ "Biography", The Chimamanda Ngozi Adichie website.
- ↑ Copnall, James (16 December 2011), "Steak Knife", The Times Literary Supplement, p. 20.
- ↑ "About Chimamanda". Chimamanda Ngozi Adichie Official Author Website (in Turanci). Archived from the original on 2018-08-20. Retrieved 2018-05-24.