Yemi Osinbajo

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Yemi Osinbajo a shekara ta 2017.

Farfesa Yemi Osinbajo Lauya, Fasto, kuma ɗan siyasa a Nijeriya. An haife shi a shekara ta 1957 a Lagos, Kudancin Nijeriya (a yau a cikin jihar Lagos). Kwararren Lauya ne, Malami, kuma Babban limamin coci. Ya rike shugaban hukumar Shari'a ta jihar Lagos, amma yaki yadda da ya rike shugaban cin na kasa yayin mulkin Obasanjo daya nemi yabashi, inda yabayyana cewar dalilinsa na rashin karbar aikin shine gwamnatin lokacin bata biyan bukatun al'umman ta, hasali ma bata cika alkawuran data dauka nauyin yi. Maitamakin shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ne daga shekarar 2015 (bayan Namadi Sambo).