Ivan Franko
Ivan Franko | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Nahuievychi (en) , 27 ga Augusta, 1856 |
ƙasa | Austrian Empire (en) |
Harshen uwa | Jamusanci |
Mutuwa | Lviv (en) , 28 Mayu 1916 |
Makwanci | Lychakiv Cemetery (en) |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Olha Franko (en) |
Yara |
view
|
Karatu | |
Makaranta |
University of Vienna (en) Doctor of Philosophy (en) : falsafa Lviv University (en) (1875 - : falsafa Chernivtsi University (en) (1891 - |
Matakin karatu | Doctor of Philosophy (en) |
Harsuna |
Harshan Ukraniya Polish (en) Jamusanci |
Sana'a | |
Sana'a | marubuci, ɗan jarida, maiwaƙe, cultural historian (en) , marubucin wasannin kwaykwayo, mai aikin fassara, Mai tattala arziki, literary critic (en) , ɗan siyasa da short story writer (en) |
Wurin aiki | Lviv (en) |
Employers | University of Vienna (en) |
Muhimman ayyuka | Kameniari (en) |
Ayyanawa daga |
gani
|
Wanda ya ja hankalinsa | Taras Shevchenko |
Mamba | Shevchenko Scientific Society (en) |
Fafutuka | literary realism (en) |
Sunan mahaifi | Джеджалик, Мирон, Мирон Сторож, Мирон Ковалишин, Руслан da Іван Живий |
Artistic movement |
waƙa short novel (en) ƙagaggen labari novella (en) Gajeren labari wasan kwaikwayo |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | Ukrainian Radical Party (en) |
IMDb | nm0291609 |
Ivan Yakovych Franko (Yukreniyanci: Іван Якович Франко, ana fursta shi [iˈwɑn ˈjɑkowɪtʃ frɐnˈkɔ]; 27 ga watan Agustan shekara ta 1856 - 28 ga watan Mayu shekara ta 1916) [1] ya kasance mawaki dan kasar Yukren, marubuci, mai sukar zamantakewa da wallafe-wallafen, ɗan jarida, Mai fassara, masanin tattalin arziki, dokta a falsafar siyasa, Masanin ilimin lissafi, kuma marubucin litattafai bincike na farko da shayari na zamani a cikin Harshen Yukren.
Ya kasance mai tsattsauran ra'ayi na siyasa, kuma wanda ya kafa ƙungiyar gurguzu ga ‘yan kasa a yammacin Yukren. Baya ga aikinsa na wallafe-wallafe, ya kuma fassara zuwa yaren Yukren ayyukan sanannun mutane kamar William Shakespeare, Lord Byron, Pedro Calderón de la Barca, Dante Alighieri, Victor Hugo, Adam Mickiewicz, Johann Wolfgang von Goethe da Friedrich Schiller. Fassararsa ta bayyana a kan mataki na Gidan wasan kwaikwayo na Ruska Besida . Tare da Taras Shevchenko, ya sami babban tasiri a kan tunanin wallafe-wallafen zamani da siyasa a Ukraine.
Tarihin rayuwa
[gyara sashe | gyara masomin]An haifi Franko a ƙauyen Yukren na Nahuievychi wanda a wancan lokacin ke cikin yankin ƙasar Austrian na Galicia, a yau wani ɓangare na Drohobych Raion, Lviv Oblast, Yukren. Yayinda yake yaro, Uba Yosyp Levytsky, wanda aka fi sani matsayin mawaki kuma marubucin Hramatyka na farko na Galician-Ruthenian, kuma daga baya aka tura shi gudun hijira zuwa Nahuyevychi don "harshe mai kaifi". A gida, duk da haka, ana kiran Ivan Myron saboda imani na camfi na gargajiya cewa idan aka kira mutum da wani sunan na daban zai guje wa mutuwa.[2] Iyalin Franko a Nahuyevychi an dauke su "mai kyau", tare da bayinsu da hekta 24 (59 acres) na dukiyarsu.[3]