Jump to content

Jami'ar Agriculture ta Tarayya, Zuru

Daga Wikipedia, Insakulofidiya ta kyauta.
Jami'ar Agriculture ta Tarayya, Zuru
Bayanai
Iri jami'a da farawa
Ƙasa Najeriya
Mulki
Hedkwata Zuru
Tarihi
Ƙirƙira 2020
fuaz.edu.ng

Jami'ar aikin gona ta taraya, Zuru jami'a ce ta Najeriya da ke Zuru, jihar Kebbi wacce gwamnatin tarayyar Najeriya ke kula da ita baki ɗaya.[1][2][3]

An kafa Jami'ar Gwamnatin Tarayya ta Zuru a matsayin Kwalejin Aikin Noma, Zuru. A baya kwalejin tana da alaƙa da Jami’ar Ahmadu Bello Zariya. Bayan kafa hukumar kula da ilimin fasaha ta kasa (NBTE) a shekarar 1977 da gwamnatin tarayya ta kafa domin daidaita ilimin fasaha a kasar nan, NBTE ta ɗauki nauyin kulawa da kuma amincewa da shirye-shiryen kwalejin. A shekarar 2019, Sanata Barau Jibrin ya gabatar da ƙudirin doka. A ranar 21 ga watan Afrilu, 2019, an karanta dokar karo na uku kuma aka zartar da ita. Sabuwar jami'ar ta fara aiki a watan Satumba na shekarar 2020.[1][4] A watan Afrilun shekarar 2020, Shugaba Mohammed Buhari ya naɗa Musa Isiyaku Ahmed a matsayin mataimakin shugaba.[5][6] sannan a shekarar 2021, Eze Eberechi N. Dick ya zama shugaban jami'ar na farko. Kafin wannan lokacin, Bello Zaki ya kasance mataimakin shugaban riƙo.[7] [8]

Laburaren Jami'ar yana taimakawa wajen koyarwa, koyo da bincike don cimma muradun jami'a. E-Laburaren yana da miliyoyin tushen bayanan kan layi, mujallu na e-mujallolin JSTOR, ScienceDirect.[9] Laburaren yana sarrafa kansa tare da kwamfutoci don sauƙin isa ga bayanai.

Mataimakin shugaban jami'ar

[gyara sashe | gyara masomin]

Eze Eberechi N. Dick (JP).

Maɓallin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]

Official website

  1. 1.0 1.1 Television, Channels (10 April 2019). "Senate Approves Bill On Establishment of Federal University of Agriculture, Zuru". Channels Television. Retrieved 25 February 2022.
  2. Nanono, Alhaji Sani (11 December 2019). "University of Agriculture, Zuru to take-off in 2020 ― Nanono". Vanguard. Retrieved 25 February 2022.
  3. Udegbunam, Oge (10 December 2019). "Federal University of Agriculture Kebbi takes off September 2020- FG". Premium Times. Retrieved 25 February 2022.
  4. "College Of Agriculture, Zuru, Kebbi State". Manpower Nigeria. Retrieved 25 February 2022.
  5. Udegbunam, Oge (9 April 2020). "FG appoints VC for newly-established University Of Agriculture, Kebbi". Premium Times. Retrieved 25 February 2022.
  6. Odeyemi, Joshua (9 April 2020). "Buhari Appoints VC For Federal University Of Agriculture, Zuru". Daily Trust. Retrieved 25 February 2022.
  7. Ewepu, Gabriel (10 December 2019). "Nigeria: Newly Established Agric Varsity, Zuru Gets 19-Man Interim Management Committee". Vanguard. Retrieved 25 February 2022 – via AllAfrica.
  8. Nnabuife, Collins (10 December 2019). "Federal University Of Agriculture, Kebbi To Take Off September 2020 ― Minister". Nigerian Tribune.
  9. "E-Library". www.fuaz.edu.ng. Retrieved 2022-12-28.