Hari a Jihar Borno, Satumba 2015

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Infotaula d'esdevenimentHari a Jihar Borno, Satumba 2015
Map
 11°50′N 13°09′E / 11.83°N 13.15°E / 11.83; 13.15
Iri harin ta'addanci
Kwanan watan 20 Satumba 2015
Wuri Maiduguri
Monguno
Ƙasa Najeriya
Adadin waɗanda suka rasu 117

A yammacin ranar 20 ga watan Satumba, 2015, an kai jerin hare-haren bama-bamai a Maiduguri da Monguno, a Najeriya, inda aka kashe akalla mutane 145. da kuma raunata akalla wasu su 97. Mafi yawan wadanda suka jikkata harin ya rutsa dasu ne a Maiduguri inda wasu ababen farfashewa ƙwara huɗu suka halaka aƙalla mutane 117 .

Hari[gyara sashe | gyara masomin]

Hare-haren bama-baman sun faru ne bayan fiye da wata guda ba tare da samun wata matsala ba a birnin Maiduguri daga ƙungiyar tada ƙayar bayanan da dai ƙaurin suna, wato Boko Haram mai tsattsauran ra'ayi.[1] Wani farmaki da sojojin Najeriya suka kai a watan Agusta, inda suka fatattaki ƴan Boko Haram daga sansanonin su a yankin, ya haifar da raguwar hare-hare.[1][2] Tun da farko ranar 20 ga watan Satumba; shugaban ƙungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar da wani faifan bidiyo yana ƙaryata ikirarin da sojojin Najeriya suka yi na cewa an fatattaki Boko Haram.[3][4] Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai hare-haren, kodayake ana zargin ƙungiyar Boko Haram.[5] Kakakin rundunar sojin Najeriya Sani Usman ya bayyana cewa, taron ya nuna irin halin da 'yan Boko Haram ke ciki.[5] Abba Mohammed Bashir Shuwa, hadimin gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya bayyana cewa maharan sun yi amfani da damar da jama'a suka taru domin bukukuwan karamar Sallah.[6]

A Maiduguri[gyara sashe | gyara masomin]

Misalin karfe 7:30;lokacin gida (18:30;UTC ) na ranar 20 ga watan Satumba; [7] An tayar da wasu bama-bamai guda huɗu a faɗin Maiduguri, babban birni a jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, a cikin shekaru 20, inda suka kashe aƙalla mutane 54..[5][8][9] Waɗannan ne hare-hare mafi girma da aka kai a birnin tun cikin watan Maris;7, 2015, lokacin da wasu jerin hare-haren kunar bakin wake da ake dangantawa da Boko Haram suka kashe mutane 58.[10][11]

Wani ɗan ƙuna baƙin wake ya tayar da bama -bamai, samfurin-(IED) a wani masallaci da ke Ajilari,[1] ya kashe akalla mutane 43.[9] Fashewar ta biyu (ta bom ɗin) ta faru a wata kasuwa da ke birnin bayan da ƴan ta’addar suka jefa bama-bamai a cikin wata cibiyar kallo (gidan kallon fina-fina, ko cinima), inda suka kashe aƙalla mutane 11[1][9] ko aƙalla su 15 da suka rasa rayukansu.[12] Harin bam na huɗu ya faru ne a wata cibiyar wasanni (shagunan buga games na TV. Misali wasan kamfuta na Playsatatio).[3] Mai magana da yawun ƴan sanda; Victor Isuku, ya bayyana cewa aƙalla mutane 97 ne suka jikkata.[8] Wata ƙungiyar kare fararen hula ta bayar da rahoton cewa aƙalla mutane 80; aka kashe, mutane a cikin birnin kuma sun bayyana cewa ƴan sanda sun bayar da rahoton raguwar adaɗin saboda iyalai da ke binne mamatansu nan da nan.[13] Mazauna yankin sun ce adaɗin ya zarta haka, ciki har da akalla 85 da suka mutu.[12] A ranar 22, ga watan Satumba; asibitocin gida sun ba da rahoton cewa aƙalla mutane 117 an sanar da mutuwar su, daga cikin su, su 72 a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri da kuma 45 a asibitin kwararru na jihar Borno.[14]

A Monguno[gyara sashe | gyara masomin]

Kimanin sa'o'i biyu bayan tashin bama-bamai a Maiduguri, an sake tayar da wasu bama-bamai biyu a wani shingen bincike a cikin kasuwar Monguno kimanin kilomita 135 daga birnin Maiduguri. Ya kashe akalla mutane 28.[7][8]

Duba kuma[gyara sashe | gyara masomin]

Manazarta[gyara sashe | gyara masomin]

  1. 1.0 1.1 1.2 1.3 Lanre Ola & Julia Payne (September 21, 2015). "At least 54 people killed in bomb blasts in Nigeria's Maiduguri". Maiduguri, Nigeria: Reuters. Retrieved September 21, 2015.
  2. "DHQ: Nigerian Troops Have Destroyed All Boko Haram Camps". This Day Live. 10 September 2015. Archived from the original on 13 September 2015. Retrieved 10 September 2015.
  3. 3.0 3.1 "50 killed in multiple blasts in Nigeria". Business Standard. September 21, 2015. Retrieved September 21, 2015.
  4. Ludovica Iaccino (September 21, 2015). "Boko Haram leader Abubakar Shekau calls Nigerian Army liars as deadly attacks continue". International Business Times. Retrieved September 21, 2015.
  5. 5.0 5.1 5.2 "Nigeria's Boko Haram crisis: Maiduguri blasts kill dozens". BBC News. September 21, 2015. Retrieved September 21, 2015.
  6. Norimitsu Onishi (September 22, 2015). "More than 100 Killed by Boko Haram Bombings in Nigeria". New York Times. Abuja, Nigeria. Retrieved September 22, 2015.
  7. 7.0 7.1 Lanre Ola; Isaac Abrak; Alexis Akwagyiram & Julia Payne (September 22, 2015). "At least 80 people killed in bomb blasts in Nigeria's Borno state". Maiduguri, Nigeria: Reuters. Archived from the original on September 23, 2015. Retrieved September 22, 2015.
  8. 8.0 8.1 8.2 "Extremist attack killed at least 100 in Nigeria, defense group says". Maiduguri, Nigeria: CBS News. Associated Press. September 22, 2015. Retrieved September 22, 2015.
  9. 9.0 9.1 9.2 "Dozens die in blasts in Borno state capital, Nigerian official says". Abuja, Nigeria: CBS News. Associated Press. September 22, 2015. Retrieved September 22, 2015.
  10. "Nigerian city of Maiduguri hit by multiple blasts". BBC News. September 21, 2015. Retrieved September 22, 2015.
  11. "5 suicide blasts hit Nigerian city of Maiduguri, 54 killed". Yahoo News. 7 March 2015.
  12. 12.0 12.1 Bukar Hussain (September 21, 2015). "85 dead in new Boko Haram strike on Nigeria's Maiduguri". Yahoo! News. Agence France-Pressse. Archived from the original on September 23, 2015. Retrieved September 21, 2015.
  13. Jossy Ola (September 22, 2015). "Nigeria defense group: At least 100 killed in Sunday's blasts in northeastern Borno state". U.S. News. Associated Press. Retrieved September 22, 2015.
  14. "Death toll hits 117 after NE Nigeria bombings: medics". Maiduguri, Nigeria: Yahoo! News. Agence France-Presse. September 22, 2015. Archived from the original on September 23, 2015. Retrieved September 22, 2015.