David Bamigboye
David Bamigboye | |
---|---|
mutum | |
Bayanai | |
Jinsi | namiji |
Ƙasar asali | Najeriya |
Suna | Dauda |
Shekarun haihuwa | 7 Disamba 1940 |
Wurin haihuwa | Òmù-Àrán (en) |
Lokacin mutuwa | 21 Satumba 2018 |
Yaren haihuwa | Yarbanci |
Harsuna | Turanci, Hausa, Yarbanci da Pidgin na Najeriya |
Sana'a | ɗan siyasa |
Muƙamin da ya riƙe | gwamnan jihar Kwara |
Ƙabila | Yaren Yarbawa |
Military or police rank (en) | Janar |
Femi David Lasisi Bamigboye (ranar 7 ga watan Disamban 1940[1] – ranar 21 ga watan Satumban 2018) ya kasance kwamandan sojan Najeriya kuma ɗan siyasa a Jihar Kwara daga watan Mayun 1967 zuwa Yulin 1975, bayan ya rabu da tsohon yankin Arewa lokacin mulkin soja na Janar Yakubu Gowon.[2][3]
David Bamigboye ɗan ƙabilar Igbomina ne.[4] Ƙanensa shine Theophilus Bamigboye, wani shugaban mulkin soja ya zama ɗan siyasa.[5]
A cikin shekarar 1968 ya kafa ma’aikatar ilimi ta jihar Kwara, tare da sashen da zai kula da al’amuran guraben karatu/Busar.[6] A cikin shekarar 1971 ya sanar da shawarar kafa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kwara State Polytechnic, wacce aka kafa a cikin shekarar 1972.[7] A cikin watan Disamban 1972 ya buɗe sabon harabar asibitin Ola-Olu tare da masauki ga gadaje talatin da biyar.[8]
A cikin shekarar 1977, an ƙwace wasu ƙadarorin da ya mallaka a Ilorin, ba a mayar da shi ba sai bayan shekaru 26 a cikin watan Mayun 2003.[9]
A cikin shekarar 2009, an naɗa ɗansa Femi David Bamigboye mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kwara.[10]
Kyauta
[gyara sashe | gyara masomin]- Gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed ne ya ba Bamigboye lambar yabo ta jagoranci a ranar 27 ga watan Mayun 2017.
Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://www.vanguardngr.com/2018/09/breaking-bamigboye-first-military-governor-of-kwara-dies-at-78/
- ↑ https://books.google.com.ng/books?id=9EAOAQAAMAAJ&redir_esc=y
- ↑ https://www.worldstatesmen.org/Nigeria_federal_states.htm
- ↑ https://web.archive.org/web/20051201074427/http://www.thisdayonline.com/archive/2004/02/13/20040213news42.html
- ↑ https://web.archive.org/web/20061213042036/http://www.ngrguardiannews.com/policy_politics/article03
- ↑ http://www.kwaraeducation.com/R&S/SCHOLARSHIP%20BOARD.pdf[permanent dead link]
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2022-08-08. Retrieved 2023-04-07.
- ↑ https://web.archive.org/web/20100105195051/http://olaoluhospital.com/history7.htm
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2016-03-03. Retrieved 2023-04-07.
- ↑ https://web.archive.org/web/20100416042956/http://www.kwarastate.gov.ng/executive-council.html