Joshua Olalekan Ogunwole
Joshua Olalekan Ogunwole | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jahar Ibadan, 23 ga Yuli, 1967 (57 shekaru) |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello |
Sana'a | |
Sana'a | scientist (en) |
An haifi Joshua Ogunwole a garin Ibadan a ranar 23, ga watan Yuli 1967. Shi masanin kimiyyar ƙasa ne a Najeriya wanda a halin yanzu yake aiki a matsayin mataimakin shugaba na 4, na jami'ar Bowen.[1]
Ilimi da aikiaiki.
[gyara sashe | gyara masomin]Ogunwole ya yi digirinsa na farko da na biyu da na uku a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. A tsakanin shekarar 1990-1992, ya yi aiki a matsayin manaja na gonar Yula, Kaduna.[2]
Ogunwole ya koyar a sashen samar da amfanin gona da kariya na jami'ar tarayya dake Dutsin-Ma a tsakanin watan Dec 2013 - Maris 2016, kuma ya zama darakta na ci gaban jami'a da haɗin gwiwa.[3]
Shi Farfesa ne a fannin ilimin kimiyyar ƙasa, Sashen Kimiyyar Ƙasa da Gudanar da albarkatun ƙasa, a Jami'ar Tarayya dake Oye-Ekiti, har zuwa lokacin da aka naɗa shi a matsayin mataimakin shugaban jami'ar Bowen.[4]
Hanyoyin sadarwa da kyaututtuka.
[gyara sashe | gyara masomin]A cikin shekarar 2004, Joshua Ogunwole ya sami lambar yabo ta bincike don aikin noma mai ɗorewa, daga gidauniyar Schweisfurth da tallafawa Afirka ta ƙasa da ƙasa ta Jamus.[5]
A shekarar 2012, a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya, ya samu nasarar shirya taron karawa juna sani na ƙasa da ƙasa kan tsarin tafiyar da jikin ƙasa a yammacin Afirka.[6]
An shigar da Ogunwole a Kwalejin Nazarin Associates na Jami'ar Majalisar Ɗinkin Duniya-Cibiyar Albarkatun Ƙasa na Afirka a cikin shekarar 2015. Shi memba ne na al'ummar kimiyyar ƙasa a Najeriya.[7]
Ayyuka.
[gyara sashe | gyara masomin]Ayyuka sun haɗa da:
- Tracking the fate of pulse-labeled carbon and nitrogen in Pearl Millet residues, freshly incorporated, into soils.
- Evaluation of Maize-Desmodium-Soybean Cropping Effect on Soil Quality and Crop Yields in an Alfisols of Northern Guinea Savanna, Nigeria (wanda yayi bincike tare da wasu furofesoshi shida).
- Har ila yau yana daya daga cikin masu hadin gwiwa guda takwas a kan aikin bincike mai suna Soil Properties Characterization .
Takardun bincike da muƙaloli.
[gyara sashe | gyara masomin]Joshua Ogunwole ya rubuta fiye da takarda bincike guda 60, da muƙala, sanannu daga cikinsu akwai:
- contribution of Jatropha curcas to soil quality improvement in a degraded Indian entisol .
- Soil organic carbon, nitrogen and phosphorus distribution in stable aggregate of an Ultisol under contrasting land use and management history .
Manazarta.
[gyara sashe | gyara masomin]- ↑ "Absence Of Link Between Varsities' Research, Industries Stalling Nigeria's Development — Ogunwole – Bowen" (in Turanci). Retrieved 2019-12-19.
- ↑ "Joshua Ogunwole Archives". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). Archived from the original on 2019-12-19. Retrieved 2019-12-19.
- ↑ "Bowen University appoints Ogunwole as new vice-chancellor". Punch Newspapers (in Turanci). 14 August 2018. Retrieved 2019-12-19.
- ↑ https://www.pressreader.com/nigeria/the-punch/20191119/282278142167602. Retrieved 2019-12-19 – via PressReader. Missing or empty
|title=
(help) - ↑ "Joshua O. Ogunwole - Google Scholar Citations". scholar.google.com. Retrieved 2019-12-19.
- ↑ "Absence of link between varsities' research, industries stalling Nigeria's development — Prof Ogunwole, VC, Bowen varsity". Punch Newspapers (in Turanci). 14 July 2019. Retrieved 2019-12-19.
- ↑ "Professor Joshua Ogunwole Assumes Duty as the Vice Chancellor of Bowen University, Iwo". SSSN (in Turanci). 2018-08-03. Archived from the original on 2019-12-19. Retrieved 2019-12-19.