Hamzat Lawal

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Name: Hamzat LawalBorn:1987 (age 35–36)State of Origin: Kogi State Nationality: NigeriaAlma mater: University of AbujaSana'a: Fafutuka Domin Al'ummaShekarun Farawa: 2012 — izuwa yauSanayya: Follow The MoneyManyan Ayyuka: Follow The MoneyGidan yanar gizo: http://www.hamzatlawal.com/ [1]

Hamzat B. Lawal Mai fafutukar yaki da cin hanci da rashawa ne. Shi ne wanda ya kafa "Follow The Money", wani yunƙuri na bibiya da bahasin kasafin kudi da kashewa na gwamnatin tarayya wanda ya ƙunshi manazarta bayanai, 'yan jarida, masu fafutuka, da ɗalibai. Hamzat kuma shi ne Babban Jami’in Gudanarwa na Connected Development (CODE)[2], wata kungiya mai zaman kanta da ke ba wa al’ummar Afirka masu rauni damar samun bayanai kan yadda za su kara hada gwiwa wajen tabbatarda an aiwatarda ayyukan gwamnatinsu.

Farkon Tasowarsa[gyara sashe | gyara masomin]

Lawal dan jihar Kogi ne. Ya halarci Makarantar Firamare ta Model Asokoro da ke Abuja, kuma ya kasance shugaban ‘yan Scout, a lokacin da yake karatun sakandire a makarantar gwamnati ta Karu da ke jihar Nasarawa, ya yi aiki a matsayin kodinetan kungiyar Boys Scout da kuma Utility Prefect. Sannan ya yi makarantar sakandare a Seta International College, Jihar Nasarawa.

Karatun Gaba da Sakandare[gyara sashe | gyara masomin]

Lawal ya kammala karatun digiri ne a Jami'ar Abuja, inda ya yi digirin farko a fannin kimiyyar siyasa.

Kwarewar Aiki[gyara sashe | gyara masomin]

Ya yi aiki a matsayin Rep Serviceman a wani kamfanin fasahar sadarwa, daga baya ya yi aiki a matsayin kwararre kan fasahar sadarwa tare da Cibiyar Ksa-da-kasa kan Makamashi, Muhalli da Raya Kasa (ICEED)[3] a lokacin da sha'awar canjin yanayi ta karu. Lokacin da maigidan nasa ya lura da fannin sha'awarsa, sai ya ba shi shafin Kundin-Tsarin Yanayi na Majalisar Dinkin Duniya na yanar gizo akan canjin yanayi don yin bincike, kuma bayan ya bi takaddu da ka'idoji, ya sami ƙarin sha'awar wannan yanki. Daga baya ya yi rajista tare da dandamali da yawa na canjin yanayi kuma ya shiga cikin ayyuka da yawa.

A shekarar 2012, Lawal ya ji takaicin irin gubar da aka sha a jihar Zamfara shekaru biyu da suka wuce. Sannan a Lokacin da ya fahimci cewa babu wanda ke magana game da bala'in wanda ya janyo rasa mtane sama da 400, sai ya yi tafiyar sa'o'i 14 zuwa cikin al'ummar Bagega, inda lamarin ya faru [4], don ya ƙara karantar lamarin bayan aukuwar matsalar. Wannan ya zaburar da shi zuwa ga fafutukar al’umma da kuma fara wani yunkuri mai tushe da aka fi sani da Follow The Money[5], ta hanyar amfani da bayanai don rikar gwamnati da hakki, da kuma neman dauki daga hukumomin gwamnati. A watan Maris 2021, Hamzat Lawal yayi nasarar lashe kyautar $120,000 na Gasar Aiki Mai Dorewa na Gothenburg[6].

Fafutuka[gyara sashe | gyara masomin]

Lawal ya fara fafutuka ne a lokacin da yake Jami'ar Abuja. Daga nan kuma ya dauki nauyin bayar da shawarwari domin shugabanci nagari a tsakanin dalibai da kuma cikin al'ummar dalibai. Ya ci gaba da tofa albarkacin bakinsa kan cin hanci da rashawa, take hakkin dan Adam da kuma tauye hakkin matasa da sauran ‘yan kasa. A cikin 2013, Ma'aikatar Tsaro ta Jihar ta kusan kama shi bayan an zarge shi da tunzura matasa a kan gwamnatin lokacin.[7]

Ayyuka[gyara sashe | gyara masomin]

Lawal dai shi ne mukaddashiun fafutuka na kungiyar ‘Not Too Young To Run[8], kungiyar matasan Najeriya da ke goyon bayan ‘yancin matasa na tsayawa takarar mukaman siyasa ya tabbatar da cewa an zartar da dokar rage shekaru a fadin kasa, wanda ke inganta shigar matasa siyasar Najeriya. Shi mamba ne a hukumar zartarwa ta Afirka Youth Initiative on Climate Change.[9]

Kwato Yancin Bagega[gyara sashe | gyara masomin]

