Guguwa

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jump to navigation Jump to search
Guguwa
subclass ofmeteorological disaster, vortex Gyara
has causecumulonimbus Gyara
measurement scaleEnhanced Fujita scale Gyara
Unicode character🌪 Gyara
guguwa
wannan wata guguwa ce a birinin Oklahoma na Amurka
Ma,aunin da ake duba karfin guguwa

Guguwa wata irin iska ce mai karfin gaske wacce take bugawa a sararin duniya, takasance itace iska mafi sauri datake kadawa a sararin samaniya da kuma sararin doron kasa a bisa ma'aunin kididdiga mai yawa.

Ita dai guguwa ta kasance tana faruwa ne sakamakon karfin iskar kusurwoyi biyu idan suka hadu a magama nan take zasuyi karo da juna sai su cure, sukuma sarkafe juna sai suyi rimi suna juyawa a bigire guda ko a bigire mabanbanta.

Sakamakon haka karfin guguwa yake zama mai karfin gaske kasancewar karfi biyu ne ya hadu waje guda.

Guguwa idan ta tashi tana tasiri akan abubuwa da dama ma'ana tana iya daukar wasu abubuwa ta tafi dasu, wasu kuma ta kayar dasu a inda suke, wasu kuwa ta fallatsa su waje mai nisa.

IRE-IREN GUGUWA[gyara sashe | Gyara masomin]

  • Guguwar tudu

ita dai guguwar tudu ta kasance guguwa ce datake tashi a bisa dandamalin doron kasa saboda canjin yanayin da wurin ya fuskanta wadda ke haifar da faruwar wasu abubuwa boyayyu wadda suke haifar da ita, irin wannan guguwar yawanci tafi faruwa a lokacin rani.

  • Guguwar teku

Sannan kuma akwai guguwar teku wacce take tashi a bisa dalilin murdewar igiyar ruwan teku, wadda da zarar hakan ya faru guguwar zata tashi da karfin gaske fiye da duk wata guguwa.

Kasancewar ruwa da iska sun hadu kaga an hada karfafa biyu kenan, shi yasa guguwar teku tafi kowacce guguwa hatsari domin ita dibar ruwan teku take ta tafi da shi, a dalilin haka za'a fuskanci mummunar ambaliya wadda ke rusa birni komai kyansa komai girmanshi.

Guguwa Mai karfi

Duk lokacin data tunkaro birni to takan rusa manyan gine-gine, haka zakaga ambaliyar ta dauki mota tana tafiya da ita kamar ba mota ba, idan kuwa taci karo da ginanniyar gada nan take zatayi rugu-rugu da ita. Asarar rayuka kuwa ai ba'a magana a nan, wannan kadan kenan daga cikin karfin wannan guguwa. Ko a kwana-kwanan nan ma ta afkawa birnin New York na kasar Amurka, da kuma wasu kasashe a nahiyar turai.