Hauwa Maina
Hauwa Maina | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jihar Borno, |
ƙasa | Najeriya |
Mutuwa | jahar Kano, 2 Mayu 2018 |
Karatu | |
Makaranta | Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kaduna |
Harsuna |
Turanci Hausa |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi da producer (en) |
Hauwa MainaMaina, Marigayiyar tsohuwar ’yar fim ce kuma furodusa ce, an haife ta ne a garin Biu da ke Jihar Borno. Ƴar wasan kwaikwayo ce a Hausa fim. Hauwa Maina ta fara fim ne a shekarata alif dubu ɗaya da ɗari tara da casa'in da takwas (1998). Ba ta da sha'awar yin wasan kai tsaye.
Tarihin rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifeta a garin kaduna, Amma asalin ta ta fito daga garin biu dake Jihar Borno, Najeriya.
Ta kammala karatunta a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kaduna, inda ta karanci fannin Ma’aikata.[ana buƙatar hujja] [1]Bayan samun difloma na ƙasa, Hauwa ta yanke shawarar aiki a matsayin 'yanci. Hakan ya kasance kafin ta haɓaka sha'awar zane-zane da wasan kwaikwayo. Tana da mutum na musamman da za ta gode wa saboda yadda ta ba ta aikin wasan kwaikwayo ta turawa,sanan jarumar yar kabilar pabur ne[2]
Aure
[gyara sashe | gyara masomin]Jarumar tayi aure tana da yarinya mace me suna ahalan, tayi aure da yaro ɗaya kafin rasuwar mahaifiyar ta.
Sana'ar fim
[gyara sashe | gyara masomin]Hauwa Maina, ta shiga masana'antar fim tun a shekarar 1998 zuwa 1999. Inda ta fara da wani fim mai suna "TUBA" a matsayin jaruma, kuma a mafi yawan fina-finan ta, ta fi mayar da hankali ga bangaren da ke nuna jajircewar diya mace.
Fim ɗin ta na farko shine Tuba, sai ta fito a fim ɗin bayajidda-wani fim na tarihi da ake amfani da shi wajen koyar da yara a makaranta a yau.[3]
Tana da kamfanin kashin kanta, kamfanin mai suna Ma'inta Enterprises Limited kuma kamfanin ya shirya fina-finai da suka haɗa da Gwaska, Sarauniya Amina da sauran su.[4][5][6]
Fina-fina
[gyara sashe | gyara masomin]- Tuba
- Queen Amina of Zazzau[5]
- Bayajida
- Sarauniya Amina
- Gwaska
- Maina
- Dawo dawo. Da sauran su
Nominations and awards
[gyara sashe | gyara masomin]Mutuwa
[gyara sashe | gyara masomin]A ranar Laraba 2 ga watan Mayu, shekarar 2018 ne Hauwa Maina ta rasu a asibiti a Kano bayan doguwar rashin lafiya.[8][9] ta fara kwanciya a asibitin Dake Kano ,ta shafe wata uku tana jinya sannan Anan ta rasu, anyi Jana,Izar jarumar a ranar alhamis a mahaifarta watau jihar Kaduna, Sannan ta rasu tana da shekara hamsin a duniya[10]
Duba kuma
[gyara sashe | gyara masomin]Manazarta
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ https://www.bbc.com/hausa/labarai-43996281
- ↑ https://www.bbc.com/hausa/labarai-43996281
- ↑ Liman, Abubakar Aliyu (5 September 2019). "Memorializing a Legendary Figure: Bajajidda the Prince of Bagdad in Hausa Land". Afrika Focus. 32 (1). doi:10.21825/af.v32i1.11787.
- ↑ Blueprint (2014-03-24). "We want to tell our African stories in Hausa movies – Hauwa Maina". Blueprint (in Turanci). Blueprint Newspapers Limited. Retrieved 2022-08-05.
- ↑ 5.0 5.1 "Hail of tributes trail late Hauwa Maina, Kannywood celebrated actress". Vanguard News (in Turanci). 2018-05-04. Retrieved 2022-08-05.
- ↑ 6.0 6.1 Edubi, Omotayo (2018-05-03). "Kannywood actress, Hauwa Maina, is dead". The Sun Nigeria (in Turanci). Retrieved 2022-08-05.
- ↑ "Kannywood actress Hauwa Maina is dead". TheCable Lifestyle (in Turanci). 2018-05-03. Retrieved 2022-08-05.
- ↑ https://www.premiumtimesng.com/entertainment/kannywood/266989-breaking-kannywood-actress-hauwa-maina-is-dead.html
- ↑ Lere, Mohammed (2018-05-02). "Kannywood actress, Hauwa Maina, is dead". Premium Times Nigeria (in Turanci). Retrieved 2022-08-05.
- ↑ https://www.bbc.com/hausa/labarai-43998583