Jump to content

Dolapo Osinbajo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Dolapo Osinbajo
Rayuwa
Haihuwa Ikenne, 1967 (56/57 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƴan uwa
Abokiyar zama Yemi Osinbajo
Yara
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa da Lauya
Dolapo Osinbajo

Dolapo Osinbajo, née Soyode (an haife tane a ranar 16 ga watan Yulin shekaran 1967) Ta kasan ce lauya ce kuma 'yar siyasa a Najeriya. Matar Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo, tun a shekarar 2015 ta kasan ce Uwar gidan mataimakin shugaban kasa kuma mace ta biyu a Najeriya.[1]

Gwamna Rochas Okorocha na Jihar Imo, Uloma Nwosu (MD House of Freeda), Mrs Dolapo Osinbajo (Matar Mataimakin Shugaban Najeriya), Misis Nkechi Okorocha (Matar Gwamnan Jihar Imo).

Kuruciya da aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

An haifi Dolapo Osinbajo a ranar 15 ga watan Yulin shekarar 1967, kuma ta girma a Ikenne. [2] Ita jika ce ga Obafemi Awolowo, dan siyasan Najeriya kuma mai matsayi a sarautan Yarbawa, [1] da matarsa Hannah Idowu Dideolu Awolowo, ta cibiyar diyar Awolowo Ayodele Soyode (née Awolowo),

Ta auri Yemi Osinbajo, wanda dan uwanta ne na nesa, a ranar 25 ga watan Nuwamban shekarar 1989. Ta kuma zama kwararrar lauya (a kungiyar Lauyoyin Najeriya) a shekarar 1990. [2]

Dolapo Osinbajo ita ce Babbar Darakta a kungiyar mata mai suna Women's Helping Hand Initiative, wata gidauniya ce a garin Epe, Lagos, wanda aka kafa a shekara ta 2014, kuma ita ce ta kirkiro kungiyar Orderly Society Trust.

Ayyuka a Matsayin Uwargida Na Biyu

[gyara sashe | gyara masomin]
Dolapo Osinbajo
Dolapo Osinbajo

A watan Satumbar shekarar 2019 ta shugabanci taron 49th Benue Women in Prayer (BEWIP), a Makurdi. [3] Ta kuma bude gidan yara na Mama Abyol da kuma Cibiyar Binuwai ta Bunkasa Kirare kere kere (BENCEDI). A jawabinta ga matasa a jihar Benuwe, ta gargade su kan yunƙurin kwafar salon rayuwa na yaudarar intanet. [4] Yayin da take zantawa da 'yan matan da suka kammala makaranta a Legas a watan Disambar 2019, ta kiraye su da su kasance masu riƙon amana a abin kwaikwayo ga na kasa da su. [5] Ta kuma nuna halin cin zarafin mata a matsayin cin zarafin daukakin al'umma ne. [6] A tsakiyar watan Disambar 2019, Uwargidan Shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari, ta nada Osinbajo - tare da matan gwamnonin jihohin Najeriya a matsayin zakarun da zasu jagoranci yaki da tarin fuka a Najeriya. [7]

    • They Call Me Mama: Daga littafin Under Bridge Diaries. 2014.
  1. 1.0 1.1 Yahaya Balogun, Dolapo Osinbajo: A cultural icon! Archived 2019-12-19 at the Wayback Machine, The Guardian, 10 July 2019. Accessed 16 May 2020.
  2. 2.0 2.1 Yemi and Dolapo Osinbajo: The 30 Years Love Story, This Day, 30 November 2019. Accessed 16 May 2020.
  3. Take all your worries to the Lord, Dolapo Osinbajo tells women. Vanguard, 14 September 2019. Accessed 15 May 2020.
  4. Read Dolapo Osinbajo’s timely advice to youths about internet, P.N. News, 15 September 2019. Accessed 16 May 2020.
  5. Dolapo Osinbajo sends message to out-of-school girls, P. M. News, 4 December 2019. Accessed 16 May 2020.
  6. Abuse against women is offence against humanity, says Dolapo Osinbajo[permanent dead link], The Guardian, 5 December 2019. Accessed 16 May 2020.
  7. Nike Adebowale, Aisha Buhari names Dolapo Osinbajo, governors’ wives as TB champions, Premium Times, 13 December 2019. Accessed 16 May 2020.