Fafutukar Kwato Yancin Bagega wanda akayiwa lakabi da "#SaveBagega" wani kamfen ne da aka fara a shafin Twitter lokacin da Hamzat ya fara amfani da hashtag a lokacin da ya wallafa a shafinsa na Twitter game da cutar gubar dalma a garin Bagega da ke jihar Zamfara.[10] A cikin watan Mayun 2012, kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders ta bayar da rahoton cewa akalla yara 4,000 ne ke fama da cutar dalma sakamakon aikin hako zinare da aka yi a jihar Zamfara a Najeriya.[11] A cikin wannan shekarar ne kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta kara yin kira ga gwamnatin Najeriya da ta yi alkawarin kusan dalar Amurka miliyan 5 don tsaftace wuraren da aka gurbata da gubar a yayin aikin hako zinare na sana’ar saboda yawan gubar dalma a cikin duwatsu. A lokacin taron Human Right's Watch a #SaveBagega, an ba da rahoton mutuwar yara fiye da 400 kuma yawancin yaran ba a iya kula da su ba.[12][13]

A cikin Janairu 2013, yakin ya kai kimanin mutane miliyan daya, kuma yawancin kafofin watsa labaru sun dauki labarin.[14]. A karshen wannan watan, gwamnatin tarayya ta saki dala miliyan biyar da digo uku (5.3m).[15]

Karramawa[gyara sashe | gyara masomin]

  • 2017: Kyautar Afirka ɗaya[16]
  • 2018: Apolical's 100 Mafi Tasiri a Gwamnatin Digital[17]
  • 2018: Kyautar-Cancanta a Tattalin Arzikin Afirka[18]
  • 2019: The Future Awards Africa (nau'in shawarwari)[19]
  • 2019: United Nations Sustainable Development Goals Action Awards[20]
  • 2020: Gwarzon Ilimi na Duniya, Malala Foundation[21][22]
  • 2021: BeyGOOD's Global Citizen Fellowship[23][24]
  • 2021: Ƙwararrun Ƙirƙirar Dimokuradiyya ta Majalisar Turai[25]
  • 2021: Fitattun Matasa Goma, Junior Chamber International Nigeria[26]
  • 2021: Jakadi mai girma a Isra'ila [27]
  • 2021: Gwarzon WIN WIN Gothenburg Kyautar Dorewa [28]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. https://www.connecteddevelopment.org/
  2. https://www.connecteddevelopment.org/
  3. https://ynaija.com/hamzat-lawa-started-i-connected-pain/
  4. https://www.legit.ng/1020830-started-connected-pain-young-nigerian-shares-inspiring-story.html Archived 2019-04-20 at the Wayback Machine
  5. http://followthemoneyng.org/about-us/
  6. https://en.wikipedia.org/wiki/Hamzat_Lawal#cite_note-6
  7. https://en.wikipedia.org/wiki/Hamzat_Lawal#cite_note-7
  8. https://en.wikipedia.org/wiki/Not_Too_Young_To_Run
  9. https://www.ayicc.org/About-Us.php
  10. https://en.wikipedia.org/w/index.php?title=Hamzat_Lawal#cite_note-9
  11. https://en.wikipedia.org/wiki/Hamzat_Lawal#cite_note-10
  12. https://en.wikipedia.org/wiki/Hamzat_Lawal#cite_note-11
  13. https://en.wikipedia.org/wiki/Hamzat_Lawal#cite_note-12
  14. https://technext.ng/2021/03/10/nigerias-hamzat-lawal-emerges-finalist-for-the-120000-gothenburg-sustainability-award/
  15. https://en.wikipedia.org/wiki/Hamzat_Lawal#cite_note-14
  16. https://en.wikipedia.org/wiki/Hamzat_Lawal#cite_note-
  17. https://en.wikipedia.org/wiki/Hamzat_Lawal#cite_note-16
  18. https://www.dailytrust.com.ng/elumelu-akufo-addo-davido-others-listed-for-aema-continental-awards.html Archived 2019-04-20 at the Wayback Machine
  19. https://en.wikipedia.org/wiki/Hamzat_Lawal#cite_note-18
  20. https://en.wikipedia.org/wiki/Hamzat_Lawal#cite_note-19
  21. https://en.wikipedia.org/wiki/Hamzat_Lawal#cite_note-23https://malala.org/champions/hamzat-%22hamzy%22-lawal
  22. https://en.wikipedia.org/wiki/Hamzat_Lawal#cite_note-23
  23. https://en.wikipedia.org/wiki/Hamzat_Lawal#cite_note-22
  24. https://en.wikipedia.org/wiki/Hamzat_Lawal#cite_note-23
  25. https://en.wikipedia.org/wiki/Hamzat_Lawal#cite_note-24
  26. https://en.wikipedia.org/wiki/Hamzat_Lawal#cite_note-25
  27. https://en.wikipedia.org/wiki/Hamzat_Lawal#cite_note-26
  28. https://en.wikipedia.org/wiki/Hamzat_Lawal#cite_note-27